Sashe 60
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dubu buya kad'ai na Taba ukun suna na nan ina Boye da su, sai da hakan ta faru na Daga hannu nagodema Allah domin zasu yi min amfani. Kawai sai naga ya sha gabana a matukar fusace cikin d'aga murya yace"Ni kike nuna ma ban isa dake ba Fa'iza..? Baya naja ina fadin"Ban ce baka isa ba.Sai dai na nuna maka isar taka ce wannan karon, bazata isa a wajena ba ka bani hanya na wuce ina bata Lokacina" Sai ya tare hanyar ni kuma sai na kasa wucewa cikin Daka tsawa yace"Ki koma nace ba inda zaki je" Sai nayi wani kayattacen mirmishi takaici na Fahimci in na zauna haka Ishaq zai cigaba da Nakasa rayuwata kamar yadda ya saba to wannan karon ya makaro domin d'an zaki ya riga ya girma. Sai kawai na kallesa ido cikin ido kafin nace"Sai dai kayi hakuri wannan karon bazan ji mganarka ba.Na fada maka tun Ranar da ka zabi Zainab da Ahalinta sama da ni..Nima Daga wannan ranar na zab'i Rayuwata da ya'yana sama da kai" Mganganuna sun dake sa sai ya kasa motsi har na raba ta gefensa na wuce abuna,Kafin na fita sai da nayi addu'an fita gida,sannan na karisa gidan Sa'adatu muka gaisa na kwanto mata Ahmad Allah yasa yayi barci ta karbe sa tare da kuninsa tamin Fatan Alheri daganan na fita na samu Adaidaita sai cikin gari. Makarantar ta yan mata ne zallah suna barayin su sannan mu kuma inda zamu zauna wani babban aji ne, ko da nazo mata sun fara taruwa sai dai ma'aikatan basu riga sun kariso ba,na gaisa da matan dake kusa dani muka zauna jiran su tara da wani abu suka iso,,Rukuni rukuni suka jeramu a layi mun nuna katin shaidarmu sannan suka sanyamu a rukunin da zamu fara koyan abunda ya kawomu. Ni rukunin girke girken aka sanya ni shi zasu fara koyar damu sai sun gama sai ayi barayin Had'a lemuka da rana ne Rukunin Koyar da Turaren wuta da Had'a Dilka.. Sai na Fahimci da Safe duk abun ci ne zasu koyar damu shiyasa sai suka raba abun,Ni dai ban tsaya kalle kalle ba na saka ido sosai,ina Fahimtar komai masu koya mana Rukunin Farko,Su biyu ne dukkan su mata ne, Daga ganinsu sun san kan aikin su Sanye da Fararen riga da Hula na masu kirkin da muke gani a Kwatin Talabijin. Ranar farko wainar kwai suka koya mana da miyar gyada mai allayahu,sosai na karu na kuma rubuta sunayen abubuwan da suke fad'amana bamu gane ba,Suna yi suna yi mana bayani yadda zamu fahimta sannan in baka gane ba sai kayi Tambaya komai da komai na girken girken su, sun zo da shi suka kafa karamin Dakin girki a babban D'akin da muke ciki, nayi tambaya in da naga ban gane ba.kuma sun kara yi min bayani suna da Sauki kai matuka da iya mu'amala. Daman kuma Koyar damu ne aikin su, har kuma mh iya sun kuma tabbatar mana da cewa zamu iya girke girke masu kyau da inganci.bayan an gama dukkanmu muka D'andana mu biyar ne a rukunin Girke girken,muna ta santi saboda yayi dadi sannan da alkawarin in muka koma gida zamu gwada mu gani. Sai rukuni na biyu Had'a lemuka,Zobo suka fara koya mana Had'ashi,Duk da na iya zobo sai naga nawa shirme ne ashe ga inda ake zobo nan,Ranar anan Rukunin ya kare shima sun bamu mun sha dad'i,Daga karshe sukace in da bamu gane ba mu yi mgana ni dai akwai karambani daman duk abunda ban ji ba sai da na tambaya suka kara gayamin,Ranar farko kawai da fara zuwana naji araina zan iya komai insha Allahu na dawo gida da Farinciki na iske Ishaq baya gidan ban Damu ba daman na fita da key da na ga ya Kulle gidan sai na bude bayan na Biya na Dauko Ahmad. Ko girki ban yi ba Dakunan kawai na gyara na share, Lokaci yayi na makara ma a rukunin Rana sai d'aya da Rabi na isa har an fara an raba mutane kowa da Rukuninsa sai da na nuna Katina sannan aka kaini Rukuni na,Abu na farko da suka fara koya mana yadda zamu had'a Turaran kamshi na Icce ne ranar shi mukayi har aka tashi,shima in da bamu gane ba suna bamu ikon Tambaya in da kuma zaka manta sai ka Rubuta na dawo gida karfe hudu da Rabi na yammah na biya gidan Sa'adatu na kara dauko Ahmad sallah kawai nayi na shiga kitchen Saboda yan makaranta suna hanyar Dawowa. Duk da na gaji ammh ban damu in dai aikin wahala ne na saba shi kuma ya zame min jiki,sai da nayi wanka sannan naji dadin jikina Yara suka dawo makaranta da yammah suna ta Tambayan Daadan su nace ya fita bansani ba,ko saboda abun da ya faru ne sai da yaran suka gaji da jiran sa, suka kwanta sannan ya Dawo ina Falo ina Tattara kayan da suka zubar daya shigo nayi mai sannu da zuwa bai amsani ba sannan bai kalleni ba. ya shige bangaransa a raina nace ko nace a banza. Washegari ma ya rigani fita,Nima ko Lokaci nayi na yi tafiyata kamar jiya,Sai dai na Fahimce zan rika shan wahala in dai ina jeka ka dawo sai na yanke shawaran in mukayi sati uku, zan fara zama achan sai mun gama Rukunin rana sannan zan dawo gida gabadaya kud'ina kada su kare wajen adaidaita na rasa mafita. Yaya Ishaq kuma tun daga wannan sa'insan tsakanin mu mgana bata kara Hadamu ba, ni dai ina fita Hakkinsa in mun had'u ina gaishesa shine baya amsani duka duka kwana Hud'u yayi ya koma ko sallama bai yi min ba. ganewar ma da nayi bai kwana agidan ba nasan duk tsanaani in dai yana gari to zai kwana agidansa.nima ko na tattarasa na watsar domin da gaske nake yi na zabi Rayuwata da Rayuwar ya'yana sama da tashi Rayuwar. Na cigaba da zuwa wajen koyon sana'o'i na hankalina kwance kusan indai akace wannan abun shi kad'ai ne Hope din ka da Fatan ka to gabad'aya Tunanin ka da Rayuwarka zaka Dorasa akansa ne,ya kuke gani in hakan ta faru da mace irina da daman jiran mafita take yi..?to kamar misalin nice Domin na maida gabad'aya Hankalina da natsuwata kan abunda nake koya,Shiyasa duk nafi kowa ganewa a Duka Rukunina tun bamu Rufe wata ba Ma'aikatan suke yaba hazakata da Kokarina,Gashi abubuwa Hudu nake koya ammh kwakwalwata tana Daukan abubuwa dadama. sannan ina gane duk abunda aka koya mana. Muna rufe wata d'aya da Farawa na koma ina zuwa sau d'aya in na tafi sai Hudu nake dawawo saboda in aka tashi Rukunin Safe sai na zauna sai Rukunin yammah Tunda ma'aikatan suna nan suma ka'ida sai Hudu na yammah suma suke tashi, duk abunda muke yi suna daukan komai sannan suna Rubutawa saboda suna turama kungiyar Bayanan komai. Yau da gobe zara bata bar komai ba kudin hannuna suka kare sai na koma takawa da kafata yara na fita makaranta nake fita da nisa sosai kafin na kai na jigata ammh hakan nake Daurewa na sama kaina yakinin ba wanda ya isa ko ya samu yana kwance, sai da ya fita ya wahala,Muna Hutu Ranar jumma'a duk sati sau Shidda kenan to ranar ne nake samun na gyara gida, har yi ma yara wanki da Sauran aikace aikace ni kaina nasan na Rame saboda wahala. Badariya sai da muka raba rabin watanninmu sannan tazo gida ranar wata jumma'a muka hadu a bakinta nake jin Anty Binta tazo sau biyu bana gida ta je ta fad'ama Mama sai Fada take,Tana fadamin Maman ta kira Yaya Ishaq din tamai mgana ba'a san me ya fada mata ba,basu kara mganar ba,Badariya tace ita dai tayi gum da bakinta bata tofa ba, tana ji Mama na fad'an na fara gantalin bin gidajen makota.nayi dariya nace gwara da kika yi shuru baki ce musu komai ba. Araina naji mamaki ban Dauka Yaya Ishaq zai yi Laushi ba ni dai abunda na sani bazan zauna Damar da na Dade ina jiranta ta Kubcemin ba,Bandamu domin ba ta su nake ba ta kaina nake da ni da ya'yana. Badariya taji dadin yadda na fadamata muna koyan abubuwa da Dadama,sannan wahalata ta ragu saboda Sa'adatu ta Daukemin Laluran Ahmad sai abun yazomin da Sauki,Ban gayama kowa ba So nake ko yan Karofi na basu mamaki Fata na da Dakiyata azabeni cikin mutanen goman da za'a basu tallafi saboda zai yi min matukar amfani. Yadda Yaya Ishaq ya tattarani da ni da ya'yana gefe d'aya.haka nima na tatrarasa na watsar Sai dai ya'yansa ban isa na cire musu tunaninsu akan sa ba,ko bakomai mahaifin su ne,ya zama Dolen su ni kuma ko da yake mijina ai ba Dole na ba ne,Na riga na jigata da tafiyar kasan da nake yi ammh ban ji ko sau d'aya na gaza ba nayi fashi sau Biyu shima Ahmad ne yayi ta zazzabi ba Halin na fita na bar shi kuma zuwa da yara an hana, shiyasa na zauna na Kula da shi har yaji sauki muna gabda cinye wattani ukun mu,Badariya ta dawo wajena da kwana ashe Mama da Anty Binta Abuja sukaje sulhu Zainab ta samu ciki sai suka yi sa'insa da Ishaq akan Farhan bai yi kwari ba, zata zubar da cikin shi kuma ya hana ita kuma sai ta Ture mganarsa ta yi mgana da mahaifinta yace ta zubar, tako je aka markadesa shine rigima ta kai su ga Har Ishaq din ya mari zainab din ai ko Badariya tace Mahaifinta ya Kira Mama yana fadin Ishaq ya gama marin auransa kuma sai yayi mganinsa sai ya yi kararsa a kotu,Ai ba jaka ya aura masa ba.shine Mama ta rud'e ta yi ma Anty Binta mgana ta rakata suka tafi Abuja su sulhunta mganar. A raina sai nace tun yanzu..? Auran barikin fa kenan,ai na Dauka ko me zainab tayi Yaya Ishaq zai yi hakuri da ita,tunda ita yar so ne kuma ita ya zaba ban dai nuna komai ba nayi fatan Allah ya Daidaita su Saboda ni bazan yi Dariya don haka ta faru ba Namiji ai duk inda yake yana amsa sunan sa na Namiji ne. Wajen kwananta hud'u a gida na sannan su Mama