Sashe 127
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shi kuma ya rike Fa'iza a hannunsa har ga Allah bai had'a auran nan da wata manufa ba. ya hada shi ne Saboda yana Tunanin Ishaq zai iya Rike Fa'iza da maraicinta har bayan Ransa bai taba sanin zai yi haka ba,In da ya sani Alhaji kabiru yana kabarinsa Allah yaji kansa bazai aura mata shi ba sannan inda yana Raye wlh shi da kansa zai raba auran nan indai ya ga Fa'iza na cutuwa" Falon sai ya yi shuru kowa na Sauke Numfashi Inno ta gyara zama tace"Duk mun ji,Daman yaran yanzu ai ka haife su ne,baka Haifi Halin su ba mu yanzu matsayin wannan auran zamu fara nema domin a shari'a ina jin Tuni auran nan ba shi" Baba Ati tace"Gaskiya shekaru bakwai ba kwana bakwai ba ne. Inno wannan Cutarwan ya yi yawa gaskiya" Abba ya yi saurin taransu da Fadin"Ban damu da wannan ba ko da aure ko ba aure sai ya sakar min y'ata tunda ba'a aure dole" Ya fad'a a kausashe Ishaq ya Dago Fuskarsa ta jike da zufa saboda Fargaba,cikin rawam murya yace"Don Allah Abba..! Hannu ya daga masa kafin yace"Ai baka sonta ko.?to ka saketa bazan yi maka Dole ka zauna da wacce baka so" Yafad'a cikin bacin rai sai kuma kowa ya kasa mgana Ammi nata jin Dadi a ranta ni Abba ya kallah ina sharan kwallah Cikin Fada yace"Ni ba sakarai ba ne ban kuma Haifi sakaran d'iya ba.Meyasa,kika zauna Tsawon wannan Lokacin da wanda baya sonki..?wanda ya zabi wata matar sama dake..? Yafad'a yana kallona Zuciyarsa har Dagawa take yi ran yan maza ya baci Tsawa ya dakamin yana Fadin"Tunda kinsan baya son ki meyasa kika yi masa afarman zama dashi..? Ina kuka jikina na rawa nace"Abba ya'yana.." Abba kamar zai Dageni ya tasomin yana Fadin"Ya'yan banza..Nace ya'yan banza kan ya'ya ne zaki zauna ya na wulakantaki Shi da yan"uwansa..?ki bar ya'yaan su mutu mana ai ba ke kika Haifesu ke kad'ai ba shima Uban su ne. Kada ki kara zama Saboda wasu ya'ya ana wulakantaki Jariri ma yazo duniya bai ga uwarsa ba. kuma ya Rayu ballatana yaran da suka girma" Yadda yake mgana yasa Inno saurin cewa"Usmanu kayi mata a Hankali" Sai a lokacin ya Saussauta mganarsa yana Fadin"Ki bude baki ki Fad'amin Tundaga farko har karshe in kika boyemin wani abu sai naci Mutumcin ki Fa'iza" Kaina naji ya sara na kasa mgana Tsawa ya sake dakamin Cikin Hargagi yace"Ki fad'amin Hujja nake nema yadda zan ci uban duk wanda ya ci zarafin y'ata wlh" Jin haka yasa da Sauri nace"Abba ba niyyata in tona masa asiri ba don Allah ka bar mganar nan" Marina ne kad'ai Abba bai yi ba,Ammh sai da na samu Tsaraban kallo kafin yace"Shi ai bai Rufa miki naki asirin ba shine ke kike neman ki Rufa masa.?Tona masa kowa yasan Abunda ke Boye" Kuka na kara Fashewa da shi har ga Allah na riga na yafe masa bana son Dawo da abun da ya wuce shima kallona yake yi alamun roko cikin lokaci daya duk ya zabge sai Zufa yake yi har Shadda jikinsa sai da ta jike da Zufa. Mama ce tayi mgana cikin Dashewar murya tana Fadin"Gwara ki Fad'a Fa'iza ki fad'a musu komai duk da nima nasan da Laifina tunda ina gani yana wasu abubuwan ban taba Hanasa ba,sai ma kokarin Dora shi kan Hanyar banza da laifina nima" Kukan da take yi baisa kowa yaji Tausayinta ba. Kamar daga sama sukaji ance"Ai bazata taba mgana ba Abba. Da zata yi mgana da ta fad'a muku ishaq ya yi ikirarin zai Daukomin yan Sanda in ya kara ganina a gidansa" Gabad'aya muka jiya bakin kofa in da muke jin mganar Yaya mariya ne ke Tsaye tana Hawaye Gabana ya fad'i shikenan Yaya mariya zata fad'i wannan sirrin da na zata ta manta da shi. Da sauri Abba yace"Taho nan Mariya ki fad'amin abunda kika sani kan zaman Fa'iza da yaron nan" Da Dauri ta kariso ta zauna agabansa kafin tace"Abba ban taba fadin ma kowa abunda ya faru ba sai yau. Saboda Fa'iza Saboda ita ammh yau bazan iya shuru ba! Ta kalleni kafin tace"Kiyi hakuri Fa'iza..'" Kafin tamaida kanta wajen Abba bayan ta gama kare ma mutanen Falon kallo ta wani sakarma Ishaq wani kallo kafin tace"Abba ban san mganar da kuke yi ba na shigo na dade Tsaye ina jin wasu mganganu. Wlh Abba Fa'iza ta sha wahalan rayuwar kaskanci da wulakanci a gidan wannan mutumin,Fa'iza bata da daraja ko Kima a wajensa da wajen uwarsa gata nan da Yayarsa Abba ni fa uwa d'aya uba Daya muke da Fa'iza ishaq ya bata Sakon ta gayamin kada na kara zuwa Gidansa da bata gayamin ba ranar da ya iskeni Abba koran kare ya yi min Fa'iza na kuka tana rokonsa ammh ya rantse in ban fita ba sai ya Had'ani da yan Sanda Abba" Gabadaya suka saka Salati Abba yace"Good..' Yaya mariya na Hawaye ta kalli Goggo tana Fadin"ai kin tuna Lokacin goggo. Lokacin da kuka barni wajen Fa'iza sanda tayi ciwon nan kikace nayi mata kwana Biyu to kwana D'aya nayi yayi min tozarcin da har na Mutu ba zan manta ba dalilin da yasa har yau ban kara taka inda Fa'iza take ba. sannan ban kuma taba gayama kowa ba,sai yau shima din naga in nayi shuru Fa'iza zata iya koma ma Wannan rayuwar data bari" Da Sauri Abba yace"Bazata koma ba. Bazata taba komawa ba indai ina Raye mari" Yafad'a idanuwansa jajir Goggo na Sharan kwallah tace"Nasan dai daga Lokacin indai zamu gidan Fa'iza sai ki zille na Dauki Saunan wani abu sai dai yadda baki ce min komai ba, Fa'iza ma ban ji tayi mgana shiyasa sai na dauka tsiyar ki ne ya tashi kika dauke kafa." Baba Ati tace"Ko ba domin Darajan Fa'iza ba,ai ya Duba zumunci" Yaya Mariya tayi mirmishi kafin tace"Ke kika san wannan Baba Ati, tunda Fa'iza ta zama banza a wajen su zaki san ba su damu da wannan zumuncin ba" Kai Tsaye Abba yace"Ki fara sanar dani abunda kika sani" Ina kuka ina girgizama Yaya Mariya kai bata Saurareni ba ta fara zayyana ma Abba abubuwan data sani akan zamana agidan Ishaq da yadda ya rabani da su da auran sa da wulakanci da Anty Binta tayi mana. da yadda na kara zama banza bayan auransa da Zainab Saboda ita mai kyau ce kuma yar gata ce,da yadda har mahaifiyarmu ta rasu bamu gana ba,kunci rayuwar da na cigaba da Fuakata kafin samun sana'ata da duk irin cin kashin da Mama da Anty Binta suke min ta fadi iya abunda ta sani kafin ta gama gabadaya su Inno sun fara kuka saboda Tausayina. Ammi tace"innalillahi lalle Fa'iza ta ga Kunci rayuwa" Abba ko Ishaq da Mama yake kallo ji yake kamar ya saka a kulle masa su har sai sun daina Numfashi,shuru falon ya Dauka sai mganganun su Baba Ati cikin Tausayawa ni ko kuka kawai nake yi cikin kunar rai abubuwan da suka faru suna Dawo min Daki Daki. A fusace Abba ya mike yana fadin"Ba anfanin wannan zaman. Ka rubuta ma y'ata takardan saki tunda ba'a Dole. kuma kwatankwancin yadda ka Wulakantamin Fa'iza wlh nima sai na wulakantaka" Kokarin Fito da wayarsa yake yi ganin haka nayi wuf na rike kafafun Abba ina kuka nace"Abba kada kayi mai komai don Allah nice daman baya so to ya sakar maka y'a Abba da gaskiyansa ni Nakashashiya ce ina da Raunin ji,sannan ni ba Fara bace bani da kyau Abba sannan ni bani da ilimin Boko kuma ban iya Turanci ba,sannan ni bani da gata bani da kowa ni ba yar kowa bace sai Diyar Bebiya,Abba da gaske ne ni nayi kutse cikin mafarkin sa ni ban Dace da Mutum irin sa ba,Abba ka Dubeni baka mara kyan Fuska wacce batajin Turanci bata kuma da gata Abba dole yaji kunyar nuna ma Duniya ni a matasayin matarsa in kuma yaji kunyar nuna ya'yansa shima bai yi Laifi ba ,Abba bai so a haife su ba Karfin Rabo ne ya samar da su na fi shi sanin zafinsu shiyasa na zauna Domin na kare su Abba. Abba ka kyalesa yana da gaskiyansa ni Fa'iza bani da wani amfani Abba ni ba macen data dace da namiji kamar Ishaq ba ne,ba ya so na ne Abba Kuma gaskiyan Mama data sha Fad'in bauta ya Dace da Mata irina. Abba na zauna na wahala da ya'yana Tunda ya zabi wata matar sama dani Abba sai mu kwana mu yini ni da yara bamu ci abinci ba Abba,Abba ba tun yau ba Mama da tab'a so ta koreni Anty Binta ta taba zuwa har gidana ta min watsi da kayana akan sai na bar gidan kaninta Abba..! Sai kuka yaci karfina na rika rusa kuka sai jikin kowa ya karayin sanyi Abba ya Duka ya rikeni jin hannayensa yasa na cigaba da Basu labarin irin zaman da nayi da ishaq irin yadda na fuskanci tozarci da wulakanci a wajensa da wajen mama yadda suke zuwa da Zainab ina musu wahala kamar jaka yadda yake tafiyar ya barmu da yunwa ni da ya'yansa,Yadda mahaifin matarsa da shi kanshi suka taru suka wulakantani Saboda bani da gata ni kaina ban san ina mgana ba Idanuwana a Runtse nake maida musu komai ina ganin shi a idona yana wucewa kamar a majigi. Ina basu labarin taimakon Hajiyar su Raliya gareni tare da taimakon Badariya da kudin da Kungiyarsu tabani kafin fara koyan san'ata da yadda muka yi da ishaq da zaman mu da shi bayan haka. Na Damke hannunwan Abba ina Fadin"Bani da abunda zai so Abba. Shiyasa na yi zaman ya'yana Lokacin da na yanke shawaran barinsa sai ya rasa aikinsa sai na janye kudirina Abba har zuwa wannan Lokacin" Kuka yaci karfina ammh ban yi shuru ba na cigaba da gaya musu yadda muka fara Sabuwar Rayuwa da duk abubuwan da suka Faru da Lokacin da ya nemi na bama aurammu wata Dama. Da sauri Abba yace"Allah yasa baki bashi wannn damar ba Fa'iza..? Ina kuka nace"Na kasa Abba..Na kasa dalilin Ishaq yasa na Tsani aure da maza Gabadaya auren ya fita a raina. Don girma Allah Abba ka saka shi ya Sakeni ina jin kamar zam mutu in na