Sashe 101
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da ilimi daga karshe hakan bai amfaneni da komai ba.." Da Sauri nace"Ya amfaneka mana Zainab na sonka sannan kuma ta fara tara maka irin zuru'ar daka ke so" Idanuwansa Jajir ya d'ago yana kallona kafin yace"Bata so na, in da tana so na,da bata fifita ta mganar mahaifinta akan nawa ba. Tana ganin tana da kyau alfarma tamin data aureni,Tana ganin tana da ilimin da Taimakona tayi ta aure ni,tana ganin tana da Gatan da ban isa da ita ba. kaico na da nabi Rudin duniya da Rudin Shed'an,ga shi yanzu ina Nadama Shiyasa duk wanda bai bi Turban Annabi ba, tun a duniya zai Tabe Annabi ya fad'ama mu auri mai addini domin itace mafi kyawun cikin su" Dagani Har Mama ba wacce tayi mgana ita kunya da Sanyi ni kuma na shiga wani yanayi mara Dadi a lokacin. Shuru yayi yana sauke Numfashi kafin yace"Mahaifinta bai Daukeni a bakin komai ba,gani yake taimakona yayi alfarma ya yi min don ya bani auran yarsa shiyasa yake takani yadda yaga dama har cikin gidan nan ya tako ya ci zarafina na, kasa komai ammh wannan karon wlh bai isa ba. sai na nuna masa na fisa cikakken iko da yar tashi ta zubar da cikin ta gani Sai dai kuma a bi wani Sarkin" Da haka ya shuru takalmansa yayi waje Mama na kiransa bai ko Juyo ba,Ni dai nace Allah ya kyauta na koma ina cigaba da wanke wanke na, Mama na Tsaye ta kasa gaba ballatana baya har ga Allah ba wai dadi naji ba ammh raina bai baci ba,Gwara su fara gani Tun yanzu ban ga laifin su ba,Irin Rariyan da ya siya ne kuma don tayi zubar ruwa shatata bai kamata yayi korafi ba. Ina gama aikina na shige Daki abuna,Na fara wata Hidiman yaran kuma karatu na iske su suna yi,Duk da nasan suna jin tashin mganar Baban nasu daga falon,tsakar gida na fito zan Dafa zobo na,Sai naga Mama an kwashi kafafun da sanyin jiki ta koma Daki Ranar sai dare ya shigo gidan ajaran majaran a falo ya fadi kan kujera yana sauke Nunfashi ina mai sannu da zuwa ya amsani a Dake kafin yace na sama mai ruwan wanka. Sai da ya rarrafa ya shiga Dakinsa na bisa na kai masa wayarsa da ya fasa da tawa ina fad'in"Ga shi matarka nata kira, tana son mgana dakai" Domin tun bayan La'asar Zainab ke kirana tana tambayansa nace mata ya fita ta Dameni ta kira yafi sau goma Daga gani bata cikin natsuwarta ne. Yana cire rigan jikinsa ya d'ago yana kallona ina shirin ficewa yace"Dawo ki Dauki wayarki" A kausashe nako ki dawowa na fice ina jinsa yana fadin"Lalle itama ko zan fasata wlh" a fili na furta"Kana fasamin waya zaka biyani kayana" Daganan na fita zuwa kitchen sai da ruwan yayi zafi sannan na juye mai na ba ma Amir ya kai mai ban koma Dakin ba, abinci ma Anum ta shigar mai da shi yaran suna falo suna karatu ni kuma ina Daki,Hafsah na gefe na muna mgana sai ga shi ya shigo daga gani yanzu ya fito wanka ga kansa nan na digar da ruwa yana shigowa yace"Hafsah jeki falo wajen yara zan yi mgana da yayarki" Ba musu ta fice ya kariso gabana yana fadin"Ki ka bama Amir ruwan zafi in ya kona sa fa..? Sai na kallesa kafin nace"Ba yau ya saba dauka ba, zai iya ne" Sai ya kuramin ido kafin yace"Ba kyau Fa'iza na horu fa don Allah ki yi hakuri".ganin ya fara sauya mganar yasa na mike na fice,na bar masa Dakin jiki a sanyaye ya koma Dakinsa ya shirya abincin ma afalo ya fito ya ci,Ina gefe sai kallona yake yi ni ko nayi kamar ban gansa ba. Wayata sai washgari ya aiko Anum da ita, ban ko Duba ko sun yi mgana ba. ammh naga an kirani Hafsah ta Dubamin tace Abba ne da Nana Fatima daman sune rana bata fitowa ta fadi basu kirani sun ji lafiyata ni da yara na ba,Har ga Allah ina kaunar Nana Fatima kamar yadda take kaunata,Sai da na natsa sannan na kirata muka gaisa sai tace measurement din yara da nawa take so na Rubuto mata sai nace ta bari sai Hafsah ta dawo zata turo mata,mun cigaba da mgana duk akan Bikin Yaya Abdul'Ahad ne da Raliya bayan sallah Tana fadamin Nana Fadila ta fitar mana da anko imu imu gabadayanmu,Na lura suna ji da Bikin nan ko don shine na farkon da zasu fara na Namiji, barin ma Ammi kamar Abdul'Ahad ba yaron ta na fari ba,ba ruwanta da kawaici da ita ake shiryawa komai. Abba kuma daman ba mazauni ne ba ne tafiya na yawan kamasa Ammi ce akan komai. Da Hafsah ta dawo na saka ta tura mata har da na takalmaa,Ban san cewa Yaya Ishaq bai yi mgana da Zainab ba, sai da ta kara kirana bayan na Dauka mun gaisa sai ta sakamin kuka na rud'e na zata ma ko wani abun ne ya faru cikin Kid'ima nace"Lafiya Maman Fadil..?. Cikin kuka tace"Maman Amir ki saka baki Honey ya daina fushi dani wlh ba laifina ba ne. Daddy ne ya matsa kuma ni nace mai bana so tunda Honey baya so kuma ba'a cire cikin ba. wlh nayi ta kiran sa wayarsa a kashe bana samun sa" Sai shesshekan kukan ta, na fara lallashinta kafin nace"Daman jiya baku yi mgana ba ne da na kai masa wayar ..? Da Sauri tace"kashewa ya dinga yi Maman Amir yaki ya saurareni ma, Daddy fa har fushi yake yi dani saboda naki amincewa da mganarsa Maman Amir don Allah ki basa hakuri wlh ban cire cikin ba, yana nan kada yace zai sakeni wlh ina son mijina" Sai ta bani Tausayi cikin sanyi na nace"Kiyi hakuri ki daina kuka in ya Shigo zan mai mgana" Da haka muka rabu sai mganarta ta Tsayamin arai, tana son mijinta har ga Allah nice shaida,ammh Mahaifinta ne ya riga ya saba da juya al'amarin ya'yansa,Ni kuma na kudiri niyar daidaita Tsakaninsu saboda itace Dahir dinsa,Da ya shigo Dakin Mama ya tsaya,sai da ya jima sannan ya shigo Dakina yara suka mike suna mai Sannu da zuwa Dakinsa ya shige Saboda ina da mgana dashi da kaina na tafi kai masa abinci,yana zaune ya yi Tagumi ammh yana ganina sai ya cire Tagumi,sannu da zuwa nayi masa na sauke mai abincin a gabansa ya jawo yana fadin"Me muka samu ne..? Ina zama nesa da shi nace"dambun Shinkafa ne da zogale" Cikin yanayin sa yace"Salon ya shake mu Fa'iza"ina Dariya nace"Tuwo naso nayi ban samu gyad'a ba,sai yara sukace Umma ki yi mana Dambu" Bai ce komai ba sai da ya tashi ya wanko hannunsa ya fara ci sannan yace"Ko bakomai zamu dora da zobo mai sanyi" Yafad'a yana kashe min ido sai nayi dariya yana ci muna hira,Sai da ya gama ya kuma dora zobo mai sanyi kamar yadda yace sannan na sako mai mganar Zainab kici kici yayi da Fuska kafin yace"Ina ruwanki da wannan mganar Fa'iza..? Na rausayar dakai nace"Da ruwana mana ai yar'uwata ce musulma kuma shi ai sulhu alheri ne" Sai kawai ya mike yana fadin"To ki cire bakin ki a ciki ba ruwanki ahto.." Sai naga daga taimako kawai sai na tattara kwanukan daya bata na fice ina fadin"Allah ya kyauta" Da gatse ya amsamin da Ameen sai abun ya bani Dariya a raina nace mata da miji sai Allah sai su shirya ma ban sani ba. Kuma saboda Zainab din yaki kai wayarsa ya gyara. ya gwammace ya zauna ba waya nidai tunda yace ba ruwana na cire bakina data kara kirana,sai nace mata nayi mgana yace zai kirata in ya gyara wayarsa Da dai taga ba Nemanta zai yi ba an fara azumi Takwas sai gata ta iso,ita kadai ko Farhan bata zo da shi ba, ta yayesa yana gidan su Tace ko Daddy bai son ta taho ba Shari'a har Falon Mama ammh Gogan ka yace shi fa ya gaji kowa yayi ta kansa baiwar Allah sai kuka take yi a raina nace ita kuma nata Jarabawar kenan na soyayya Allah yasa mu dace. Yadda yake yi mata ban dauka zai iya kallonta ba, ammh dayake Namiji sunnsa Namiji sai ga shi sun shirya an shiga kurya an yi lamo,Daganan na san sha'anin mata da miji sai Allah Shi da har masifa ya rikamin wai na ce ta tafi nace dayake ni na kawo ta ba,Bata koma ba sai da suka Daidaita da juna kwananta Biyar ta koma Abuja,motar Haya ta shiga abunda bata tayi ba ammh ga shi Namiji ya sakata acikin wani Hali. Ni daman tunda yace na cire bakina na kama kaina, ko da tazo ta zaunar dani tana gayamin har abunda ma bansani ba iyakata da ita hakuri kawai Domin kamar yadda yace ba ruwana to ba ruwana din. Mun yi azumi sha biyar Hafsah suka samu Huta,Washegari Yaya Abdul'Ahad yazo wajen Raliya shi ya wuce da ita Tare da Anum da Laila ta matsa sai an zo mata da ita haka kurum Allah ya hada kaunarta da Anum da taji ma dagantarkar dake Tsakani sai tace daman ba haka kawai take kaunar Anum ba ashe jini d'aya muke da mijinta. Musty har da kuka akan sai ya bi Anum Dakyar Babansa ya Lallashesa akan zamu je da sallah sannan ya Hakura,Azumi nada ashirin da Biyar sakon Abba na kayan sallarmu ya iso karofi aka kai,Yaya Isa ya kawo min nawa har gida duka da ni da yara. Har da Babansu,kala biyar biyar,harda na Anum data ke chan Da na Hafsah kenan wasu za'a sake dinka musu Yaya mariya haka aka kai mata nata ita da Yaya Asiya,Bakina yaki Rufuwa na kira Abba ina masa godiya sai yace"Ba godiya tsakanimu Fa'iza duk abunda nayi muku ba komai ba ne, ku ya'ya na ne kamar yadda zan yi ma Nana Fadila haka zan yi muku" Sai na kasa mgana,Saboda farinciki ya gamamin komai ganin ba na Mama aciki sai na saka kudi na siya mata kala uku har da Hijabi da takalmi ta karba Karo na farko da Mama ta taba godemin bayan nayi mata wani abun alheri.. Shi kuma Yaya ishaq da nace