← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 175

Sashe 3

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

na wankesu domin Fa'iza in akwai abunda ta tsana kwano ya kwanar mata akitchen ba'a wanke ba. Ita dai barta da barin shirgin yara da Rashin Shiga mai Fasali ammh ita da ya'yanta basu da kazanta ko yaya ne wanka ne Safe da yammah ita da yaran Duk Ranar duniya har sun saba suma. Sai da nagama na kara leka Dakin na wajen Ahmad in sauri ban tsaya na Tofe shi da addu'a ba yasa na bata Lokaci Wajen Yimai addu'a Hafsatu bata Dakin kila tana Dakin datake sauka in tazo Gidan. Dayake nayi wanka Dazu da mangariba ban yi Tunanin Sake wani wankan ba na Sauya kayana zuwa wata Dogouwar Riga ta barci mai Taushi mai gajeren hannu,Duk da ina na da masu wando basa Burgeni nafi son Dogayen masu rufe min Har Cinyoyina Fa'iza ta Tsani ta saka kaya taga sun kamata ko sun nuna Tsiraicinta. Ina cikin Daure gashin kaina Da na Tsefe shi yau da Safe,Hafsatu ce zata min Kitso yau bata samu Dama ba Karfanfan gashina tun na Virgin Dakyar yake Haduwa cika garesa bai da Tsawo inaa Hakin kamasa na Daure cikin Ribbon baji muryan ISHAQ asama yana Faman kiran sunana kamar yadda ya saba. "FA'IZA.." "FA'IZA.." Da sauri na bar abunda nake yi lokaci daya na Rarumi Hulata ta barci na Saka ina niyar fitowa Daga Dakin ya shigo,ganinsa Tsaye a gaban ba Kikam da irin kallon Dayake min yasa nq rankwafa da Sauri ina Fadin"Gani ina..ina..! Ban karisa ba ya Daga min Hannu Lokaci Daya yana Fadin"FA"IZA hala baki sam zan kara aure bane..? Yafada yana Tsareni da manyan Idanuwansa. Gabanna ya Fadi Ras! Sai na Daburce Da yanayin da yayi mganar,ba da karfi bane sai dai ai mganar auran nasa na Haddace ta akaina shiyasa nq karancin Bakinsa. Cikin Fusata yace"Wai bada ke nake mgana bane kikamin banza..? Da Sauri nace"Eh..Eh..Na sani..Mamakofar soro ta fadamin..Sannan sannan.." Daka min tsawa yayi yana Fadin"Sannan me..? Kinsan bana son wannan sanyin naki in muna mgana ko..? Mgana bata kai ta kawo ba kiyi ta uban Rabata kamar wani abun arziki zaki Fada.." Kokarim Boye Raunina nayi Cikin Dakewa nace"Anty Binta batagwara ta Fadamin wanchan satin da muka Hadu gidan Mama." Wata Uwar Harara ya jefa min kafin yace"Kin sani ammh ko Fatan Alheri bazaki min ba Fa"iza..? Kina bakinciki ne saboda zan kara aure..? Da Sauri nace"Ahah.Naga baka nan ne,Shiyasa.." Takaici ya kamasa kafin yace"Baki da waya ne..? Ko lambatace baki da ita..? Koda yake ke ai ba matar kiran jin Lafiyan miji bace za dai ki kira in wata Bukatarki ta taso miki." Ya karishe Fada yana kallona Cikin Doguwar Rigar Barcin dana sanya kadan ya Rage bai yi Dariya ba. Dariyan Takaichi wai zaki kwana da Miji ki saka wannan abu kamar kullib goro. Karamin Tsaki yaja kafin yace"Na zata kina Bakinciki ne nace kin so kanki Fa'iza Shekara Takwas nayi ina Zaune Dake ban kara aure ba..Tsakaninki ga Allah ban miki alfarma da Mutumci ba Fa"iza..? Fadamin da bakin ki na yi miki adalci ko ban yi miki ba..? Ya fada da karfi yadda Zan jisa jikina na rawa nace"kaayi min..sosai kayi min adalci.." Naso na Daure ammh ina Raunina ya bada ni sai kuka hawaye sharr Tsayawa yayi yana kallon na kafin ya Tabe baki yace"Naji Dadi da kika Fahimci haka..Kada Goggon karofi da yan'uwanki su tasaki suna Faman tambayanki kice musu ban yi miki adalci ba kiga yadda zamu kwashe.." Malama ki kuma cire min wannan bargon Dake jikin ki wlh matukar wajena zaki kwana na Haramta miki kara sakamin wadanan Rigunan ai ba Cinikaya zamu yi ba..Ke kinga ma sha ma Zamanki ana tabaki Ke mai cikin Haihuwa Zan D'aure nan da Wata D'aya ne kamar gobe ne.." Yafad'a Lokaci D'aya ya juya zai Fice Daga Dakin na Bisa da kallo ina D'igar kwallah duk da ba Duka mganarsa na ji ba ammh nasan yana kushe ni ne kamar yadda ya saba. Har ya fita Daga Dakin ni kuma har na juya kawai naji dawowarsa da kara Kiran sunana da yayi da karfi. "FA'IZA..! Da Sauri na Juyo Cikin muryata Data Fara sauyawa saboda kuka nace"Na'am..! Kallona ya tsaya yanayi lokaci d'aya yana rike da Kofar Cikin Mamaki na yace"Kuka..? Na Dake ki ne..? Da Sauri na Share hawayena ina Fadin"A"ah kamar wani abu ne ya Fadamim a ido na..!" Bai Damu ba Kafad'a ya Zakud'a kafin yace"Mama ta fada miki gidana na Abuja Zeey zata zauna..? Kai na gyada mai bai bani Damar mgana ba yacigaba da Fadin"Fa'iza kinga barin yaran nan suna bata gidan nan Duka duka yaushe muka tare acikinsa ammh kalli yadda suka maidasa..? Komai naki ba kula ba Lura..? Ko da yake ke kanki abar akula Dake ne bama ki kula da wani ba Anyway dai tunda kuka lalata gidan in ma mugunta ce ke zata ci..Sai da Safe.." Daga haka ya Sakar min kofa ya fice na Bisa da kallo hawayena na kara cika Idanuwana ina jinsa ya Bude kofa ya shiga D'akin yaransa ya Dade kafin naji ya Fito ya Tafi bangaransa. Kamar wacce aka Mangara kawai sai na fashe da kuka wiwi,Sai kuma nahau Rufe Bakina,lokaci D'aya da wayata Dake samam madubin dakin ta D'auki Karan neman agaji. Da Sauri na mike na nufi wayar kirar Kamfanin Itel karama Tunda Anum tataba Fasa min Sreen din Samsumg din da Ya Ishaq ya siya min bai kara siya min wata babbar wayar ba ya Had'ani da karama acewarsa ba amfanin ma Siyan min Shafa shafan tunda ba iyawa nayi ba, ta bakinsa Fa'iza ba turanci. Gabana sai da ya amsa ganin wacce ke Kirana Maman Naja ce Yaya ASIYA,Sunan d'iyarta ta fari ce wacce ta rasu Naja'atu ammh dayake sunan ya riga ya bita da Maman naja ake kiranta. *ASSALAMU ALAIKUM* *KAYA SUN SAKE SAUKA*. *INGANTATUN SAIWOWI DA SASSAKE NE DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZA DA SU*. *ABIN BIRGEWA BA SAU DAYA AKE AMFANI DA SHI BA. SANNAN BASU DA BAURI MASU KIDIMARWA*. *KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR KO KUWA KE DA KANKI ZAKI YI GYARA?* *INA SAKE YIN ALBISHIR DIN GARIN DAKA MAI KYAU DAN CHADI, SHA DA MADARA KO NONO DA KUMA TSUMIN GAMGAM*. *INA DA TABBACIN INGANCINSU*. *TUNTU'BI WANNAN LAMBAR DOMIN KARIN BAYANI* *08032773332*. *SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE* *Janafty**KANA NAKA...* *Wattpad:Jamilaumar351* *Mallakar:Janafty* *Arewabook:Jamilaumarjanafty* *Fatan alheri gareki SURAYYAH DAHIRU GWARAM,Madallah da kawar arziki irin ki da karfafa Gwiwarki,Labarin nan yazo ma masu karatu Ina miki fatan alheri a koda yaushe na gaida Uwar Dakin Sa'ada da Gudiyo,sannan na ce Madallah da Uwar Dakin Yabi* Da sauri na share Hawayena nayi kokarin daidaita yanayina domin ni Fa'iza ko Uwar data Haife ni bana kaunar taga raunina ballatana yan'uwana da kullum suke kallona abar Tausayi wacce batayi dacen Gidan aure ba acewar su. Saboda yanayin Raunin ji na, in aka kirani a waya a speaker nake saka ta wato amsa kuwwa yanzu din ma haka nayi na Daga kiran sannan na saka a speaker daidai Lokacin da naji muryan Ya Asiya na kiran sunana na amsa mata cikin dan D'aga murya. Dagachan bangaran Ya Asiya tace"Fa'iza Ashe Yaya Ishaq zai kara aure bamu sani ba..? Fa'iza tayi wani mirmishin yak'e kafin tace"Eh Yaya Asiya zai kaara aure.." Ya Asiya tace"Shi ne baki Fadamin ba, kuma baki fada ma Mariya ba ko..? Fa'iza tayi shuru batayi mgana ba Ya Asiya Haushi ya kamata ta fara Fada Tana Fadin"Kila ma baki sani ba..? Domin sai ma an Dauke ka da Daraja da kima ne ake sanar dakai wani abun." Da Sauri nace"Aaha nasani fa..Wlh na sani Mama ta fadamin sannan Anty Binta batagarawa itama ta fadamin." Ya Asiya Dagachan bangaran ta jimjina kai kafin tace"Shi Uban gayyar bai Samu Fada miki ba kenan..? Sai a bakin Uwarsa da yayarsa kike ji kenan..? Anya Fa'iza wannan Rayuwar zata tafi ahaka kuwa..? Shekara Takwas ai ba kwanaki Takwas bane." Fa'iza ta share hawayenta da suka zubo mata kafin tace"Ai shima ya fadamin yau daya dawo.." Ya Asiya tace"Umhh..! Saboda takaici ma ta kasa mgana,Fa'iza kuma Daman ba ma'abociya mgana bace Ya Asiya Tagaji da shurun Fa'iza yasa ta katse mganar da cewa"Goggon Karofi ke Fadamin Zai yi aure yanzu muka gama waya da ita..Ita kema Fadamin Hafsatu tazo wajen ki shekaran jiya." Fa'iza tace"Eh tazo shekaran jiya..tazo..." Sai ta saki wanchan mganar Saboda bata son tayi Tsawo ita kanta Ya Asiya ai ta sani Fa'iza bata kaunar mganar Data Danganci Ishaq da Danginsa in ma ka matsa sai ta saka maka kuka Ajiyar rai ta sauke kafin tace"Yaushe ne Bikin..? Fa"iza tace"Bansani ba.." Ya Asiya tace"Allah ya kyauta zan shigo katsinar nima In nazo Duba Tamadina hala ba ma kiji bata ji Dadi ba..? Ciwon kafafu take fama dashi." Fa'iza tace"Naji Da Hafsatu tazo ta Fadamim." Ya Asiya tace"Yaushe zaki leka ki Dubata ke da ke kusa ma Fa'iza yaushe Rabon ki da Dutsenmah Tun Sanda Ta madina ta kwanta asibiti an kusa shekara fa" Fa'iza tayi shuru ta kasa mgana Saboda bata da tacewa Ishaq ne baya barinta tana son zuwa inda Mahaifiyarta take sai yace me zataje yi tana gidan wani..? Ya'yansa bazasu je gidan wani suna Rab'e Rab'e ba. Ya Asiya tayi shuru yasa ta kyaleta sai ta shigo da mganar"Ina yaran nan..? Hala sun yi barci..? Ta amsa mata Ya Asiya tace"Shikenan Sai mun shigo zamu karisawa Tattauna ki kara Hakuri Fa'iza kowani bawa da irin tasa kaddaran..Mu Tamu kaddaran Rasuwar Baba ne itace silar Shigar mu duk Halin da muka shiga." Fa'iza tace"Haka ne Daman ai KANA NAKA ne Allah na nashi ne..Sannan na Allah ne Daidai." Ya Asiya na jinjina kai tana Fadin"Hakane Fa'iza Allah ya mana mai kyau..Mu kwana Lafiya. Fa'iza ta rakata da Fadin ta gaida yaranta Daga haka sukayi sallama Sannan na ijiye wayar nq koma gefen gado na zauna ina mai kura ma Madubi Ido duk da ance ba kyau kallon kai a madubi in Duhu ya shiga ammh ni sai ta samu kaina da kare ma Jikinna kallo. Tare da Fuskata ina Ayyana adadin Lokuta nawa ya Ishaq ya kalleni ya yab'a min..? Koda yaushe cikin kusheni yake yi an samu ma bayan sun fara Tara zuru'a ya Daina jifana da kalmar Mummuna ammh kalmar Baka sai dai in yan Cin mutumcinsa basa
Chapter 3 · 0% Book details