← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 175

Sashe 62

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mace ta mike ta nema to zata samu da yardan Allah,Sannan sun horemu da mu gyara kanmu mu zama masu tsafta da kwalliya da ado saboda kada mu zama Borori a gidan mazajen mu, ni dai ban bi ta kan wannan mganar ba saboda da mata masu kyau da nasaba ake yi ba irin mu da muka ke da nakasu a komaii ba, abu daya na sani wannan wajen da nazo ya kara Budemin ido akan rayuwa na Fahimci harkan nema ba bambamci mai kyau ko mara kyau in ka iya kawai ka Huta. sai biyu na rana aka tashi Taron Haka Badariya da Raliya suka rikamin Gayya gayyan kawayen su muna gaisawa,Badariya ko bata gajiya da Fadin matar yaya na ne fa Sai naji wani abu ya soki raina ko yayan nata bai taba nunani haka acikin mutane kamar ta ba, shiyasa nake kaunar Badariya kwatankwancin yadda take kaunata. Nayi sallama da matan da muka saba dasu yayin koyan abubuwan da muka koya,Ban samu ganin Hajiyar su Raliya ba suna cikin mutane sai nace Badariya ta bari ta rakani har gida nayi mata godiya. Ranar saboda farinciki ina komawa gida na tasa kudin nan a gabana ko Bude su ban yi ba ina ta ma Allah kirari da Hamdala,Yara suna Dawowa makaranta na rika daga su sama ina Juyi afalo fad'i nake yi"Umma tayi nasara ya'yan Umma..nayi nasara" Sai suma suka rika murna suna tsalle Har da Amir ma kamasu na Rumgume hawaye suka gocemin komai na zama a duniya ya'ya ne karfina da ba domin su da ban san kuma ya zan yi ba. Na shiga gidan sa'adatu washegari nayi mata godiya kwana uku tsskani Badariya tazo mukaje gidan su Raliya chan kusa da anguwan su Anty mahma ce nayi mata godiya tana yaba'min har tace Raliya ta kawo mata alala yayi dadi suna bada girke girken Suna ko Birthday, ko biki in sha Allahu Zata saka arika nema na nace nagode sannan tace nayi shawara da mijina ko yan'uwa na samu wani abun sana'a na siya da kudin hannuna wanda zai taimake ni kada na kashe su a banza nace mata in sha Allahu,muka yi mata sallama ta bani sabulai da Turare kamshi da kudi tace na siya ma Ahmad sweet muka fito ina ta yaba kirkin matar a hanya nace Badariya in ta na da kudi a waya ta kira mun Goggo tace tana da shi,ta ko daga waya ta kirata bayan ta Dauka ta ma zata Hafsat take nema sai tace mata tana bayi Bayan sun gaisa,Sai Badariya tace Fa'iza ke son mgana da ita. Yadda Goggo ta jini cikin farinciki yasa ina cewa ina son ganinta tace"Zan zo in sha Allahu gobe daman kamar kin san cikin satin nan nace zan leko na dubaki,najiki cikin farinciki fa:i daga gani wani babban albishir ne ko Ishaq ne ya biya miki Umra".? Bansan Lokacin da na kyalkyace da Dariya ba,Itama nasan zolayata take yi.muka rabu akan sai tazo, daganan Badariya ta nufi gida nima na Dawo gida. Kwana Biyu tsakani sai ga Goggo Ya Isa ya kawota da Safe bayan mun gaisa na basu ruwa na Dauko kudin da Kyautar da aka bani da Takardan shedan abunda muka koya, na sauke gabanta lokaci d'aya na kora mata jawabin komai bakina har kunne Goggo ta Dauki kudin ta farke ta Fiddo su sabbin yan Dubu Dubu ta nuna ma Isa tana fadin"Isa kaga Bud'i daga Allah ko..?. Yaya isa ya karba ya gani duka kayan ya jinjina kai kafin yace"Lalle Fa'iza na tayaki murna dakyau" Goggo tace"Duka kyauta Fa"iza..? Na gyada kai ina Mirmishi Goggo tace"Masha Allah..Allah ya saka musu da alheri Allah ya biya su kudin nan sunzo a daidai daman mun yi mgana da Sauran yan'uwanki nace su had'a miki kudi wanda zaki rike ki fara wata sana'ar zama haka bazai yuyu ba,sai kuma muka ga abun alheri ai shikenan ma fad'uwa tazo daidai da zama kenan" Goggo tace na ijiye kud'in zata koma in na chan sun hadu zata sake dawowa,na tambayi Goggo dame zan fara na sana'a? Da sauri Yaya Isa yace"Ki fara da sai da zobo da Kunun aya, da ruwa tunda kin koya kuma kin iya sauran sana'o'in ko daga baya sai ki fara bazai gagara ba" Nima na yarda da shawaran sa haka ma Goggo sun tafi da niyar goggo zata kawo min kudin in su hada na bangaran su. sai na had'a dashi Tare da Yaya Isa zasu kara dawowa.sai ayi shawaran Fridge din da za'a siya mai kyau, wanda zan fara sana'ar dashi. *TASTED & TRUSTED* *GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*. *AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*. *ABIN BIRGEWA DA WANNAN SAIWAR ZAKI YI AMFANI DA ITA SAMA DA SAU DAYA.* *AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*. *SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.* *DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*. *SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?* *TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU* *08032773332* *DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*.. *Janafty* *KANA NAKA..!* *Wattpad:JamilaUmar315* *Mallakar:Janafty* *Arewabook:Jamilaumarjanafty* *Madallah da gidajen Sada zumuntar dake cike da mutane masu karamci,Naji dad'i sosai ina ganin sharhin ku Janafty tace Son so.* *JANAF NOVELLA.* *SURRAYYA DEE FANS.* *KANA NAKA COMMENTS SECTION.* *SABO DA KAZA COMMENTS SECTION.* *TAKORITES.* *JANAFTY'S.* *JANAFTY GIVEAWAY ROOM.* *ZAUREN KHADIJA CANDY.* *KITTY NOVELS.* *BENEFICIAL WRITERS.* *FEEDHOM NOVELLA.* *MY WATTPADIAN PIPU,FA'IZA TACE SANNUKU DA KOKARI.* *Kuna da yawa baki ma bazai kirga adadin ku ba,ammh Fa'iza taji kuma ta gani,tace na fada muku ana kyawun tare.* *Tagode kwarai Allah ya bar zumunci da kauna* Ranar da Goggo suka zo suna tafiya,da yammah sai ga Yaya Ishaq ya dawo,wanda rabon sa da garin tun zuwan da yayi muka yi sa'in sa kan Fita, gashi har mun gama.kimanin wata uku kenan baya nan, ammh a haka har yana da kwanjin son ya zaunar dani a gida, sannan yana da bakin fad'in mgana kan ya'yan sa. ya'yan da in ya saka kafa ya tafi mantawa yake yi da su, ba domin Allah da Dubaran mu na mata ba,da Tuni wata mganan ake yi ba wannan ba. A she tare da zainab suka zo ban sani ba,Sai bayan ya fita ya dawo da Daddare yaran suka nufesa suna murnan ganinsa ni bai min mgana ba ko a d'azun da ya shigo na gaishe shi bai amsani ba sai dai ya kalleni ya kauda kansa, sai dawowar da ya sake yi ne bayan ya raba ma yara tsaraban Sweet din da yazo musu da shi, ya fito yana fad'amin na shirya yanzu ni da yara zamu gidan Mama na gaida Zainab tayi rashin lafiya an yi mata aiki an cire mata tsakuwar ciki, da kamar zan ce bazani ba. sai kuma na fasa ban yi mgana ba yaran suna ta murna ni kuma sai na Had'e rai na ko Kyallin Fara'a ta bai gani ba. bayan sallar isha'i yazo ya kwashemu sai gidan Mama. Naga abun mamaki Mama haka take rawan jiki akan Zainab da Farhan kamar zata kwanta mata,afalon Mama muka sameta an kara mata filo ta ma fa warke,ammh Mama ji da ita take yi shiyasa taki bari ta sauka a gidan saboda acewarta na fara halin gantali bazan kula da ita ba sosai gata ba ta da lafiya mun zo ba Dadewa sai ga Anty Binta ta iso itama dai kamar Maman kamar zasu maida Zainab ciki ni dai Farhan na dauka ina mamakin girmansa har ya fara Tafiya fari da shi Dumur mur kamar yaron Turawa ko da yake meye maraban sa da Turawan..?sai bangalamin Dariya yake su Anum suna mai wasa yaana kara sakin Dariyan su na yara. Mun gaisa da Zainab nayi mata sannu ta amsa min ina d'an nesa da ita ne bayan mun gaisa sai na sauya wajen zama ina rike da Farhan a hannuna Anum tazo ta rikemun hannu tana fadin"Umma Anty tace kizo" Sai na Dago ina kallon Zainab sai ta yafito ni da Hannu da zan tashi sai Farhan ya sauka kasa yabi Anum da ta mai chakulkuli ta gudu ,gefenta na samu na zauna ashe Mama da Anty Binta suna kallon mu bansani ba. Gaisuwa take so tayi min bayan ta muskuta daga zaunen da take ta kalleni tana fadin"Kwanaki Honey yake fadamin maman ki ta rasu ko..? Sai na jinjina mata kai cikin Tausayawa tace"Ayya sory for d lost..Allah yajikanta da gafara" Da karfin gwiwa na amsa mata da Ameen,ita ta cigaba da ja na da Hira ni sai dai nayi yaken Dariya sai korafin take yi ban taba zuwa Abuja ba, ammh ita tazo ta sauka wajena yafi a kirga ina Dariya nace"Megidan ne bai taba min tayin zuwa ba" Cikin mamaki tace"Kai.!Ni kuma Honey ce min yayi kece baki son zuwa fa" ban yi mamakin mganarta ba,sai nayi Saurin cewa"Na bari sai kin haifa ma su Anum kani tukunna, Farhan ya girma yana bukatar kani ko k'anwa" Sai ta zabura Lokaci d'aya tana Fadin"Aa bazan iya ba maman Amir ai ko ke naga kokarin ki da'yan ma is ok" Ni dai ina ta Dariyan mganarta a raina nasan zasu kwashi yan kallo da Yaya ishaq shi da mafarkin sa kenan auran mace mai kyau da samun ya'yan Turawa,ga shi ya samu sai kuma ya fara ganin mike ai bazata sabu ba,Anty Binta da Mama kamar su mutu da bakinciki ba so su Zainab din ta sakarmin ba sun so yadda suke min wulakanci itama ta wulakantani sai Allah ya fisu. Ammh duk da haka basu kyaleni ba, su dai in basu tozartani ba basa jin Dad'i a gaban Ishaq din da Jamal da yace cikin satin nan ya dawo Badariya ce kad'ai bata nan tana gidan Anty mahma,Allah yasa yaran suna chan suna wasa hankalin su baya kanmu Mama ta kalleni cikin yanayin kaskancinta gareni tace"Ke kuma wani gantalin kike zuwa kwanaki Binta tayi ta zuwa bakya nan..? Sai na maida kaina kasa na kasa mgana Domin nayi alkwarin bazan ce mata komai ba.. Anty Binta ne tace"Ai bazata fada miki ba ta fara zama gagararriya.Shi kan Shi Ishaq din ta fara fin
Chapter 62 · 0% Book details