Sashe 47
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tafiya muka tashi. kowa kagani da Kuzarinsa ban da ni,kwata kwata kamar an zaremin lakkan jikina,Goggo sai fad'a take min wai na kwazzabi kaina bana cin abinci Yaya mariya na wajen tace"Kuma zama da yunwa bazai taba Sauya komai ba..Tamadina ta rasu sai dai mu yi fatan Allah yasa tana kyakyawan karshe" Sai hawaye ya kecemin suka shiga tsere bisa kumatuna, bayan mutuwar da ta dake ni,yayi sanadiyar tasomin da ciwona da daman kamar jira yake na shiga hali makamancin sa,Mun had'a duka kayanmu na yara Hafsatu ta wanke musu ta had'a musu ta musu wanka,ta shiryasu haka ma su Yaya mariya sai kuma sabon kuka ya tashi muka zauna mu hud'u muka ci kukan mu muka koshi,muka share Hawayen mu. Goggo tagaji da bamu baki ta Hakura ta koma gefe ta zuba mana ido bayan ta kira Yaya Isa tace yazo ya Dauketa ita da Hafsatu da mariya da Baba Ati, Yaya Asiya kano zata wuce nima kuma gidana zan koma. Da azahar sai ga Hajiyar Dala,mun dauka ma bazata zo ba ne ahalin taji Rasuwar. tunda Goggo da kanta ta kira wayar ta,ta fad'a mata,Tazo tayi mana gaisuwa ta bama Yaya Asiya dubu goma Sadaka batayi awa d'aya ba,Ta ce zata tafi, nan take zencen zata karisa katsina Tare da Direba take jin Haka yasa Goggo ta kalleni tana fadin"Fa'iza tunda kun gama shiri,sai ki bi goggon taki tunda katsinar zata shiga" Da Sauri tace"Aa ba gidan Saudatu zani fa gidan Wani abokin Major ne. mahaifiyarsa ta rasu zan biya nayi musu gaisuwa suma na wuce" Ina jin haka nima murya a sanyaye nace"Ki bari kawai Goggo zan tafi da kaina" Sai goggo ta jinjina kai kafin tace"Shikenan" Daga haka tayi mana Sallama tatafi Goggo ce ta rakata har Dakunan matan gidan tayi musu gaisuwa, kafin Tafiyarta sai da ta dawo sannan Yaya Asiya ta bata kudin da Hajiyar Dala ta bata Goggo ta karb'a tana fadin"Kudin ku ne ai Asiya ba ni aka bawa ba" Yaya Asiya tace"Goggo mu bama bukata ayi sadaka Allah ya kai Haske kabarin mahaifiyarmu" Goggo ta amsa da Ameen itama fita tayi da kudin Dakin Maman isuhu ta shiga ta bata kudin Dakyar ta karba, Goggo tace kun yi wahala damu wajen kwana takwas ku karba ku kara Allah ya Rufa asiri .sannan ta karb'a tana sharan kwallah da kara fadin Allah ya jikan Tamadina. Yaya Isa ya kira yace gashi nan zuwa,Shinkafa suka dafa mutam gidan suka zubo mana yaran aka zuba mawa suna ci ni dai bakina yayi nauyin bana jin Dad'in komai kaina wani Dum dum kawai yake yi duniyar ma ba daidai nake jinta ba. Kwatsam sai gasu Sa'adatu da Habiba sun zo min gaisuwa nayi mamakin zuwan su sai da aka gama gaisawa sannan na kalle su ina fadin"A ina kukaji rasuwar sannan waya kwatanta muku gidan nan..? Sa'adatu tace"Ai tun da naga an kwana biyu baki dawo ba nace ba Lafiya Megidan ma nata jimamin abun. yace haka kurum bazaki je ki zauna ba ko don makaranta yara da muka ga an yi kwana biyu sai yace bari yaje gidan kakaninsu su Amir yaji ko Lafiya. to chan yaji abunda ya faru wajen kanwar Baban su Amir ce domin ina ganinta tana zuwa itace ta fad'amai mahaifiyarki ta rasu sai ya Nemi ta kwantatamai gidan nan sai ta mai kwantance mun d'an sha wuya kafin mu gane,sai dai kinsan gidan mutuwa baya boyuwa balle da naga ba'a gane ba sai na rika kwantance da cewa Bebiya bata mgana sai ko gashi an kawo mu" Na jinjina kaina,kwallah na Taruwa acikin idona makota na ne da ban had'a komai da su ba,Ammh sun nemi inda nake sun zo min gaisuwa Su mama kuwa tun ranar uku basu dawo ba,bana saka ma Yaya Ishaq a lissafi bai Dauke ni da Daraja ba,ballataana ya Dauki dangina da iyayena abun Daraja Har afili na nuna musu jin Dadi'na na nuna su ga sauran yan'uwana da Goggo suka dinga saka albarka har da gurasa Habiba tazo da shi ita kuma Sa'adatu sai ta Dafo Dambun Shinkafa da yaji Zogale Goggo ta karba ta kai ma Mutun gidan suna fad'in Allah ya bada Lada A nan suka yi sallar La'asar sannan suka yi shirin tafiya sai nace su jirani mu wuce tare Lokacin Yaya Isa ya iso ya tafi masallaci ne,na mike na shiga uwar Dakin Tamadina na Dauko jakar kayan mu da Hijabina.da Yaya Asiya ta wankemim Goggo ta matsamin nayi wanka da Safe na fito falo na ce Hafsatu tazo ta sakamin Ahmad a bayana na goyasa ta sakamin shi har na saka zani na goyasa irin na D'ago kaina sai Duhu ya mamaye ganina na fara Laluban bangon gabana na rasa sai nayi luu ta baya zan fad'i sai naji an tareni ana salati kuma hannuwana ne da yawa suka rikeni,Sama sama nake jinsu jiri ya rikeni da kaina da ya dauki wani irin azaban ciwo,Kamani sukayi na zauna Yaya mariya ta kwanto goyon Bayana Goggo fad'i take"Daman ni nasan yarinyar nan bata da lafiya, shigen zurfin cikinta yasa taki mgana" Asiya kira min Isa yayi maza yazo in asibiti zai kaita ya kaita kada ta yi ma kanta Lahani bamu sani ba" Ina nan zaune Dafe da kaina ina jin Sannu sannu na tashi Daga bangarori Dadama, chan jimawa na zame na kwanta naji shigowar Yaya Isa da Bayanin da Goggo take yi masa,sai yace a kamo ni muje asibiti a dubani. Yaya mariya ta kamani muka fita mutan gidan na tambayan lafiya tace jiri ne ya kwasheni Maman isuhu tace"Daman daga ganinta bata cika lafiya ba itama" Ni dai ina jinsu har muka fice muka shiga mota wani asibitin kud'i acikin gari ya kaimu shi ya shiga ya fita muka ga likita akan Lokaci gwajin Farko sai ga jini na ya yi sama Dari Biyu da Doriya sai ucler likitan nata fada ina so na kashe kaina da na fadi zan iya kamuwa da Ciwon barin jiki, ko jini ya haye yayi sama na mutu mgunguna ya bani bayan yayi min alluran jijiya ta ucler sannan yace na rika cin abinci sosai saboda kiyaye lafiyata. Muna hanyar Dawowa Yaya Isa sai fad'a yake yi,Yaya mariya bata mgana sai dai kawai ta sauke numfashi tace"Uhm" abun yafi karfin ta wannan karon ko da muka koma makotana sun tafi sun so su jira dawowarmu Goggo tace su tafi Saboda Dare sannan sun bar iyalansu agida to sanadin haka komawa Katsina bata yuyu ba da Goggo ta kawo mganar Yaya isa ya maidani sai yace"Haba Goggo kalli Halin da take ciki fa..?,jininta yafi dari biyu a yadda take nan ko kanta bazata iya mora ba ballatana ga yara tare da ita,kawai mu wuce da ita gida in taji sauki sai ta koma" Sai Goggo ta kasa musamai saboda taga Halin da nake ciki,Ni a motar Yaya isa muka tafi ni da Goggo da Baba Ati da yara su Yaya mariya da yaya Asiya da itama tafiya kano tasha ruwa suka hau ta haya mun yi sallama da mutanen gida muka rabu suna Hawaye muma muna yi. Sai dare muka isa karofi ni dai abinci suka matsamin naci, nasha mgani na kwanta barci. Salolli na ma sai da asuba na rama su na ji saukin Jirin sai dai ciwon kan ne,Washegari Yaya Asiya ta koma kano Yaya mariya daman muna isowa ta wuce gidanta Wasa wasa jikina ya ki dad'i har sai da na kara Sati a karofi Goggo na kula da ni,tare da su Amir kamar kada na koma inda na fito sai dai ba Dama ranar da nake da kwana bakwai a karofi Goggo ta saka Yaya isa ya maidani da Yammah bayan taga naji sauki,Tare da sha tara na arziki komai ta had'amin su garin kunu,garin Danwake,Wake,Tsaki,rama bushasshiya da Zogale sai Taliya yar Hausa da yara suke so sai ta saka aka Murzamin ta samin a kwali saboda kada ta karye hatta kayan maggi sai ta siyamin,da kayan miya mai yawa sannan ta saka Yaya isa ya kaini har gida ni da yara ina ta masa godiya shima da ya saukeni ya bani dubi biyar yace na rike sannan ya Jadaddamin naa kula da lafiyata na amsa mai da in sha Allahu. Gyaran gidan na fara ko'ina duk yayi kura,Amir na tayani da kwashe kaya su Anum kuma sai dai su kara batawa,Adaran Taliya yar murji na Dafa mana na manja mai ruwa ruwa muka ci tare a faranti daya muma Santi muna gamawa bayan mun yi sallah na saka suka kwaso littafan makarantansu nace su duba tunda gobe zasu koma makaranta. Wasahegari Laraba da wuri na shiryasu na kuma fita da su da kaina,Haruna da Sa'adatu da na leka gidan suka karamin gaisuwa da tambayan ya karfin jikina..?nace naji sauki sai hamdalar ubangiji. Makota na dake kusa dani wad'anda ban taba ma shiga gidajen su ba sun shigo sun min gaisuwa daga suce Sa'adatu ta fad'a musu ko Habiba naji Dadi Sosai domin ba karamin masoyin ka ba ne zakayi rashin uwa yazo yace maka Allah ya kara hakuri kuma bazaka manta da wannan mutumin ba, wanda kuma bai ce maka Allah ya kara Hakuri ba,shima girman abunda ya aikata yana nan acikin ranka bazaka taba mantawa dashi ba. Na dawo da kwana Biyu Anty Mamah tazo min gaisuwa tace ta zo sau biyu bana nan,nace mata eh nayi rashin lafiya ne tayi min gaisuwa ta kuma bani Hakurin sun yi tafiya ne chan dangin megidanta Kumo dake jahar Gombe ta jima muna ta Hira sai la'asar tatafi bayan nayi mana Danwake da manja da yaji taci ta koshi,sannan mukayi sallama washegari kuma daga makaranta Sai ga Badariya tazo min gaisuwa itama da ban hakura Mama bata nan bikin D'iyar Hajiya Barira k'awarta tatafi wajen satin ta daya Abuja aka kai Amarya, dagachan ta biya gidan su Zainab ta kwana biyu. Sai kawai na samu kaina da cema Badariya"Sun dawo ne..?ya mai jiki..? Badariya tace"Basu dawo ba suna chan jikin Farhan da sauki sun dai Tsaya Hutawar su kawai" A fili nace"Allah ya dawo da su lafiya" Daganan ban kara tofawa ba,Bata jima ba ta tafi tace saboda Mama yanzu in taga ta Dad'e sai ta fara fada, nace gaskiya kam ya kamata ta tafin kada dare