← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 175

Sashe 77

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Janafty* [7/5, 6:22 PM] +234 810 299 5100: *KNKB2005* *Ki biya ki karanta cikin salama,Kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta min littafi,Sannan kada ki yad'amin shi,Pay N500 regular ko kuma VIP N1000, Via Jamila Umar Gt bank 05521790550,ban da tsarin kati wannan karo a turo ta POS, Shaidar biya ta wannan lambar 09069067488* Ranar monday da safe bayan yaran sun shirya Hafsah tayi musu abun karyawa,Musty sai tura baki yake yi shi bazai je makaranta ba yau. Na kallesa ina kokarin saka masa safa yana Turje kafa cikin haushi na mangarar da kansa ina fadin"Zaka tsaya ko sai na dake ka..? Sai ya fara kokarin sakin mun kuka na ko zare mai ido ina fadin"Na dake ka ne da zaka min kuka..? Amir na gefe da ya shirya Tsaf yau zai fara zuwa makaranta yace"Umma cewa yayi bazai je ba, saboda Anum bata nan yau" Na kallesa da mamaki sai abun nasa ma ya bani dariya na jawosa jikina na Rumgume ina fadin"Haba babban mutum na Umma.Anum din ai yau zata dawo yi hakuri ka saki ranka kaji" Cikin muryan kuka yace"Da gaske yau zata dawo..? Da sauri na amsa mai da Insha Allahu sai ya saki ihu Ahmad na tayasa Amir na gefe an saka hannuwa aljihun wandonsa kamar wani babba na kallesa ina Dariya Hafsah ta fito daga Daki tana fadin"A'a yan jss ba zama ne yau..?a tsaye zamu tsaya..? Fuska yayi bai yi mgana ya Dauki Sabuwar Jakarsa ya rataya yana fadin"Umma yaran nan su zo mu tafi" Na bisu da Allah ya kiyaye hanya bayan na rike ma Ahmad jaka zan rakasu kofar gida Hafsah ta daga murya tana fadin"Amir shine ba mgana..?zaka zo ka same ni ne.." Muna gabda fita daga falon naji muryan Yaya Ishaq a sama yana fadin"Yaushe Amir ya fara zuwa makaranta ban sani ba..? Su sun riga sun fice sai na mikama Hafsah jakar Ahmad tabi bayan su ni kuma sai na Dawo tsakiyar falon, yana daga kofar Dakinsa alamun yanzu ya fito sanda zamu fita daga falon zuwa waje. Cikin sanyi na, na gaishesa ya amsa a gajarce yana sake fadin'Ko ba shi ba ne nagani da kayan makaranta ya fita da su Ahmad ba.? Kai tsaye nace"Shine ni naje nayi biya komai ranar jumma'a yau suka ce ya fara zuwa tunda karatu yayi nisa" Sai kawai ya tsaya yana kallo na Fa'iza ta sauya sauyin dake basa mamaki bai isa in zata yi abu ta nemi shawaransa ba, ance mai hali baya fasa halinsa kawai sai ya fara fada yana fadin"Meyasa kika raina ni ne Fa'iza kin ware ni kan sha'anin ya'ya na ban isa ki fadamin Amir zai fara zuwa makaranta ba sai dai ki rika yin komai kanki tsaye..?sai yanzu na yarda da mganar Mama, kina ganin yanzu kina samun kudi kina Dauke laluran kanki da na gida shine kike ganin zaki iya yanke hukuncyi kan ya'yana to baki isa ba,ba na so.." Ya karishe fad'a har yana nuna min yatsa kawai sai na saki baki ina kallonsa na kwaso gauron numfashi zan tare sa da mganar ya wuceni Fuu kamar kabubuwa ya fice sai Dakin Mama na bisa da kallo hannuna sabe da Haba na a fili na furta"Yau naji karfin hali ko na gani zencen ni Fa'iza" To in ba karfin hali ba sai yanzu kasan da ya'yan ka ne?a baya da kake banzar ta dasu ka zabi wasu akan su ba'ayi maka mgana ba sai yanzu ne kake da bakin mgana..? Kawai sai nayi tsaki na cigaba da Harkan gabana abun karyawansa ma sai Hafsah ya ma mgana ta basa, ni Daki na shige na kwanta a raina nace bazan sake yarda ka rika sakani Damuwa ba. Daman da kullatan fad'an safe ya shiga kuma Dakin Mama ta kara ma Wutar fetir, da yammah sai ga Direban Hajiya ya kawo Anum da sha tara na arziki kaya akwati guda nata ga kayan wasa har da karamar Ipad na game din yara,da Sabuwar jakar makaranta da littafai da kayan biki cike da Jakar bikin ga Hoton Amarya da ango nan sannan ga kudi dubu goma Sabbin yan Hamsim Hamsin a Cikin wata farar takarda,Harda takalma masu kyau sai sweet da chaculate na su musty,Anum da shigem kaud'i sai murna take yi bakinta ya tsinke da Labari har Yaya Ishaq dake ciki sai da ya fito,Yana kallon kayan Anum na ganinsa ta nufesa ta rikesa bakinta yaki yin shuru an bata kaza sun je kaza sun je kaza. Fuskarsa ba fara'a ko kad'an,kamar ta Fahimta ne yasa ta bar ta batunsa ta kwashe kayan taje ta nuna ma Mama Hafsah taso ta hanata nace ta kyaleta ta shiga ba dad'ewa sai gata tazo kiransa in ji Mama, ya tashi ya tafi ba jimawa sai ga shi ya shigo ina faman tattara sauran kayan da Anum ta watsar ya daga murya yana fadin"Daga yau ya'ta bazata kara zuwa wani gida kwadayi ba" Sai na Dago ina kallonsa ni yanzu ya Daina bani mamaki a baya sai nake ganin Rayuwa tasa yayi sanyi ammh daga Safiyar yau na Fahimci lambo yayi. Kamar zan yi mai mgana sai na fasa na zata shikenan kawai sai naji yana fadin"In ke zaki je kije, ammh kada ki kara tura ya'ata wani gida da sunan kwaad'ayi." Sai na sake dagowa ina kallonsa ban yi nauyin baki ba nace"to ai in dai kace naje kamar kace itama taje ne.Saboda ni ya'yana na zaba akan ka.Kai kuma ka manta ka zabi Zainab da iyalanta a kaina da ya'yanka..? Tsuramin ido yayi nasan yana mamakin kalamai na ne ni kuma ganin yaji mganata yasa na juya nayi shigewata Daki na barsa nan bansa ya yakare ba, Anum ta dawo da kayan ba jimawa su Amir suka dawo da ga makaranta sai Ihu ya tashi Anum ta Dawo labarai ta rika basu na abunda ya faru a chan har da abunda taci ta kwaso musu kayan suka yi min Baja baja da falo sai da na fito nayi musu fad'a Amir ya hau taya Anum tattara kayan yana fadin"Kiyi hakuri Umma zamu kwashe" Sai na Sassauta ina fadin"Lokacin sallah yayi ayi alwala ku tafi masallaci Anum tazo muyi namu a gida" Da haka suka kwashe kayan suka maida Dakinsu mazan suka fita alwala Babansu na dakin Mama ya tarasu suka tafi masallaci mu kuma mukayi namu agida ba abinci sai Hafsah tayi Taliya jallop,ta sa ka kazan da Anum tazo da shi na biki aciki,ita muka ci da Daddare kafin mu kwanta na raba ma yaran kayan Fulawan da Anum tazo da shi na Bikin harda lemuka na kuma aika ma Mama nata,ta kuma karb'e ko kunya, sai da safe na Kira Hajiya nayi mata godiya. Daga wannan lokacin sai ya Dawo sak Yaya Ishaq din da na sani mara ragowa sannan mai tsanani sai na Fahinmci,wani abu har da zafin Talauci ya sake firgitasa sai dai bai min tijaran da ya saba da agaban mama ko mutane, saboda yaga bakina ya bude yanzu zan maidasa mganar da bazai so ta fita wani yajita ba. Duk nayi biris da shi domin har ga Allah ba ina zaune saboda ina son sa ba ne,babu wani birbishin so a cikin zuciyata in a baya na so shi Saboda yana Uban ya'yana yanzu ko wannan Darajan bana dubawa,abu d'aya na sani ina zaune ne saboda ya'yana ba saboda shi ko jiginannen auransa ba. Shiyasa nake kama kaina ina chan ina Hidimar sana'ata da ga shi Har maman bana ta kansu,Anty Binta ma ta rage zuwa akai akai su Anty Mahma ma sai dai su leko mu ni kuma ban fasa abunda na yi niyya ba,Kananun lalurori har manyan ma ina Daukan su da sana'ar da nake yi,wannan zafin ran da na Talauci ban yarda na zauna ya saukemin ba,Ya saba in ya gama min Tijara na rika basa Hakuri ammh yanzu da ya fara in bana jin mgana zan bama banza ajiyarsa ko na bar masa wajen. A cikin wannan takun sakan da muke yi ne, kayan abinci suka kare dole ni na fidda kudi na siya Mama da gadara duk abunda take bukata zatace na bata kaza kamar ita nake yi ma wahalan,sai dai ban taba biye mata ba, ina ganin ta a matsayin uwa shiyasa ban taba Daga kai akanta ba. shi kuma komai nayi sai yace na rubuta in ya samu aiki zai Biyani ni ko nace shi ya Lissafa da kansa mana Muna cikin haka zazzabi ya Sarke sa kamar wasa ya kwantar da shi Ranar kwance ya yini Dakin mama,Yadda bai fad'amin ba shi da lafiya ba, nima ina da Miskilanci ko lekawa Dakin Maman ban yi ba ballatana nayi mai sannu Abakin su Amir naji Daada bai da lafiya, Mama ce ta leko da kanta Dakina da bata taba shigowa ba, sai dai ta tsaya daga bakin kofa tana ce min na bada kudi Amir ya raka Ishaq kemis bai jin dadi,kamar nace bani da shi sai kuma ban ce ba na ba ma Amir dubu biyu suka tafi a ka mishi allurai da mganguna ashe maleria ce ta kamasa,ni iya dakina da dakin yara nake siyan ma mganin Sauro na kunna sai Dakin Mama ban yi tunanin yana jin cizon sauro ba ma. Abu kamar wasa daga zazzabi sai zawo cikin dare haka ya kwana zagayawa,da safe har da Amai duk karfinsa ya kare,washegari daga zuwa bayi sai dai na je na daukosa duk ya bata jikinsa da amai da zawo duk yadda nake kauce ma wata mu'amalan ganin sirin juna tsakanina da shi sai da na yaye wannan Hijabin ranar,Tun kafin auran sa da Zainab ko Hannuna sai da kuskure yake gegata ballatana ganin juna a yanayin da bai dace ba,Sai ranar ni nayi masa wanka Maman dai bata yi masa rana ba,Ina yi ina kauce kauce shi kuma jiki yayi lakwas duk yayi laushi sai abun yayi min wani barambaram kwai namiji da suna Hajara. Bayan na yi masa wankan na koma na wanke bayin da kuma kayan shi da ya bata, sannan na fita baya damu kad'an inda Chemist yake na kira mai zaman wajen yazo ya gansa ya dora masa karin ruwa da allurai abu kamar wasa nan take sai da ya chajeni
Chapter 77 · 0% Book details