Sashe 165
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
washegari suka koma kaduna. Bayan Ammi na kira su Badariya,Anty Fadila da tace min jiya suka dawo Lagos ga Anum ma bata riga ta koma ba har ta bani muka yi mgana. Dukkansu ba wanda ban kira nayi musu bangajiya ba. Nana fatima sai shakiyanci take min,wai ina cin amarci na kashe waya. Na kira Abba mun gaisa yanata tambayana ya bakon waje..? Nace lafiya lau,Tunda dai ba fita nake yi ba ina gida Engr yace duk makotan mu yare ne da wad'anda ba musulmai ba,Har Goggo na kira mun gaisa da Sauran yan'uwa kowa mukayi mgana sai yace na dace sai fatan zaman Hakuri da juna. Engr bai koma aiki ba yace sai ya yi sati zai koma,ranar da muka kwana Biyar nace ya bar siyan abinci yayo cefane zan rika Dafawa sai da ya kalleni yace"Kin tabbata..?bana so ki na wahala fa" Kai tsaye nace"Hakki na ne fa na girka na baka ko wanda kaga ina barin ka kana siya na bakunta ne,ni dai kayo cefane zan fara girki" To kasuwan ma tare muka je muka siyo komai na cefane da kayan abinci naga garin Edo cike da yaruka kala kala da mabambantan al'ummah. Da muka dawo tare muka shirya kitchen din nayi nayi ya tafi yaje ya Huta sai ya noke kafada har ce min ya yi "Kin manta nace miki sunana makale mata manne mata" Ai ko naga makale mata girkin ma da nayi na Doya da miyar kwai tare muka yi yana mikomin abubuwa sannan yana tayani Hirarrakinsa masu dadi da ban Dariya. Da na gama girkin nace masa megadi da Direba kai tsaye yace"Ni kad'ai ne Dolen ki Faa'iza su ko ba Dolen ki ba ne ki kyalesu ina basu kudin abinci" Tunda ya nuna haka sai ban ja ba,aammh nace masa in ya ragu gudun kada ya lalace zan rika basu sai yace shikenan in ba Takura. Tundaga ranar na nake yi mana abincin yaci kuma yana Santi yana sakamin albarka wani lokacin har hawaye nake Daukewa a boye ashe ashe nima zanga wannan ranar..?. Ranar da zakayi ma miji abun alheri yaci da godiya yana saka maka albarka. Cakarewa ta nake yi a gida ina cin gayuna ban cika dai kwalliya ba tunda ban saba ba,ammh ina saka kaya masu kyau ina gyara kaina. Tunda Engr yana yabamin ko wani irin shiga nayi ko na burgeshi ko ban burgeshi ba,sai yace"Tife na kin yi kyau" Wannan yabawar tasa ke karamin kaimi ina jin wani karsashi a kasan raina. kuma Engr bai taba min korafin rashin kwalliyata ta yan matan zamani ba,zai gani kuma zai yabamin shiyasa ban ma san Lokacin da nake cin masa gayun ba saboda bakinsa da idanuwansa suna nuna Darajata sannan suna yabamin shiyasa nima nake yin wasu abubuwan ban sani ba. Zuciya tana son mai sonta sannan tana Daraja mai yaba mata. Ranar da muka cika sati na kira Maa muka gaisa na tambayi Kafaya tace suna makaranta tunda University of Abuja suke yi,bayan mun gaisa sai tace"Kuna nan dai lafiya dai ko..? Ba wata matsala shi Babatunden d'in bai yi miki komai ba ko..? Sai nace mata lafiya lau muke haka fa da mukayi waya da Paapa shima haka yace min ko oluwatosin din na bani matsala nace musu komai lafiya muka rabu suna sakamin albarka. Yafara zuwa aiki ranar yana ta kirana ina waya sai da na gama na kirasa da ya tambayeni da wa nake waya nace ma su Paapa ne. Kai tsaye yace"Uhm lalle kin kwace gwammati na. Nifa basu kirani ba yau kwata kwata." Ya fad'a kamar zai yi kuka. Ina Dariya nace"ko kana kishi dani ne..? Da sauri yace"Name..?zan famshe a wajenki ni dai in dai zaki gatan tani ai shikenan''Dariya nayi masa ban ce komai ba sai da ya dawo muna cin abinci ya kalleni kafin yace"Wai Hajiya baki gama Hutun naki ba ne..? Ban gane mganarsa ba nace"Hutun me..? Sai da ya kashemin ido kafin yace"To ina so na fara kara'i na da shagali mana" Kunya ta kamani na sunkuyar da kaina ina hararansa shi ko sai ya saka Dariya kafin yace"Ji min yarinya daga na Daga miki kafa sai ki saki jiki..? Tab shagali zai fara soon" Na lura daman ya riga ya gama Dagamin kafa,tunda naji abunda ya fada nima sai na shirya duk da ina jin Fargaba da faduwar gaba. Bayan mun idar da sallar isha'i tunda in dai yana gida shi yake jan mu jam"i ya fita ya dawo da leda a hannunsa ashe Zabbi ne gassasu da Yan shilla,sai madaran youghourt mai kauri da sanyi,ya sani na kara Dauro alwala muka yi sallah raka'a hudu tare addu'o'i sannan ya jani kan cinyarsa ya ciyar dani zabbin nan tare madara duk da ina kaucewa ammh bai damu ba. Bayan mun gama shi ya kwashe komai ya kai kitchen ni kuma sai na shiga wanka,shima dayan bedroom din ya shiga domin ya kimtsa kansa. Rigar barcin da Zainab ta aikomin da shi na saka rudewa iya rudewa Engr ya yi ya kamkameni yana shinshinar kamshin Turarena lokaci daya yana Fadin"Ke ma kin amimce in fara shagalina Tife na" Kasa amsa masa nayi ina sunne kaina a kirjinsa tun ina ganin al'amarin kamar wasa kamar yadda ni na saba jinsa,sai dai ina lamarin ya sha bambam wanda na sani dabam ne da wanda Engr ya jani zai sanar dani. kusan shidewa nayi lokacin da naji yana kaima kowacce gaba dake jikina Sumbata kafin na dawo hayyacina yabi duk inda ya sumbata yana Tsotsa abunda ya kara rikitani har Tafin kafana sai da Engr ya lashe. Ya bi dani ta wata hanya ce siririya mai wuyar isa ammh fa babu gargada ballatana kwalabai . Kwalbati ne a shimfid'e cikin natsuwa da kwanciyar hankali ya kaini bakin Bodar inda labarin ya sha bambam. In nace ban ji tarin bambamce ba nayi karya,na saba jin shigar abun kamar agaggauce,ammh wannan karon a sannu sannu ne cikin Fitar hayyacin sambatun kalamai masu dadi da sanyaya zuciya,naji ni na kame tunda Ammi batayi min wasa ba Shiyasa Engr ya Rude nima ya Rudar dani da Farko naji Zafi gaskiya Daga baya kuma sai ya yi sauki zafin ammh mganar gaskiya Engr ya famshe Bashinsa na tsawon sati Dayan da yayi yana min hidima. Ya fita hayyacinsa sai sambatu yake yi yana faman kirana da sunaye mabambamta,har da yarensu ya juya yana ta yi bana Fahimta. Ni dai na mika masa Jikina da zuciyata gabadaya kamar yadda nima ya bani komai nasa,dakyar ya iya kyaleni bayan ya samu natsuwa ya wani Saukemin nauyin shi a kan jikina Lokaci daya yana sakin Numfarfashi a jere kamar wanda yayi gudun Tsere sai kuma chan naji kamar baya numfashi jikinsa ya saki na rude ga shi ya yi min nauyi a jikina haka na rika Shafa Fuskarsa ina fadin"Tosi...Tosin..Engr.." "Engr..engr.." Gabana ya yanke ya fadi ras,gabadaya sai naji na rude da nayi wani tunani ko dai ya rasu ne Fa'iza..? Ganin yadda na rude ne yasa ya yunkura daga kan jikina ya mulmula gefe chan sannan ya rikoni,ya dawo dani samansa ya kamkameni yana ji yadda na sauke ajiyar zuciya na salamu jin ashe yana lafiya. Yana kamkame dani,ya na sauke numfashi,cikin wata irin murya a shake yace"Ban mutu ba. Tife na ban mutu ba kawai dad'i ne ya yi min yawa" Yana fad'a yana tusa kansa a tsakanin wuyana kamar zai yi kuka ya cigaba da fadin"Anya ke ce kika haifi Amir da Anum..? Ina Danne dariyata nace"Harda Mutsy da Ahmad ma ka manta" Girgiza kai yayi lokaci daya yana Fadin"Anya daga nan suka fito..? Yafada yana kai hannunsa wajen na Turesa ina yar Dariya wata rumgumar ya karamai kafin yace"Allah ya yi miki albarka. Allah ya yi miki albarka Nagode sosai Tanque Very Musch Faa'izaa Tife na" Albarka bansan adadin da na sha ba har muka je muka yi wanka muka Tsarkake jikin mu.. Muka koma muka kwanta mun Dade bamu yi barci muna ta Hira har mamakin kaina nake yi ni ce kan gado daya da wani namijim..?har muna Hira cikin so da kauna haka..?. Allah ne abun godiya domin shi yake baka abunda baka taba tunanin zaka samu ba". Da asuba ma muna idar da sallah daga gaisuwan Safe ya nane min har da shagwaba yana fadin"Kinga dai jiya na fara ko..? Dariya kawai nayi na biye masa ya yi kara'insa nan ma fad'i yake"Ni dai ina tamtama anya su Amir ya'yan ki ne..? ko dai ya'yan Yaya Asiya ne?saboda naji wajen gam. Tsam da shi wlh kamar ni na fara shiga" Filo na dauka ina makamai Lokaci daya ina fadin"To kuma wayace ka fada..?ba sai ka yi shuru ba" Filon ya rike yana fadin"To kuma bakin Tosin ke rufuwa.?ni fa d'an Free duniya ne komai na gani sai nayi mgana haka kurum na rika shuru ana Cutata" Nasan daman bazai yi shurun ba shiyasa na kyalesa,ranar makara ya yi zuwa wajen aiki sai da rana ta take ya fita shima din domin suna da Meeting ne. da bazai je ba kuma yace min da an yi mgana zai ce to sai jiya ya fara kara'in sa Tife na hutawa ne shiyasa nasan zai aika yasa na rike bakina ina kallonsa shi kuma yana min dariya. Ranar yana dawowa ya fad'amin yan Office din su sun shiryamana Liyafan aure,ya kuma ce in dai bana ra'ayi bazamu ba nace meyasa..?zamu je mana tunda don mu suka had'a walimar. Ai ko mun je yar liyafan ta Dare ce,Shi Suit baki da Fari yasa ka ni kuma sai na nuna mai wani less d'ina mai baki da blue sai yace na saka shi Riga da zani ne na saka takalmina baki mai saukakkan Tudu sai Dan kunnena zinare da aka siyamin da Sadakina harda zobba. Ban yi kwalliya ba amnh nayi kyau Tunda kusan shigar alfarma tana ma mata kyau,mayafi na saka mai girma kalan kayana na rufe jikina da farko ma sai da na tambayesa ko mayafin ya yi..?Sai yace min ko Hijabi na so sawa na saka abuna bakomai ra'ayina ne. abunda zai fi min daidai a jikina. Sai ni kuma na kada baki nace"Kai dai ka dubamin ko ya yi. kasan abun ka da ba yar boko ba kada su ganni su ce