Sashe 93
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gudirina" Da Sauri yace"To bazan takura miki ba" Yafad'a harda daga hannu,Hawayena na Share ina kara rike zanin gadon hannuna kada ya subucemin,a marairaice ya kalleni kafin yace"Fa'iza ki yi ma girman Allah ki barni na rumgumeki ko na samu saukin abunda nake ji" Ido na sakarmai cikin mamakin kalamansa kafin na daure fuska nace"Sai yau ne ka fara shiga wani Halin Saboda ni ko yanzu ka fara di'n..? Ban basa damar mgana ba nacigaba da fadin"kuma kada ka fara karya alkawarin ka,nima zan karya nawa" Da Sauri ya matsa baya yana fadin"Na bari.Wlh na bari bazan kara tab'aki ba,sai kin ce na tabakin" Sai ya kusa bani Dariya sai da na murmusa,kokarin mikewa nake yi ya mike zai riko zanin gadon na balla masa Harara da Sauri ya juya yana Raruman kayana ya mikomin yana fadin"Dama..dama kayan ki zan d'auko miki" Ban yi musu ba nasaka hannu na karba,da sauri ya bani Hanya yana fadin"Ranki ya dad'e ki huce lafiya". Ban tankasa ba na fara tafiya ina Tattare zanin gado yabi ni da kallo har na fice ya koma ya zauna saman katifar yaraf kamar an sauke kayan wanki kansa ya dafe yana fadin"Allah na tuba..Allah ka yafemin..Ya Allah ka lallashi zuciyar Fa'iza ta sake bama auran mu wata damar" Ban kara ganinsa ba,tunda na koma dakina naci kukana sai da na koshi sannan naje nayi wankar Tsarki na Tsabtace jikina, ranar ko Kunin aya ban yi ba zobo kawai na Dafa,Shima Daki ya yini sallah kawai ke fitar dashi ,sai da Hafsah ta dawo ta kai nikan kunin ayan,abinci kad'ai nayi mana sai gyaran gida,ko da Daddare kwanciyata nayi a daki ban fito karatun dare ba, Anum tazo na korata bace bani da lafiya ba jimawa sai ga shi ya shigo har gadon ya zauna yana Taba goshina da Sauri na jaye kaina ina bata rai da wata murya yace"To taba goshi ma sai ya zama laifi..? Saurin matsawa nayi ina fadin"Ai a shari'a ma yanzu kai ba mijina ba ne,in nace bazan zauna dakai ba,ba wanda zai matsamin na zauna dakai" Ina gani jikinsa yayi sanyi cikin wani yanayi yace"Fa'iza wata shari'ar ce ta ce haka..? Kai tsaye nace"Baka sani ba..?ai musulunci yace Haramun ne ka yi wata Hudu baka kusanci matarka ba. Sannan jinginan aure a musulunci kamar sakin aure ne" Kafin na karisa yayi saurin tareni da fad'in"Ba saki ba ne Fa'iza wlh ban sake ki ba. kuma har abada kinsan auran mu ba saki in sha Allahu" Ina jinsa ban tankasa ba na koma na kwanta shi kuma sai ya mike yana fadin"Da alamu dai lafiyan ki lau yau laifina ya shafi ya'yan Umma kenan..?. Baya na juyamai ban kara masa mgana ba ina jinsa har yana gyaramin bargo ya fice yana fadin"a huta lafiya Fa'in Ishaq" Tun daga ranar bai kara matsamin ba da ya fara na d'ago na ballamai harara sai ya koma gefe yace"Yi hakuri". Ko Allah ya baki hakuri,Daganan sai na samu lafiyansa,ko bakomai na daina fargaban zai ritsani ko zai mamayeni irin na ranar,ammh duk da haka ina taka tsantsan da shi Saboda naga da gasken yake yayi nadama,kuma na karb'i nadamarsa ammh ba domin zan iya karban bukatansa na sake basa wata damar ba. Mama ta dawo bayan tayi kwarari wajen wata biyar a yamai, yan'uwan ma sun so tayi zamanta achan ne Mama taki sana'o'i suka dinga yi a chan ita da Anty Hure kuma sun had'a mata yan kudade kafin ta dawo da su aka samu aka biya kudin makarantan yara,aka siyan kayan abinci tunda yan kudad'en hannuna mun cinyesu wajen siyan abinci sannan ya turama Jamal shima wani abun,Ga Badariya itama suna shirin zuwa bautar kasa ne ita laluranta kad'an ne babban abu shine kud'in haya da kud'in makarantar Jamal tunda shi ajin karshe zai shiga ya maimaita aji hud'u,yana karatun Software enginearing ne. Kudin Hayan nan da shi nake kwana araina,kud'i ba yan kad'an ba wajen dubu Dari hudu ne wannan gidan,Shi kan shi ya damu tunda mai gidan ya fara mganar kudinsa tun watan daya gabata sai ya bashi hakuri yace ya karamai Lokacin,mai gidan daman ba shi da kansa ba ne,Komai na Hannun babban d'ansa ne,kuma ba wani kirki da ya cika ba,Don ma yana ganin mutumcin Yaya Ishaq da Tuni ya fara yi mana sallama. Zagayowar wannan shekaran sai dai Godiyar Allah jamal ma gida ya Dawo,Anty Binta kuma da an yi mgana sai tace tana da biki a gabanta,bata da kudi shi bai ma nemanta,Mama ce ta kan kirata a waya tana fad'a mata sai ta fara korafin itama akwai hidima agabanta,Abuja ma yanzu sai yafi wata bai je ba,Ita Zainab din ne ma,takan turo masa kudin ya tafi yayi sati ko kwana goma ya dawo nima ta kan kirani lokaci bayan Lokaci mu gaisa auran nasu har mamaki yake bani kamar Dole,to ita tana son mijinta kuma mahaifinta yasan haka, shiyasa bazai yarda auran ya lalace ba shima Ai yana son matarsa da baya sonta da Tuni ysan mafitarsa. Tun mai gidan nan na d'aga mana kafa,har yazo ya daina Sauraran ban hakurin Ishaq ranar da Safe yayi mana Dirar makiya Allah yasa yara suna makaranta da abun bai yi dad'i ba,Da kakkausan murya ya ce mana ya bamu nan da sati daya in bamu biya ko rabi ba sai dai mu bar gidan. Hankalin mu ya tashi bamu ijiye ba,ba kuma mu ba wani ajiya ba. Yaya ishaq ko barcin kirki ba yayi duk ya bushe a tsaye gashi yana ganin Jamal a gida shima ba kudin abinci da pocket money ballatana ya koma makaranta har shi da kansa yayi ma Anty Binta mgana tace bata da kudi ta shiga adashe ne,ni kuma jarin hannuna duk yayi kasa sai na Bukatun cikin gida. Mama ma duk hankalinta ya tashi,Mama a baya datake yar gayu yanzu wahala duk yasa ta tsufa kamar ba ita ba,Sai dai ya shiga D'aki yana Tufka yana warwara ba mafita Hafsah mganar kudin makarantar Jamal ta sani shi kadai takai labarin Karofi wajen Goggo,sai ga shi ta kira Jamal yaje wajenta ita da ya'yanta sun had'amai dubu sittin tace ya biya kudin makaranta,bayan ta hadamai kayan abinci,haka yazo mana da kayan arziki Mama sai kunya ya kamata har da kuka sai gashi ta Biyoni har daki tana cemin"Fa'iza ke kika yi ma Goggon taku mganar jamal hala..? Ina zaune nace"Aa Mama inajin Hafsah ne da taje wannan satin" Sai mama ta kasa mgana ta fita ta koma Dakinta abun mamaki sai ga Mama da shiryawa ta tafi karofi yima Goggo Godiya sai da ta kwana Biyu ta Dawo tana fad'in irin alherin Goggo da ya'yanta a raina nace da ba Hajiyar Dala ce kad'ai yar'uwar mijin ki ba,ashe kin san da Goggon,Hajiyar Dala da take ganin tana tare da ita ko jinta ma ba'a yi. Yanzu naga Mama ta daina Takura min,ba kamar baya ba. Kuma bata shiga harkata, naga ma alamun Ta koma wata shuru shuru a d'aki kamar bata nan,Aranar da satin d'ayan da mai gidan ya bamu,zai cika kasa barci muka yi,a daran ranar har ce ma Yaya Ishaq nayi"Me zai hana ka yi ma zainab mgana ko akwai taimakon da zatayi maka ta bangaran su..? Kai Tsaye yace"Aa bazan roki kowa ba Fa'iza ai susan ina bukata kuma basu Dauko sun bani ba. In sun bani zan karba in basu bani ba, bazan taba rokan su ba" Sai ya bani Tsausayi daganan ban kara masa mgana ba, sanin da nayi tunda yace bazai yi mgana to bazai yin ba,Da Sassafe bayan ya raka su Amir makaranta gidan Anty Binta ya tafi,yana chan bai dawo ba sai ga yaron megidan da wasu matasa majiya karfi har gidan suka shigo Hafsa na makaranta Badariya ke gida tunda sunanta bai fito a bath A ba. Tijara ya fara yima sannan yace watsi zai saka ayi mana da kaya,Mama ta fito nima na fito ni ke basa Hakuri Mama ko cikin gadara tace"Ka dad'e baka sa an yi mana watsi da kaya ba, ban da yanayin rayuwa kai har ka isa ka wulakantamu. shekaran da ta wuce kai baka isa kazo kana mana barzanar banza ba,rayuwa ce ta maida mu haka" Ta fad'a cikin baci rai,ido cikin ido ya kalleta kafin yace"Tsohuwa ina daraja Furfuranki ammh ke baki gani ba ko..? Kai Tsaye Mama tace"in kana Daraja Tsufana ai da baka tsaya ina fad'a kana fad'a ba" Kai tsaye yace"Gidan nan ai ba na tsoho ba ne ko?to in dai bana Tsoho ba ne sai kin fita daga gidan nan,yau na zata abun naku na mutumci ne. kuma Darajan d'anki kikaci wlh da yau sai kin raina kanki ina ruwana da rayuwarki a baya wama ya sani ko a lokacin baya d'in da kike da arzikin ba alheri kika shuka ba tsiya ce shiyasa kika ga karshen ki? Ai sai Mama ta saka kuka tana fadi'n yayi mata rashin kunya na riketa ina fadin"Haba Mama ba girman ki ba ne ki Tsaya kina tanka tanka da shi" Sai mama ta kasa mgana nan na saka Badariya ta shiga da ita ciki D'aki sai kuka take yi. Wani Lokacin masu gidajen haya kalilan ke da burb'ishin mutumci saboda nasan bamu da gaskiya Kuma a maganar Gaskiya Mama ta zak'e da yawa ne shiyasa. Hakuri na rika basa ina fadin"Kayi hakuri don Allah ,ya fita ne ya dawo yanzu zai shigo" Kai tsaye ya kalleni ba wani babba ba ne, bazai wuce sa'an Yaya Ishaq d'in ba kawai dai irin ya'yan masu kudi'n nan ne, kallo na yayi yana fadin"wanchan tsohuwar ai ta bata komai Hajiya.Kai ashiru ku shiga ku fara fito musu da kayan su waje" Sai na durkushe a gabansa na had'a hannayena ina fadin"Kayi wa girman Allah kayi hakuri.In kayi mana watsi da kaya ka tona mana asiri ina zamu..?ka da ka manta mu musulmai ne kuma duk inda musulmi yake dan'uwan musulmi ne,In ka rufamana asiri ka suturtamu sai kai ma Allah ya Suturtata taka ranar gobe kiyama. kayi hakuri don Allah zamu biya ku kudi'n ku da zarar mun samu" Na fad'a cikin magiya sai kawai ya Tsaya yana kallona cikin Tausayi kafin ya ce na mike sai na mike ammh ban sauke hannayena ba cikin Tattausan murya yace"bakomai naji rokon