Sashe 85
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
nace mata toh. Ana gobe sallah na ba ma Mama kayan sallarta da Jamal har Anty Hure nayi ma Turmi,Mama ta karba a reni ko saka albarka bata yi ba,Jamal har daki ya biyoni yana godiya Yaya ishaq bayan ya gama ganin nasu Mama da yara bayan ya shiga daki na Dauko nasa na bashi duka an dinka,Hafsah ta ba wani dan ajin su yana dinkin maza ya dinka musu,suna mutumci da mai dinkin ne. Sai kawai Ya rumgumeni yana fadin"Nagode Fa'iza Nagode kwarai. Madallah da Fa"iza..Fa'iza matar Ishaq" Da wayau na zame jikina daman ina so nayi mai mgana kan Zainab Saboda ina jinsu tana ta kiransa baya son daukan wayarta, kan mganar zuwansa da azumi bai je ba Mama kuma tamai mgana bazai saurareta ba. Sai nayi amfani da wannan damar na sako mai mganar shuru yayi yana kallona kafin yace"kina so naje da sallah ne ke kuma fa da ya'yana..? Sai na jinjina kai ina fadin"itama ai matarkace tana da hakki akan ka, sannan itama tana da ya'ya suma kuma suna da hakki a kan ka" Kawai sai ya kuramin ido yana kallona kafin ya kama hannayena duka biyu ya rike lokaci daya yana fadin"Wata irin zuciya Allah ya yi ma Fa'iza..? Sai nayi mirmishi kai tsaye nace"Zuciyar hakuri da Takwali ne" Sai ya girgiza kai yana fadin"Da kuma zuciyar Diomod wanda samun mai macen aure irinta acikin maza dubu sai mai sa'a Fa'iza" Sunkuyar da kaina nayi ina jin jikina na yam yam! saboda yadda yake murza yan yatsuna,sai kawai naji Tattausan muryansa gabda kunnina yana fadin"Zuciyar Fa'iza me hakuri ce zuciyar Fa'iza mai biyayya ce da yafiya Allah yasa zata iya yafe ma Ishaq gigimemen laifin sa a gareta? Dagowa nayi ina kallonsa muka yi ma juna kir,kallo ne yake min cikin wani yanayi dake kassara zuciyar ko wata lafiyayyar diya macen da aka zaunar da ita, ana yi mata irin wannan kallon da Ishaq Kabir karofi ke bi na dashi" *Janafty* *KNKB2008* *Ki biya ki karanta cikin salama,Kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta min littafi,Sannan kada ki yad'amin shi,Pay N500 regular ko kuma VIP N1000, Via Jamila Umar Gt bank 0552179550,ban da tsarin kati wannan karon, a turo ta POS, Shaidar biya ta wannan lambar 09069067488* Ba iya kallon dake narkar da zuciya ba,Sai da ya had'a da langon Matso da jikinsa yana gogan jikina lokaci d'aya da Numfashinsa yana sauka a dokin wuyana,sai suka taimaka wajen fitar dani daga Hayyacina har ina shirin manta matsayina?ballatana da naji yadda hannayensa ke kara kaina acikin Hannayena. Ban dawo Hayyacina ba sai naji mganarsa a dokin wuyana gabda da bakina yana fadin"Fa'iza zaki iya yafe ma Ishaq.?zaki iya basa rayuwarki a karo na biyu..? Kamar an dawo dani cikin Hayyacina haka na zabura na mike jikina na rawa,yana shirin riko ni na fizge hannuna na fice daga Dakin da Sauri zuwa Dakina,bai biyo ni ba ina tunanin Saboda ganin yara ne,ni ko gado na na fada ina kokarin daidaita kaina Sai kuma daga baya naga wautata na manta matsayina ne da zai rudeni na saki jiki..? Meyasa sai yanzu yake tunanin yayi min laifi yake neman gafarata..? Ko ya manta nice dai Fa'izan da ya sani yar gargajiya kurma mara ilimi da gata baka mummuna ko ya manta wad'anan nakasun a tare da ni ne..? Sai naji bana son na fita mu kara haduwa,Na shige daki duk hayaniyar yara da buruntun su naki fitowa ina jin su afalo yana ta sha'aninsa da yara da Hafsah sai washegari Ranar idi muka had'u shima gaishe shi kawai nayi sai ya amsa yana wani kafe ni da ido nayi saurin kauce ma kallonsa. Da shi da yaran suka shirya gabadaya har da Jamal,sai a ranar naga ya Dawo da gayunsa sai dai ba kamar da ba,da zasu tafi masallaci muna tsakar gida muna tuwon Shinkafa miyar agushi ni da Hafsah ban sani ba naji ya karkato wajen kunnena yana fadin"Ishaq na jiran wankan sallar Fa'iza domin ya tanadar mata babban Tukwaici" Sai na tsorata garin juyowa saura kad'an na fada tukunyar miya ya saka Hannu ya tareni yana fadin"Ki kula da kada ki yi min asara" Sai na sunkuyar da kai ganin Hafsah na Dariya sai ya bi bayan su jamal yama Fadin"Hafsty ki kular min da matata kada ta fada cikin miya ta ragemin kara'in da na shirya mana da sallar nan" Har ya fice ina kara jinjina mamakinsa,Hafsah ma ta kalleni tana fadin"Naji dadi Yaya fa'iza yaya Ishaq ya sauya kamar ba shi ba" Saboda bana cikin yanayin mgana yasa ko tankata ban yi ba. Ba su jima da fita ba muka gama komai ni na wanke tsarkar gida Hafsah tayi wanke wanke,Ni nace taje tayi wanka na fara gyaran Dakin data gama ta shirya sai tazo ta karbeni itama Goggo ta aiko mata da kayan salla na kala Biyu. Ba domin ya roka ba sai domin daman nayi ra'ayin cin kwalliyata da gumina sai na saka wata karamar super waz din da na siya ta Dubu Goma sha biyu,mai kalan ja da fari dinkin riga da zani ne ammh rigar fited ce ta kama jikina Dam na saka Sabbin Dan kunne da sakarna da abun Hamnu,Ban yi kitso ba sai dai na wanke kaina na tufke Hafsah ce zata min kitso kuma bata samu damar min ba, saboda layin yan lalli taje karofi tayi gabda sallah ta dawo wajena Anum kad'ai tayi ma kitso,ni kuma aiki yayi min yawa ballatana daman ni ba yar kwalliya bace. Ko kafin su dawo na aika ma da Mama nata tuwon da naman salla sannan zobo na musamman nayi saboda gida da sallah,Na kuma shiga da kaina har daki na gaishe su nayi musu barka da sallah Anty Hure ta amsani da fara'a Maama ko sama sama tana kallona tana tabe baki ban damu ba,na fita ko ba soso da sabulu sannan na sauke nauyi. Suna dawowa suma abincin na kasa musu suka ci,shi ko sabon mijin nawa sai kallona yake yi,to sabon mijina mana Tunda komai ya sauya,ashe ban sani ba Hoto ya dinga Daukana sai da naji Anum na fadin"Laa Umma zo ki ganki a wayar Daada" Sai na juya ina kallonsa sai ya basar yana dagamin gira jijjiga kaina nayi a raina ina tambayan kaina wannan chanjin duk na menene..? Duk yadda yaso ya samu kebewa dani naki basa daman hakan,washegarin sallah da kwana Biyu na samu ya tafi Abuja kudin mota ma ni na bashi ya tafi bayan ya jaddamin in ya dawo yana so zamu yi mgana nace Allah ya Dawo da shi lafiya. Ya bamu izinin tafiya yawon sallah Shiyasa ban zauna a gidan ba, muka sha yawo ni da yara da Hafsah har gidan Anty mahma mun je da gidan Hajiya,na leka har anguwan da muka taso mun yi zumumci da makotan arziki su Sa'adatu yini zir mukayi sannan muka dawo ita kuma Mama tana gida ita da ya'yanta su Anty Binta washegari da wuri muka gama girki shinkafa da miya nayi da Salat na saka a babban cooler sai karofi da na shiga gayama Mama chan zamu kwana sai gobe zamu dawo sai ta kalleni tana fadin"To in kin tafi da yunwa kike so ki bar ni kenan..? Zan yi mgana kenan Anty Hure,ta karbeni da fadin"Kyaleta taje baka ga ni ba, zan yi mana girkin" Ba dai a son ran Mama muka tafi karofi ba,Chan ko naga yan'uwana har Yaya Asiya nan tayi sallah ita da iyalanta ga Yaya mariya da sai dai mu hadu a karofi har yau ina jin takaicin wannan abun in na tuna. Kowa ya ganni sai yace na sauya kamar bani ba ni kaina nasan na samu kwanciyar hankali ba kamar baya ba sannan sana'ata ta taimakamin wajen inganta rayuwata mun sha ziyara a karofi ni da yara da su Yaya Asiya mune har gidan kakanin mu Baba ati na gidan muka gaisheta tare da yi mata barka da sallah ko alokacin sai da muka mata mganar dan'uwan Tamadina ko an ji Labarinsa tace har yanzu shuru. Duk aranar mukaje har Cikin garin Dutsemah muka gaishe da abokan zaman Tamadina kuma sun ji dadi sosai suna saka albarka ballatana da Yaya Asiya taje musu da Nama da cincin din da tayi suna saka rika albarka su da megidan da ya'yan su. Daga kwana daya sai ga shi sai da nayi Biyu Shima sai da Goggo ta yi fad'a sannan muka koma,aiko Mama ta cika Fam kamar zata fashe,Sai kananun mganganu take yi wai an barta ita kadai a gida,mamakinta ya kamani wani irin ita kad'ai..?ina jamal ina Badar..?ga Anty Hure ga Anty Binta da iyalanta nasan nan suka yi bidirin su,ammh saboda korafinta a kaina baya karewa sai da ta tofa ni dai ban ma yi lokacin ta ba shi kuma wanda ta saba zaunar da shi tayi din har ya yi lokacin nata baya nan dole ta kama bakinta tayi gum. Muna dawowa na cigaba da sana'ata saboda yan makaranta da masu sari,Ranar da Yaya ishaq ya cika sati da Tafiya da Daddare sai ga zainab ta kirani a waya daman da Maman Fadil na saka akayi mata Saving wayar na Hannun Anum ta kafa mata kahon zuka duk ta saka Hafsah ta cika min waya da game game gwara ma Amir shi karatun Qur'ani yaje aka turo masa saboda Haddansa ammh Anum Sai shiririta ko na hanata Dauka sai tayi dubara ta dauka,Ga shi kamar aljanna ko ni ta fini sanin kan wayar in an gama game ayi ta daukan Hotunan banza duk ta cikamin waya. To ranar ma wayar na hannun su ni kuma ina kitchen ina gyara aya na kunin Ayan gobe saboda Ayan Hafsah bata duba ba,duk akwai datti ajiki sai ya samu gyara. Anum ce ta rugo ta zo ta kawo min wayar tana fadin"Umma..umma ana kiran ki" Karba nayi ina kurama sunan ido,yanzu na kan iya karanta suna naga maman fadil sai na rasa ma wajen Dauka,Anum ya kallah ina fadin"Anum matsa min wajen daukan" Sai ta karba tana dariya Lokaci d'aya tace"Umma ni fa nasan bazaki iya dauka ba tunda naga kina Zare ido" Kanta na mangara ina fadin"Gidan ku Anum" Dariya take yi lokaci daya ta Daga kiran bayan tace"Umma a saka