Sashe 111
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
a gabana Lokaci d'aya yana fadin"Kin gane Fa'iza ki Fahimceni wlh ba da wata munafa nayi wannan mganar ba. Nasan ke zan iya sakaki komai kiyi min sannan zaki zauna dani ko a dakin Bukka ne,ita kuma ba kamar ke ba ce shiyasa kikaji nace haka don Allah kada ki Daukeshi a wani abu" Ya karishe fad'a yana min uban magiya sai kawai na mike idanuwana ne suka ciko da kwallah me na zama ne.?na tabbata har abada in dai a Rayuwar Ishaq kabir korofi ne ni Fa'iza bazan taba samun daraja ba. Gaban Wadrope d'ina na tsaya kawai na rasa me zan yi ma saboda takaici,Ina jinsa ya mike yana fadin"Kin ji Fa'iza baki ce komai ba..? Juyowa nayi bayan na Saita kaina Lokaci d'aya nace"Me kake so nace.?ai ba shawarata kake nema ba Hukunci ka yanke sai kuma ka ke bani Umarni,ba komai kada damu ni daman ban taba had'a kaina da matarka ba nasan tafini Daraja. Zan kwashe kayana kada ka damu ka fad'amata zan bar mata Dakina na har Abada" Na fada Lokaci daya ina kokarin wucesa na fita Daga dakin kawai sai ya Riko hannuna a fusace na juyo ina kallonsa irin kallon da na sakar mai ne yasa ya sakeni da Sauri a Shake nace"Nace maka zan bar mata dakin nawa har abada daman ai D'ofane nake kada ka damu. Hafsah daman ba zama zatayi ba Abba na nema mata Transfer zata koma kaduna yara kuma ya'yanka ne ko a soro ka zaba musu su zauna bazaka samu matsala da Fa'iza ba" Ina gama fadin haka na fice daga d'akin domin ji nayi iskar Dakin tamin kad'an,na rasa ina zan shiga sai kawai na shige kitchen na fara safa da marwa Anum ta shigo kawo kwanuka ban ma ji shigowarta ba sai ji nayi tace"Umma lafiya..?Da sauri na goge kwallar da suka kawomin,na juyo ina kirkiro mirmishi kafin nace"Bakomai kin gama wanke wanken.? Kai ta dagamin kafin tace"Yanzu zan wanke tsakar gidan ko Umma..? Sai na jinjina mata lokaci daya ina fadin"Gama ki tayani zuba zobon nan in ya wuce kada su kawo wuta bamu saka ba" Sai ta amsamin da toh Umma,Falo na koma shi kuma daidai ya fito ina ganinsa sai na juya na fita wlh bana son ma ganinsa,a kwanakin baya sai naji kamar Burina zai samu Rauni na fara Tunanin sauke kudurina,ammh yanzu na ji na samu karfin gwiwan da zan iya tunkaran komai menene tabbas ina Bukatar Sabuwar rayuwa ina son na shaki iskar yanci nima. Gabadaya yini yayi son kara min mgana ni kuma ban yarda mun had'u ba,ga shi dai nace na amince ammh kuma Fuskata ba fara'a Da Daddare na kira Abba muka gaisa sai na masa mganar Hafsah cikin barkwancin sa yace"Ina ta kokarin nema mata Transfer Fa'i..Wlh tallahi ko kuma ba domin aure ba,da gabad'aya zan tattaraku a gidana"Sai nayi dariya ina Tambayansa Ammi yace"Tana chan ta na kwalliya kinsanta gayu gayu dai Mamam Nanah taki ta bar ma yara"Da Sauri nace"Abba ta bar ma yara ka kyallo wata yar caras" Sai ya fara Dariya yana fadin"Fa'i Laala..aiko baku isa ku hanani kara aure ba.ku gama shafa dai jan bakin da hoda sai nayi ehe" Ni dai sai Dariya nake yi tuni Abba ya mantar dani Damuwar da nake ciki mun jima muna mgana,Sannan muka yi sallama,Mun gama wayar kenan sai ga Kiran Nana Fatima itakam sai da taji yanayina ba Dadi tace"Fa'in mu ya ya ne.?naji ki wata so silent ne" Sai nayi saurin ce mata kaina ke ciwo sai tace na sha mgani na kwanta da Safe zamu yi mgana da haka muka yi sallama sai kawai na kira Goggo ita har ta Tsorata cikin Tsoron tace"Fa'iza lafiya kuwa.?goma saura na Dare fa" Ina dariya nace"Lafiya lau Daman na kiraki mu gaisa ne naga kwana biyu kin manta da D'iyarki"Sai goggo tayi dariya kafin tace"Kina raina Fa'i nasan kina lafiya ke da yaranki,hidima tayi miki yawa Fa'iza kinsan sana'ar hannu tana da wahala nasan sai hankali yanzu"Gyada mata kai nayi kamar tana ganina kafin nace"Na saba goggo ba matsala ga Anum kinsan tana gida sannan in Hafsah na gida tana taimakamin,haka ma yaran ma in sun dawo. Amir kinsan san shi sarkin aiki su shara har girkin su taliya ya iya Goggo"Sai goggo taji dad'i har sai da ta bayyana min cikin Murnan ta tace"Masha Allah Dakyau.Dama iyaye su rika tunani irin naki Fa'iza su rika koyama yaransu, aikace aikacen gida tun suna da kananun shekaru, saboda taimakon iyaye da kuma taimakon kansu a duk inda Rayuwa zaata kai su Allah yayi albarka Allah ya shirya miki yaranki,Allah ya Daukaka su alfarman Annabi muhammadu salallahi alaihi wasallam" sai na samu kaina da Hawaye sun cikamin kwarmin idanuwana, ina amsawa da Ameen Ameen cikin jin dad'in da ya bayyana har a murya ta. kafin nace"Goggo Baba ati tana kaduna abunta..? Goggo tace"Tana ko chan Fa'iza ta samu hutu,Inno tace bata son ta dawo ta samu abokiyar zama ai ma ginin Abban naki an kusa gamashi kila in ya kammallu ta dawo" Kai tsaye nace"Kila ta dawon to.nima Hutu nake son nazo miki Goggo "Dariya tayi ina jin ta Dauka Zolaya ce sai tace"Ina maraba da Fa'iza Allah ya kawo ki lafiya"na amsa mata da Ameem daganan ta tambayeni megidan da Yanayin zaman mu da Mama nace lafiya lau kamar bata gidan. Goggo tace'"Nima naga duk tayi sanyi.Rayuwa ta gara Saudatu daman na fad'amiki watarana sai tafi ruwa sanyi a wajenki"na jinjina kai ina Tunanin yadda Mama ta zama kamar kankara yanzu,Duniya ce da mutanen cikinta suka maida ita haka. Bayan munyi sallama da Goggo na jima ban yi barci ba,Hafsah tana Dakin yara tana karatu sun kusa fara Jarabawa Ni da Anum me muke kwance ita har tayi barci ni kuma ina faman sake sake a daran nan na yanke ma kaina abunda zai fissheni bayan na roki Allah kada ya barni ni kad'ai ya yi min jagoranci. Da Safe wasai na tashi,Duka aikin gidana ni nayi abuna. Abun kari kawai Hafsah tamin,Sai aya data wanke ta mikamin nika kafin ta fita,ni kuma sai ta barni da Dafa zobo,Ganin yadda nayi ne ko da Safe saboda a gaban yara ne muka gaisa na Sakar mai Fuska suna watsewa na had'e raina gim ko fara'ata bai gani ba. Mama ta aiko Anum ta kirani ina zuwa na durkusa na kara gaisheta ta amsa cikin kallona Lokaci d'aya tana fadin"Ishaq ya same ni da wata mgana. Wai zaki koma Dakin yara Zainab zata zauna a dakin ki nace kin amince ne yace eh! shine nace sai na tambayeki" Kai tsaye nace"Eh Mama yau zan fara ma Tattara kayana. yaran kuma duk inda ya ijiyesu daidai ne a wajena" Sai ta muskuta tana fad'in"yaran ba matsala ga daki nan su zo mu zauna damam xaman kada'ici ya isheni kece bana so mu kara yi miki wani rashin adalci kamar yadda muka yi miki a baya,Shiyasa nace sai naji ta bakin ki,ki fad'amin in hakan bai miki ba to bai isa ba" Sai nayi mirmishi takaici kafin nace"Bakomai Mama na amince ni daman ba mazauniya ba ce.Dakin daman ai jingina ne, Zainab ce ke da wajen zama na har abada" Nasan bata gane kan mganata ba, sai dai nauyin baki yasa ta kasa min mgana har na fice,ina komawa Daki bayan mun gama hada zobo mun zuzzuba agoruna Anum ta jera a Frezee,kunin Aya ne zan had'a shi jira nake nepa su kawo wuta. Anum na bar ma sharan Falo da gyaran kitchen, ni kuma na shiga Dakina na fara had'a kayana a waje daya duk abunda nasan nawane na Daukosa babban ghana d'aya gareni itama sakon kayan sallar yara aka kawo aciki daga kaduna kuma tamin kad'an sai na kira Hafsah nace in ta shiga kasuwa ta siyomin manya guda biyu Kafin dare wardrope dina kaf ba kayana aciki Hafsah ta siyomin manyan ghana guda biyu sun isheni na dura komai nawa,aciki akwai wasu kayan da ko di'nka su ban yi ba. na Ishaq ne ban kara dinka kayan da ya siyamin ba,tun bayan auransa da zainab hatta kayan da Anty Binta ta bani na Fad'an kishiya suna nan suma na Had'a masa kayansa waje daya. Gadajen yara daman duk ya b'abb'alle,sai nayi tunanin na basu na Dakina da wardrope din ya ishe su saka kayan su,nasu kuma a gyara ma Anum tunda ita macece ni ba zama zan yi ba,so kayan basu da amfani a wajena. Da dadadre suna falo da shi yana musu karatu,na fito ina kallon Amir kafin nace"Amir ku fara had'a kayanku waje daya,ka taya kannen ka su had'a nasu .Anum na fara had'a miki naki kema kije ki karisa in kun gama" Da mamaki suke kallona ammh sai na juya zuwa kitchen ina ji suna tambayanta Umma ina zamu..? Sai na bar mishi ya basu amsa sai kuma ya kasa ina kitchen din ya Biyoni yana fadin"Fa'iza bafa yanzu ba ne naga kina ce ma yara su had'a kayansu' Ina juya tumatur din da Hafsah ta Dora Tafashensa akan wuta nace"Eh gwara su fara had'awan tun yanzu kada sai lokacin yayi kuma basu samu sararin had'awa ba. gwara tun yanzu kowa yasan matsayinsa" Na fad'a ina kokarin rab'asa na bar kitchen din sai ya bake hanyar yana fadin"Fa'iza.." Kai Tsaye na kallesa ina fadin"Na'am Ishaq" Sai mamaki ya hansa mgana,Girata na Daga ina fadin"Bani hanya na wuce" Ba musu ya matsamin na fice ina jin wani irin Tukuki acikin kaina Amir ne ya taso yana fadin"Umma ina ZAMU KOMA..?Ko zamu yi tafiya ne.? Ban kallesa ba nace"Ku yi abunda nace Amir kaji" Sai ya amsamin da Toh ammh sai jikinsu duka yayi sanyi,nan na barsu na shige Dakina ina Sauke numfashi,Adaran na saka Hafsah ta taimaka musu suka had'a kayansu itama ban bata ikon mgana ba sai dai ta tambayi yaran Anum tace"Umma bata ce mana komai ba" Sai itama bata kara mgana ba, ammh ta kara tsorata da ganin na kara had'a kayana a karo na biyu wannan karon bata san kuma me zai iya Dakatar dani ba. Lalle kana naka Allah na nashi Washegarin jumma'a da Safe Ishaq ya samu wayar Dr.Lawal inda yake sanar da shi an gano saka hannun nan ba nasa ba ne, kwaikwayo ne na