Sashe 46
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
rike da jakar kayanmu muryata shake nace"Amir rike ma Anum Hannu" Gaba nayi ban tsaya bi ta kansu ba yau,ina dai jefa kafane kalaman Yaya mariya na dawomin da cewa in tamadina ta mutu sai nafi kowa kuka,Saboda Halin da nake ciki Tun daga Bakin asibiti har anguwan su Tamadina anguwan mallan yusuf Dutsemah a kasa muka je shi Anum ta gaji da kiran Umma ban ko amsa ta ba, nagaji bata kanta nake yi ba shi kanshi Amir din ya jigata ni kuma nafi su wahala ga Goyo da Musty ga Jaka ko da muka iso futu fitu kamar wad'anda suka fito daga Cirani kofar gidan cike da maza masu karban gaisuwa ni bana wani gani sosai ban iya gane kowa ba ina gaba su Amir na bin bayana har Cikin gidan da Mata suke cike Damkam ni dai so nake na isa Dakin Tamadina na tabbatar da ta rasu ne ko wasa ne..? Ban san me matan da na wuce a tsakar gidan suke fad'i ba sai da na Dangana da Dakin Tamadina naga Mutane zazzaune suna ta kuka Goggo na fara Hangowa tana ganina ta Dago tana fadin"Ga fa'izan ta iso ma ba ma sai Isan yaje Dauko ta ba" Jakar Hannuna na Sauke tare da Musty na karisa gaban Goggo na Duka ina fadin"Goggo kada kice min da gaske ne abunda aka fadamin a asibiti wai Tamadina ta rasu..? Ina mgana sai hawaye sharr Goggo ta rike kafadata tana fadin"Sai hakuri Fa'iza duk wani mai rai mamaci..Tamadina ta amsa kiran Mahallincinta yau da asuba basu jima da dawowa daga makabartan ba" Ni dai naji ni na sulale jikin Goggo na fashe da wani kuka,Kukan da yasa Dakin ya rikice Ahmad dake baya na ya fara kuka jin na Dannesa haka ma Musty da Anum Amir ne kawai bai saka kuka ba Goggo ta jani ta sunce goyon ta Dauki Ahmad,Ya Asiya kuma ta mike tana sharan kwallah tana Fadin"Hafsatu riko Amir ga shi chan" Dukkansu kukan suke yi ammh na zucci ta mike ta rikosa suka zo suka zauna sai ya kalleta yana fadin"Anty Hafsatu Maman Umman ce ta mutu.? Sai ta gyada mai kai Lokaci d'aya ta Rumgumesa tana kuka. Bansan adadin Lokacin da na Dauka ina kuka ba, nan da nan wani malolin abu yazo ya taremin makoshi ya kasa wucewa hakuri kawai su Goggo ke bamu Daga baya sai kuka na ya Dauke sai dai Tafarfasan zucci kawai. Har washegari ban iya saka komai abakina ba Hafsatu ce ke ta Dawaniya da su Anum,Ahmad kuma yana Hannun Goggo har ta da su Yaya mariya sai da na dawo ina basu tausayi suka koma suna Lallashina naci wani abu Dakyar adaran na sha Farau Farau sai dai ko minti goma bai yi ba acikina na amayar da shi na koma ina Numfarfarshi Bakina baya da wani Dand'ano ballatana na iya cin wani abu,sai Ranar Biyu da rasuwa na samu nasha Fura ya zauna acikina Mutane Dabam dabam sun zo gaisuwa Dangin mazajen su Yaya mariya da mazajen kansu,suna nan da su ake zaman gaisuwa hatta da yan makarantar su Hafsatu sun mata kara na zuwa da kuma kololin abincin su,Hatta da sauran dangin mu ta bangaran uwa suna nan tare damu,ammh ni ba Mijina ba Ahalinsa sai ranar uku sai ga Mama da Anty Binta sun zo da rana suna ta wani jin kai,ko awa d'aya basu yi ba sukace zasu tafi,Muna zaune adakin Tamadina dukkanmu,ni ina gefe kaina a jikin bango ina bin kowa da kallo Carbi ne a hannuna inaja Hijabin Yaya Asiya ne ajikina da shi nake kwana nake tashi wanka kuma tun da nazo ko sau daya ban yi ba. Mama ta isa kusa dani tana fadin"Ai ya kamata ki koma gida hakanan saboda karatun yara sannan ki bar gida ba kowa kada a haura ayi sata." Bata bani mamaki da kalamaanta ba, sai na kalleta da Jajayen idanuwana kafin nace"Aka rasa rai ma aka Hakura ballatana abun duniya..? Na tsareta da idanuwana cikin wani yanayin da na tabbata bata ganina aciki ba.sai ta mike tana fadin"Rai ai da'ya ne, shi kuma asara ai suna da yawa" Ban ce mata komai ba Anty Binta kuma ko ya Hakuri bata iya ce min ba nima ko ban gaisheta ba,sai dai naji tana Tambayan ina yaran..? Naji Yaya Asiya na gaya musu Hafsatu ta shiga makota dasu tayi musu wanka,Da zasu tafi Mama bataji kunya ba tace Ishaq na yi mana gaisuwa Dayake basa kasar shi da Zainab. sun je india a Duba Farhan Saboda Haushi Goggo ce kad'ai tayi fatan su dawo lafiya ni kuwa Idanuwana na Rufe naji wani Tiriri na fitowa daga k'asan raina,kaina ciwo yake yi har na bala'i ga jiri,nasan bani da lafiya. ammh halin da nake ciki ban ki nima ace na Mutum ba,da dai irin rayuwar da nike ciki wacce bata da wani amfani. *Littafin KANA NAKA book2,3.paid book ne biya kudin karatun ki akan Naira N500 Regular posting sau d'aya a rana.* *Ko kuma tsarin VIP 1000 Posting sau biyu a rana akan wannan acct din 0552179550 Jamila Umar Gt bank,sai a turo shaidar biya ta wannan lambar 09069067488 Wannan karon babu tsarin kati,kowani tsari zaka yi ka turo ta POS,Mutanen mu na Niger kuma zaku tuntubi Kausar Aglan Nissa ta wannan lambar +22796562223* *Janafty*KANA NAKA..!* *Wattpad:JamilaUmar315* *Mallakar:Janafty* *Arewabook:Jamilaumarjanafty* *Ina gaida Matar Abba,Maryam jumare.* *Madalla da ke Hauwa'u(Real smasher)Fa'iza ta ce na gaishe ki* *Fa'iza na gaida mai sunan k'anwarta Hafsah Hafnan,(Sahibatu) tace sannu da Himma.* *Fa'iza ta ce na isar da sakon gaisuwarta ga uwar Dakin Gudayo da Yabi,tace madallah da kawar kirki irin ki Surayya Dahiru gwaram.* *Ishaq na gaida Ahalin Masoyansa gabad'aya,yace na Fada muku. ya ji duk zagin sa da kuke yi groups groups,Har da masu sauya masa suna wai Isiya,Yace kwa yi ku gama shi da Fa'iza mutu ka raba takalmin kaza.* *JANAFTY NA GAIDA MASOYANTA MASU AIKO MIN DA SAKO GA FA'IZA DUK NA ISAR DA SAKON KU,TAJI KUMA TACE TA D'AUKA IN SHA ALLAHU ZATA MIKE TA TAIMAKI KANTA* Ranar da akayi addu'ar bakwai da Daddare,aka taramu saboda washegari zamu watse. kowacce zata koma gidan mijinta,Cikin taron har da Megidan Tamadina da abokan zamanta. sai manyan ya'yan gidan maza,sai mu sai Goggo da Baba Ati kamar kaka take wajen Tamadina ita kad'ai ta rage acikin dangin mahaifinsu da na mahaifiya tunda daman auran zumunci ne tsakanin iyayan nasu.. Bayan bude taro da addu'a da yi ma Mamaciyar addu'a sai d'an nasiha garemu na hakuri da rayuwa,duk yadda tazo ma bawa sai kuma aka gangarowa mgana kan abunda ta bari na magada.mu kenan to da yake bata bar wani abu ba,sai yan kayanta da gado da Sauran tarkace nan take kuma mukace mun yafe a raba ma bakuta,suka shiga saka mana albarka Megidan su ya ce Tamadina tun iya zaman da yayi da ita, bata taba sab'a mai da gangan ba,saboda haka ya yafe mata duniya da Lahira,haka Sauran abokan zamanta suke ta fad'in alherinta suna fadi'n bata yi musu komai ba mace mai kirki da son zaman lafiya,Daga karshe Yaya mariya ta muskuta tana kallo Goggo Lokaci d'aya tana fadin"Goggo ya mganar bashi.shin ko sun san ana binta a bashi Saboda a biya a sauke mata nauyi..? Maman isuhu ta kad'a baki tun kafin Goggo tace wani abu tace'"Allah ya jikan Tamadina ba mace bace mai cin bashi ba,ga yara nan duk sai su tsallakemu su kawo mata ajiyan kudadensu,wlh yadda suka bata haka suke karb'an su ko chanzasu batayi.bata taba cin bashi ba,macece mai godiyar Allah da Wadatar zucci" Gabad'ayan mu dad'in wannan yabon mukaji,har sai da hakan ya nuna a saman fuskar mu,an tashi taron cike godiya da fatan Allah ya jikan Tamadina bayan Goggo ta sanar da Mutan gidan gobe zamu koma gidajenmu suka nuna alhininsu. Bayan mutan gidan sun fice suka bar mu, mu kadai Ni ina gefe nayi tagumi bana mgana Amir ne kadai bai yi barci ba yana jikin Hafsatu,Yaya mariya ce da Yaya Asiya ke ta zencen su da Goggo da Baba Ati acikin Hiran ne Yaya Asiya tace"Baba Ati wai har yanzu ba'a samu labarin inda Dan'uwan Tamadina yake ba..? Baba Ati ta sauke Numfashi kafin tace"Ke dai bari Asiya wlh ba'a samu ba.Kwanaki har chan karayen naje da muka kai yar gidan mallam Akilu aure chan. aka tabbatar min sun tashi sun koma cikin garin kano hannun wani Dan'uwan ita Zuwairan" Yaya mariya tace"kuma babu lambar waya Baba Ati..? Ta jinjina kai kafin tace"Gaskiya babu..Ai tun lokacin zamanta a korafi batayi dogon Huld'a da kowa ba Zaman nasu ma da mahaifiyar Tamadina kakar ku kenan ba dadi gaskiya har da shi Mallam din saboda bata so auran ba,mahaifinta ya had'a abun akwai wanda take so shiyasa sanda aka kawota batayi huld'a da kowa ba,ko Haihuwar Usman din Rabo ne kawai da ya rantse yasa aka samar dashi. Sai kuma mallam din yazo ya rasu.to bayan ta fita Takaba,Danginta suka zo tafiya da ita.sai ta nuna zata tafi dashi to rayuwar nan ba wanda ya damu da rikon D'an da ba nasa ba, saboda ganin Nauyi ne in ma ta barsa anan d'in shiyasa ba Gaddama akace zata iya tafiya da shi Har ga Allah na zata zata rika kawosa ko don yar'uwansa da suka Had'a uba sai kuma gashi Tunda ta saka kafa ta bar Karofi yau shekaru sama da Arba'in da Doriya bata Dawo ba.sannan shima Usman din bai nemi Dangim mahaifinsa ba har yau din nan kuwa" Ba kuma wanda yasan inda suke ahalin yanzu" Gabad'ayan mu muka sauke Numfashi Yaya Asiya tace"To Allah yasa yana raye" Yaya mariya tace"In sha Allahu ma yana Raye kuma in dai da rai da rabo watarana zamu had'u da shi" Muka amsa gabadayan mu da Allah yasa Goggo ta gyara zama tana fadin"Duk inda yake in dai jinin ku ne zai nemeku jini ai ba karya ba ne". Muka jinjina mata kai alamun gamsuwa ni ko araina sai na samu kaina da addu'an Allah yasa yana raye domin shi kad'ai ne shakikin Tamadina anan duniya mu kuma kawun mu Namiji kwara d'aya tak da yau zamu bugi kirji muce muna da shi acikin raina ina addu'an in dai yana raye Allah ya bayyana sa da gaggawa. Washegari da shirin