Sashe 58
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shige ciki ni me zan ci..? Sai nayi s huru ban ce komai ba ya kara maimaita mganarsa ya karishe da fadin"ina jin yunwa kuma ban tsaya gidan mama naci abinci ba' Cikin yanayin mgana tace"Sai Faten in zaka sha..? Yadda yayi da fuska ne sai da naji kamar nayi dariya sai dai na kanne cikin kaushinsa yace"ki sama min wani abu" Ko bakomai yaci darajan Zumunci da ya'yan da suka had'amu sai na juya zuwa Kitchen ina fadin"Sai dai shinkafa ita kad'ai garemu" Ina jinsa ya mike yana fadin"Dafamin ki yi min source din miya tunda naga akwai kayan miya dare yayi ba na son na sake fita ne" A daran nan ma dafamai Shinkafa araina ina kallon gas d'ina ina godema Wutar nepa ba domin anguwar da muke ana barin wuta ba, da tuni na raina kaina Gas ne mai shidda,wanda ke amfani da Gas da Electric,basan shekara nawa na kwashe ina amfani da shi da wuta ba, tun Auran Ya Ishaq da Tarewansa a Abuja komai ya sauya,a baya yana mana Refliing ko ya aiko Jamal ya yi mana, ammh daga baya komai ya sauya sai da nayi da mai wuta,shi kuma baya da saurin girki,tunda bani da wata mafita hakanan nake hakuri da shi,Daman gas din Yaya Ishaq ya siya san da zamu dawo gidan. Har goma da wani abu sannan na gama na had'a komai na kai masa shashensa a falo na sauke mai komai yana ciki ko bari ya fito ban yi ba na koma Dakina nayi shirin kwanciya,na kwanta sai barci ban farka ba sai asuba,bayan na idar da sallah nayi ma yara shirin tafiya makaranta saboda yau Jumm'a ne basa dad'ewa sai basu je da Kwandon abinci ba sai ruwa da na Dura musu suna shirin fita su yi ma Haruna mgana sai ga shi ya fito yace zai kaisu suna ta tsallen murna. Shi ya kwashe shi suka fita ya kai su sai wajen goma ya shigo gidan,da amajirai guda biyu suna ta shigowa da kaya,kayan abinci ne ya siyo masu yawa har da Biskit din yara da Lemun su da ruwa har da kayan Tea wanda har yaran sun manta da shi sun saba da kunu har da su kwai kayan miya da kayan lambu,Dankalin Turawa da yawa haka ya siyo ina zaune ina karishe ma yaran guga afalo sannu da zuwa kawai nayi mai na juya na cigaba da aikin gabana har ya sallami yaran ya shige shashensa ya sake fitowa kayan na nan zube afalo ban kauda su ba cikin fad'a da bacin rai yace"Wai fa'iza wani salon iskanci kuma kika samo..? Na dago ina kallonsa ya cigaba da Fadin"nine kike nufin zan kwashe wad'anan kayan ko me kike nufi..? Ban ce komai ba na kashe soket din Abun gugan, na wuce na fara Daukan kayan ina shiga dasu ni ko na daina rawan jikin kan abunda bazai D'ore ba Sai da na kwashe duka na shirya komai a muhallinsa ina shirin na koma na cigaba da aikin gabana yace"ki sama min abunda zan ci" Kamar nace zainab bata aiko maka dashi ba ne..? Sai na fasa rashin kunya ba Halina ba ne sai na Tashi na shiga kitchen dafamai mai Dankalin Turawa nayi,sai nayi mai miyar kabeji da taji albasa sai na Dafa mai ruwan tea na Dafa mai kwai guda biyu kuma duka na Tattaramai ko abakina domin na koshi Faten jiya na dumama nasha abuna yaran, kuma Farar shinkafa na Dafamusu da Mai da yaji sukaci kafin su tafi makaranta. Yana zaune afalon na kawo mai ya kalli Filet da jug din da na sanya mai Ruwan zafin kai tsaye yace"Gabad'aya komai naki ya tsufa Fa'iza..Ji kwanukan cin abinci sun fita Hayyacin su mtswww.." Ya saki tsaki daga karshe ina jinsa ban ce masa komai ba na koma na cigaba da aikin gabana,sai da na gama na kashe komai na kwashe zan koma Daki naji ya daga murya yana fadin"Ki shirya in yara suka dawo makaranta zamu je gidan Mama a gabanta sai ki fad'amata in ni nayi miki iyaka da zuwa gaisheta" Sai abun ya bani mamaki.matar nan Kwata kwata bata kaunar ganin kwanciyar Hankalina, burinta ta samo hanyar da za'a tozartani, to da ikon Allah kanta zai koma ni dai ina Daraja ta ko ban auri Yaya Ishaq ba. kamar uwa take gareni, tunda ta rikeni bata barni na yi rayuwa a titi ba sannan duk tsananin wuya da Dadi ta killaceni acikin gida rayuwata bata shiga tsaka mai wuya kamar na sauran matan da rashin gata da mafita yasa suka fada harkan banza ba,ballatana ina auran Abunda ta Haifa har abada bazan ki Darajata ba. D'aya saura na rana yaran suka Dawo shi yaje ya Dauko su da kansa masallaci jumma'a ya tafi da mazan har da Ahmad ni da Anum mukayi tamu a gida,Shinkafa da miya Da salat nayi mana ni da Anum muka fara cin namu kafin su dawo suna Dawowa na zubo mai yaci tare da yaran,Suna ta Murnan tunda na saka musu sabbin kaya nace gidan mama zamu je. Wajen uku saura na rana muka isa gidan Mama,Mun iske gidan cike Anty Binta,da su Halisa da Anty mahma da ya'yanta kamar ana biki yaran muna zuwa suka had'u da abokan wasa suka tafi suna ta wasan su. Afalon kowacce tayi shigar alfarma har ta da Mama ko da taga jiya taga yau da na gaishesu dakyar suka amsa min gwara ma Anty mahma Halisa daman ita ta gaisheni har tana min gaisuwa,Ni da Badariya ne muke mgana kasa kasa kan gobe Badariya tace"Kin fad'a ma Yaya ishaq dai ko..? Na girgizamata kai kafin nace"Ban fada masa ba ammh zan shaida masa yau in mun koma gida" Badariya ta zaro ido kafin tace"in ya hana ki fa ?nasan Halin Yaya Ishaq barin ma in ya fad'ama Mama wlh bazaata bari ba" Kai tsaye nace"Wannan karon bazai iya hana ni din ba" Cikin mamaki take kallona bata samu zarafin mgana mukaji muryan Mama asama tana Sababi sai da na Saurara naji dani take tana cema Yaya Ishaq gatanan ka tambayeta yaushe rabon da kafarta tako gidan nan da sunan gaisheni.? Anty Binta ta karbe da cewa"Ballatana ni banza abanza mama" Shi kuma sai ya d'ago daga Danna wayarsa yana kallona Lokaci daya yana fadin"Shiyasa na kawo ta gata gani ta fad'a in ni nayi mata iyaka da gidan nan? Gata nan ni da kaina na yarje mata zuwa Gidajen ku duk sati ta gaisheku ita zaku Tuhuma me ke hanata zuwa" Mama ta tabe baki tana fadin"Rashin mutumci ne ba wani abu ba.ko yaran nan bata kawo su, nace to in kai ne ma kake so ka raba su da nan gidan basu da inda yafi gidan nan a wajen su ta bangaran ta da take takama wa take dashi ?uwar tasu da ta rage itama Allah ya karbi a binsa sai naga karyan tsiya " Idunuwana suka ciko da kwallah na kasa mgana zagi da cin mutumci ba wanda Mama batamin ba Anty Binta na tayata sai da Anty Mahma tace"Haba Mama ki barta hakanan mana ba ta baki hakuri ba" Sai Mama tayi shuru tana Numfarfashi ni dai kaina na kasa ina bata Hakuri Saboda Yaya Ishaq yace na duka na basu hakuri in ba haka ba sai ya sabamin ban ki ba na Duka gwiwa Bibbiyu na basu hakuri dakyar suka Hakura. Daganan suka yi kamar bana falon suka cigaba da Hiran su sai Badariya tajani Dakinta tana bani Hakuri na kalleta cikin wani yanayi kafin nace"Bakomai duk wanda yayi ma Aure bauta bazai taba tabewa ba..Sannan sakamakon sa na wajen Ubangiji" Daga haka muka saki mganar mu kama wacce nake ganin zata Fisheni Badariya sai jinjina yadda zan rika zuwa sau biyu arana take yi.nace mata kada ta Damu zan iya ai nace Allah adakin ta nayi la'asar sannan Mama ta aiko wai nazo nayi musu abincin dare haka na kwabe Hijabi na shiga kitchen da Badariya ta shgo zata tayani Mama na ganin haka sai ta kirkiri aikenta sai bayan mangariba ta dawo Lokacin na gama Tuwon shinkafar har na kulle a leda Miya ce bata karisa ba. Har ta Anty Binta sai da taci tayi guzuri Anty mahma dai da wuri ta koma gidanta mu kuma sai wajen goman Dare tuwon nan ko bakina ban ci ba,su Amir dai sun ci da Babansu duk na Takura na kosa na koma gida. Kusan Lokaci d'aya muka fito da Anty Binta itama zasu wuce afalon Mama ta kalleni tana fadin"Wai ni kam fa'iza ina kayan ki da Ishaq yake miki ne..?bana ganin ki da su sai tsumma kike sawa" Gabada'ya suka kalleni harda shi da Mama,Bai dai yi mgana ba sai Mama ce ta tabe baki kafin tace"Daman da Tsumman ta dace.aiko don yan'uwanta su zagesa zata rika mugun shigga alhalin daidai misali yana fita Hakkinta" Har muka isa gida mganar Mama tamin Tsaye arai bayan wannan kayan Da Anty binta ta bani ko Hijabi Ya Ishaq bai kara dinkamin ba.ammh Mama ta iya bud'e baki ta fadi yana Fita Hakkina, Lalle gaakiyan masu iya mgana da sukace wata shari'ar sai Lahira. Sai da duk nayi ma yaran shirin barcin daman ko da muka dawo su Anum duk sun fara barci,sannan na Dauki wannan Katin I.d card kenan na nufi bangaran Yaya Ishaq acikin raina ina jin cewa wannan karon bazan iya bin Umarninsa ko ya amince ko bai amince ba wannan karon ba gudu ba kuma ja da baya insha Allahu. Na shiga na iske baya falo yana cikin Bedroom dinsa ba domin ni nake bukata ba,ba yadda zai sa na bisa ciki Tuni na kiyayewa kusantar inda yaya Ishaq yake saboda Dalilai masu karfi. Bedroom din na shiga da sallama baya Dakin sai nayi mamakin to yana ina..? Har na juya zan fita naji karan Bude kofa kii..Sai na juyo muka hada ido shima kallon da yayi min nasan na mamakin ganina ne. Yana sanye da kayan barci riga da wando, masu taushi Farare na barci,Ya kariso tsakiyar dakin yana fadin"Lafiya..? Har yana wani gimtse ransa kila yayi tunanin wani abu nazo nema sai yaga na mikamai abun hannuna ya karb'a yana zama gefen gado lokaci daya yana fadin"Wannan kuma na menene.? Sai dai