Sashe 61
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
suka dawo, sai ta koma gida Saboda harkan gabana nake yi yasa ban damu da na Bibiya ya suka kare ba,Nidai bana fatan tun yanzu auran su ya samu matsala ina Fatan su tara kyakyawan zuru'an da Yaya Ishaq yake mafarki da fata ko zai daina kallona a matsayin wacce ta zama Sillar shiga tsakaninsa da mafarkinsa da Burinsa. Mun cigaba da zuwa muna koyan abubuwan da ake koya mana har ga shi yau da gobe bata bar komai ba zamu kammalah,Watanni uku kamar kwana uku ne a wajen Ubangijinmu,Ranar jumma'a muna Hutu asabar zamu gama gabad'aya ranar Lahadi kuma za'a sallame mu da Takardan shaidar abunda muka koya, a kuma wajen za'a bama wad'anda suka chanchanta tallafi. Ranar jumma'an ina gida tunda bama zuwa ranar Sai ga Badariya da Raliya sun zo min da labari mai dadi bayan mun gaisa na kawo musu ruwa su Amir suna haraban gida suna waasa. Raliya ta kalleni tana fadin"Anty Fa'iza ina tayaki Murna kin yi abu mai kyau, Hajiyar mu tana ta fad'amin a duk report din da ake kawo musu a duka Rukunin da kike Dauka kin zama zakara sosai ma'aikatan suke yabawa da kokarin ki" Sai naji dadi na godema Allah acikin Raina Badariya na gefenta tace"Ai Anty Fa'iza ba daga nan ba Raly ni daman nasan zata iya" Raliya tace"Haka na fad'a ma Hajiya..Nidai mun zo cin sauyin Sabon girki ne Anty Fa'iza me zamu samu..? Na mike ina Dariya nace"Daman jiya alalan mai kifi da kwai aka koya mana yau daman ina da niyar gwadawa" Ihu suka saka gabadayan su Badariya tace"a hada mana har da lemu mai Dadi don Allah" Sai nace to a raina ammh ina Tunanin ina zan samu kudin kifi da kwai, tunda ina da wake kamar Badariya ta sani taja Raliya suka fita ba jimawa sai ga shi sun dawo da cefane har da kankana da kankara sukace Lemun kankana suke so nan da nan ko na shiga Kirchen na fara aiki suka shigo suna Tayani da hira da d'an taimakon da bazai gagara ba. Nikan Waken Amir na aika ya kai mana makota muke da gidan nikan, kusa da gidan Habiba ne daman in dai aike ne ko nika kusa haka to Amir nakan aika Tunda ba nisa sosai,cikin awa uku muka gama alalan kwai da kifi na kuma had'a musu lemun kankana nan sukayi sallar mangariba suka zauna suka ci suna santi Raliya tace"Anty Fa'iza in da saura a samin a leda sai na kai ma Hajiyarmu alalan nan taci taji itama" mirmishi kawai nayi daman na Mudu daya da rabi nayi na Dibar mata da yawa tace kowa sai yaci a gidansu ta karishe da Fadin"Zan miki tallah Anty Fa'iza dole mu bude Fa'iza Kitchen" Badariya tace"Sosai ai Oder zamu fara yi wannan girki ai ko Hotel ko Restaurant albarka" Haka suka yi ta zuzuta girkin da zasu tafi mukayi sallama suka tabbatar min da jibi zasu zo tunda taron a babban Hall din makarantar su ta Umaru musa yar'aduwa za'ayi. Washegari da mukaje gwaji dukkanmu mukayi,Ma'aikatan duka gefe suka koma suka bar mana abunda zasu yi ranar, Kunun gyad'a muka yi bangaran abun sha kuma ni na zama zakaran rukunin mu sai bangaran girki kuma yam ball muka yi ma'ana Fanken doya,shima ni na zama zakara na Rana ma rukunin hada Kolaccha ma ni na Jagoranci Rukunin mu,haka bangaran had'a Dilka da Halawa anan wajen muka mulkama kafafun mu da Hannuwan mu,wasu har da Fuska ni dai ban saka ba,Sannan mun had'a Turaren Humra na ruwa mai kamshi shima muka goga a jikin mu saboda muji yanayin kamshin,Ranar sai Yammah na dawo gida su Amir gidan Sa'adatu suka zauna sai da na dawo. Ranar Lahadi kuma na fada ma su Amir su yi min addu'a yau zan gama abun da nace musu ina yi suka yi ta cewa Umma Allah ya baki sa'a na amsa da Ameen. Saboda taron gamawa ne Tare da Ahmad naje bansan makarantar ba, mai adaidaitan ya kaini hall din ba Boyayye ba ne ina zuwa na tambayi inda ake taro wasu yanmata suka nuna min, da wuri naje wasu duk basu zo ba ammh naga wasu daga cikin mu. Karfe sha d'aya aka fara taron manyan mata masu alaqa da kungiyar duk sun zo ciki har da Hajiyar su Raliya na ganta ba su gayyato yan jarida ba Saboda basa son duniya ta sani su don Allah suka yi,Sai mu kawai da muka samu Horan sai kuma yan'uwan wasu daga ciki da ma'aikatan da aka Dauka suka koyar damu sai yan kallo. Su Badariya sun zo su da gayyar kawayen su sai dai hannu suka Dagamin, tunda su suna baya mu kuma gaba akace mu jeri mu Talatin din da muka samu Horan. Bayan jawaban godiya da kuma Fatan alheri ga wannan kungiyar aka gayyaci wata Hajiya Zubadai itace kamar ma'ajin kungiyar reshen Jahar katsina ta fito tayi jawabi akan manufar kungiyar da kuma manufar taron da suka shirya garemu na mata talatin da suka koyar da su sana"o'i goma. daganan aka bata sunayen mu ta rika kiran mu d'aya bayan d'aya muna karban Takardan shedar abunda muka koya ni ce ta goma acikin wad'anda ta kira Fa'iza sidi karofi. Dayake tana amfani da amsa kuwwa abun mgana, najita na fita Ahmad na goye a bayana ta bani Takardata sai da nayi Hawaye,Ina gani wata ta kusa da ita nayi mata rad'a a kunne ta kalle tace"Fa'iza sidi karofi ko..? Na jinjina mata kai sai ta bani Hannu muka gaisa cikin kayattacen mirmishinta tace"Weldone Fa"iza" Duk da ban ji me tace ba nasan yabo ne sai na jinjina mata kai sannan na koma na zauna,ina Duba Takardan Hannuna da Turanci ne sunana kad'ai na iya ganewa aciki,ammh nasan ko a hakan na tsaya na cinma wata gagarumar nasara a rayuwata ba Nakasashe sai Mai nakasar zuciya, sannan akace babu maraya sai Raggo. in ka tashi ka nema bayan ka bama Allah za bi to shi kuma Allah zai saka maka da kyakyawan sakamako. An cigaba da kiran mu har zuwa ta karshe sannan wata Hajiya laila daga kaduna itace mai rike da mikamin P.R.O na kungiyar ta fito zata bada shedar girmamawa ga wad'anda suka zama zakaru a rukuninsu,Allahu Akbar ban taba zata ba, Ba zato ba Tsammani naji sunana Fa'iza sidi karofi na fita aka bani wani d'an kwalba mai ban sha'awa da sunana ajiki sannan matar ta tsaidani tayi jawabi da turanci sannan tayi da Hausa tana mgana akan cewa ina da Hearing problem, sannan ban yi boko ba.ammh na iya zama ta farko a fanni masu kokari a dukkan abunda na Koya, sannan ta sake bani wani abu nazare a wuya na ta makalamin na Girmamawar na koyi abu hudu masu wahala a acikin wattani Uku,Sai tafi raf raf ta bani Hannu muka gaisa har tana yi ma Ahmad dake bayana wasa ko da na koma na zauna sai na daga hannuwana sama ina fadin"Allah na gode maka..Alhamdullahi ya Allah dukkan wata ni'ima daga gareka ne" Matan dake kusa dani suna ta min murna ina amsawa bakina har kunni na juya ina hangen su Badariya ta D'agomin hannu na Daga mata kyautan da takardan da aka bani, ita kuma sai ta Dagamin babban yatsanta alamun jinjina. Bayan ni an kira mata uku suma an basu lambar girmamawa ta zama zakaru a rukuninsu,Daganan an wakilta uku daga cikin mu suka fita suyi jawabin godiya ni dai nace bazan iya ba Saboda ban taba fita gaban jama'a nayi mgana ba ko karban kyatuttukan ma Dakyar na iya fita kamar zan fadi haka na rika ji. Ma'aikatan da suka koyar damu suna sun yi jawabin godiya ga wannan kungiyar sannan sun gode mana Bisa yadda muka basu had'in kai har muka koyi abunda ake so mu koya har kwalliya ta biya kudin sabulu. Daganan sai suka koma gefe suna mganganu bayan minti goma aka sanar da kungiya ta ware zakaru guda goma da kungiya zata bama tallafi,Sauran kuma da ba'a basu ba,ba domin ba su kai ba ne a'a haka tsarin kungiya take suma nan gaba zasu iya samu. Gabana sai ya fara fadi na riga nayi yakinin ko ba'a bani ba bazan bari abunda na koya ya tafi a banza ba sai ga shi nice ta Biyu Fa'iza sidi karofi Hawaye sharr suka zubomin na kasa sharesu bakina har kunne na fita. Kudin a Farar takarda ne an nade sannan ga sunan kungiyar ajiki Hajiyar su Raliya ta bani na Duka har kasa zan karba sai kawai na Daidaici gabas duk da goyon Ahmad dake bayana ban damu ba nayi Sudujul Shukur sai Hall din ya Dau Tafi da kabbara ina dagowa ina hawaye Shabe shabe na saka hannuwa bibbiyu na karb'a sai ta bani abun mgana tace nayi godiya,muryata ta shake ga kuka sannan ga yanayina cikin mganata nace"Alhandulillah ya Allah Godiyar ta sace.Domin abu mai kyau ko akasasin sa daga gare sa ne,Ina godiya ga wannan kungiyar na gode..Madallah da mutanen kirki, madallah da mutanen kwarai masu karamci. Nagode Allah ya jibanci lamuran ku, kamar yadda kuka jibanci namu Allah ya suturtaku kamar yadda kuka suturtamu Allah ya albarkaci dukiyar ku da ya'yan ku da iyalan ku gabadaya, Allah yasa wannan aikin taimakon naku ya zama mizanin ku a gidan Aljannah..Nagode Nagode, na yaba ubangiji ya gani sannan yafini yabawa" Ina ma wannan kungiya fatan alheri Nagode" Duk da mganar bata fita sosai ammh sun fahimta sai tafi su kuma suna ta amsawa da Ameen,ina tahowa muka had'e da Badariya muka Rungume juna Fadi take"Congratulation Anty Fa'iza" Ahmad da yaji matsa sai kuka na Sauke shi ta Dauke sa ta dagasa Sama tana fadin"Kai yau ranar farin cikin Umman ka ne ba kuka" An ta kiran sauran ana basu suna addu'a mata da yawa muna cikin wata Rayuwa masu kuka in an basu suna da yawa,asauran da ba'a basu ba suma ance kungiya zata san abunda zatayi musu daga karshe sun horemu da mu tashi Tsaye mu mori abunda muka koya, acikin Gidajen mu da kadan kad'an watarana sai mu zarce Tunanin mai Tunanin sun Hore mu kada mu zama ballagazun mata mu zama mata wad'anda zasu iya shiga ko'ina saboda kansu da ya'yansu. maraici ba komai ba ne in dai