← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 159 OF 175

Sashe 159

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ammh Yanayin yadda granny ta rikice ne kuna ga shi Lokacin an gano tana da matslan koda,saboda ya faranta mata yasa ya amince ashe auran ba mai dadewa ba ne,A chan Benue duka aka yi shagalin bikin su daganan suka wuce Edo gidansa dake chan duka duka Sati uku ne yana wajen aiki ta kunna gas ya tashi da ita duka gidan ya kone ko Tsinke ba'a Fitar ba gawarta ma duk ta kone sai k'ashii. Bazai ce bai shiga damuwa ba. tunda Tauhida na son shi,shi kuma mutum ne daya san Darajan dan adam barin ma mace,sai yake biye mata kuma dai bai yi wasa ba ya haikemusu yar yarinya yana ma tsaka da moran auren ne ta rasu to shiyasa ya shiga Damuwa kuma dalilin haka ne aure ya fita ransa,Lokacin da za'a cire ma hajiya Kudirat koda a yi mata dashen na siya da akayi har rigima ta tada akan sai Tosin yayi aure yako ce gaskiya sai dai in yanzu zata karisa mutuwa ammh matukar ko aurensa take jira ba yanzu ba,Dole ta shafamai Lafiya. Lokacin da yaje ma da Maa da papa da mganar Fa'iza duka fatan alheri suka yi masa suna jin dadin Tosin zai kara wani auren,basu zata abun zai zama cikin gaggawa ba shiyasa achan Benue ba wanda yaji sai labarin auran sukaji Daga sama Dayake mutane ne masu Fahinta paapa na musu bayani suka gane sukace in za'a tare nan benue zai kawota ayi shagalin al'ada. Farinciki ya cika su kayafatu Shiyasa suka amshi lambar Fa'iza suna kiranta Domin duk abunda Brother Tosin yake so suma a wajen su abun so ne da Girmamashi. Gidan Papa dankarare ne yana nan a Gwarinpa,Shi ma kuma Engr yana da Dankareren gidan a Apo dake garin Abuja sannan yana da wani Edo bayan gobara ya bata wanchan sai ya Saida ya siya wani a anguwan Benin City,a garin Benue ma suna da gida inda suke sauka inda sun zo kato mai bangarori da dama. kaf ahalin su ba alfahari ba,babu talaka suna da kudi suna da ilimi sannan suna kasuwanci. Suna kuma da kowani yare acikin su ba kyama da tamgwama,har balarabiya Kanin papa ya auro daga sudan,wani kawun su ma na auran baturiya,acikin yaran su matasa irin su Tosin akwai wanda ya auro Bafullatana acikin Ruggar jigawa. shiyasa nace suna da hausawan suna kuma da turawa da larabawa da kuma Yarbawan, shiyasa basa ka ma da ya'yan su sun fita daman kamar ba su hada jini da yarbawa ba. Ammh ba su bar gida ba,yara da manya sun yi kokarin koya musu yaren su saboda duk inda suka shiga a gane su ko ba ta kammani ba. ******* Na dauka yara na za su yi rigima ko kuma zasu raunana kamar yadda na zata a farko sai dai kuma Alhamdulillah da sukaji bazan dawo ba basu yi rigima ba,Ahmad ne kadai yayi kuka shima din Amir da Anum sun lallashe sa,Hatta Anum bata yi kuka ba inaga Amir me ya yi mata mgana da suka kirani ta wayar Jamal Anum kamar Babba sai ce min tayi"Umma Yaya Amir yace sabon Babanmu shima mai kirki ne yace zai rika kawo ki kina ganin mu, muma zamu rika zuwa muna ganin ki" Mirmishi kawai nayi cikin jin dadi kafin nace"In sha Allahu. Anum ki kula da kanki sannan ki kula da sauran kannen ki Karatun Qur'ani da azkar salla akan Lokaci Anum ban da rashin,jin mgana komai Antyn ku ta sakaki kiyi kin ji ko..? Ta amsa min da Toh Umma sannan muka rabu sai hankalina ya kwanta,da jin yarana suna lafiya,Sai dai ance shi Ishaq din bashi da lafiya har da su kwanciya a gadon asibiti, Abakin yaran na fara ji sannan da muka yi waya da Badariya take kara fada'min jiki yaki dadi. Likitoci sun ce jininsa ne ya hau da kuma Damuwa a raina nace"Dakyau! Shi sai yanzu ya samu nashi hawan jini..?kafin shi ni ya fara sakama hawan jinin" Ban fad'a a fili ba saboda ina jin nauyin Badariya har ga Allah ban ji tausayin shi ba,Itama matsaloli duk sun sha mata kai uwar mijin ta kara matsa lamba tunda bata samu ciki ba,tana mganar sai Yusuf ya kara aure,Kullum Badariya ta kirani ko tana kuka ko tana cikin damuwa,Ni ce ma ke tausanta da Hakuri tunda mijinta na sonta kuma yana kaunarta kawai matsalan uwarsa ne da matarsa. Ni dai ba ni da matsalan komai a rayuwata ko da yaushe muna makale a waya ni da Engr mun kara wata irin shakuwa kamar mun shekara da Haduwa,tunda yace kada na sake yin wani abu ban kara ba iyaka dai ina Taya Goggo dafa zobo tunda ita na barma sana'an tun tafiyata Kaduna,Aikin Dambun nama su jummala na barmawa ko an kawo sai dai nace akai musu hatta da Hadin Turaruka sai dai in An matsamin ni zan yi tuni na samu Hutu nayi kiba nayi haske kamar bani ba. Ina cin mai kyau ina shan mai kyau,kuma ina shafa mai kyau tunda ni da kaina nayi ma kaina fada ina Shafa mayuka masu tsada saboda gyaran jiki. mun yi mgana da shi na kayan lefe yace in ya dawo kudin kawai zai bani na siya abunda nake so mganar gida kuma a Abuja zamu zauna bayan mun Dawo daga benue sannan yana Tashi komawa wajen aiki Edo state kafarsa kafata ln nace to tosin ranka ya Dade sai shi kuma yace yauwa yar matata Bolawatifenisola(Tife) sunan da ya samu kenan da yarbanci ni sai dai nayi ta dariya na ma saba har amsawa ma nake domin daya kirani ina Dauka zai ce"yar matata Tife kina lafiya..? Sai nayi mirmishi in ce"Ina lafiya mijina Tosin" Rayuwa muke gudanwar cikin aminta da juna ba gundura ba kosawa,Sannan in nayi abu baya so kai tsaye zai ce min"Gaskiya Faa'izaa ba na son abu kaza..kaza nake so" Shi dan Afadi mgana ce ko yaya zaka Dauka shikenan shidai ya fad'amaka iya gaskiyansa,Mutum ne free da bai da kwana kwana acikin lamarinsa kuma in ya fad'i mgana hakan take daga karkashin zuciyarsa. Labarin aure na da Engr har ya kai kunnen Hajiyar Dala ba kira tayi ba har Karofi tazo,ta same mu ni da Goggo tana ta kananun mganganu tun suna daki ita da goggo da ta fito zata tafi ina falo ina yanken kumba ta kalleni sama da kasa kafin tace"Yanzu ke Faa'iza ki ka k'i dan'uwanki. saboda Bayarbe ko..? Mganarta tamin ciwo sai dai ban tanka ba kuma kaina na kasa ban dago ba sai ta tabe baki kafin tace"Ko da yake an ce yana da kudi masu gidan rana baza'a damu da Yarensa ba. Ammh wannan abun kam ba tsari ki ki' bahaushe dan'uwan ki ki auri bayarbe asalin yarbawan ma na garin Benue" Na kasa juran wannan cin zarafin nata Goggo ce ke fadin"Fatan alheri zaki yi mata kuma kada ki manta wani baya auran matar wani" Kamar an goggo ta watsa mata ruwan zafi haka ta yarfa hannu tana fadin"Wannan karatun ki ne .Ammh ni ba kudi ba ko duniya ya tara in dai bayarbe ne bazan bashi auran y'ta ba. ai gwara banufe da bayarbe." Dagowa nayi ina kallon Hajiyar Dala kafin nace"Shi Bayarben ba musulmi ba ne..? Na fada idanuwana suna kallon nata kawai sai tace"Musuluncin su bai cika cika Daidai ba. sunan dai suna musulmai ne" Nima yadda bataji kunyar gayamin mgana ba nima ban ji ba sai kawai na mike ina fad'in"Kamar yadda a muma Hausawan ana samun b'ata garin addinin musulunci da wad'anda basu cika daidai ba da kuma wadanda suka cika shi daidai suma kamar hakane,Daya muke da su bamu da bambamci musulmai ne su kamar yadda muke musulmai masu imani kuma shi Addinin Ubangiji ba ruwansa da bambamcin yare duk Daya muke a wajensa bai bambamta ba sai wanda yafi jin tsoronsa, ya fi so kuma ban ga Nafsin ko aya da Hadisin da yace kada mu auri wani yare sai namu ba. In kuma da Aya ko hadisin da ya Haramta aurena da Engr ki fada'min Goggo kila su Abba sun samu makuwa ammh yanzu in kika Tunasar damu sai kila mu gyara kuskuran mu? Daga ita har Goggon sun yi mamakin kalamai na ita ko kasa mgana tayi saboda bata da abun cewar ganin haka yasa na kakkabe jikina na wuce daki ai sai ta fara tafa hannu tana fadin"Kina gani ko..?ni yarinyar nan zata yi ma rashin kunyar don na fadi gaskiyata.? Ni dai naji Goggo da ke biye mata tana bata hakuri ko kara sauraran su ban yi ba araina nace ai na bar kara yin shuru a rika raina min wayau ana Dannen min hakki shi bahaushen da na aura dan'uwan nawa me ya tsinanimin..?ban da bakin ciki da takaici, Allah na tuba da wani Bahaushen ai gwara wasu yaren sun fi sanin Darajan mata da sanin amfanin su. Ba irin wasu mazan mu na Hausawa ba. da suka maida mata jakuna ababen biyan bukata masu cikin haihuwa,da wahalhalun duniya Allah dai ya sa mu dace a kowani yare akwai nagari akwai na banza sai fatan mu dace da had'uwa da na garin. ***** Ba iya ni kadai ba hatta Abba,Engr ya fad'amasa da zarar ya dawo zan tare sai Abba ya kirani a waya akan nazo yana son mgana dani,daman kuma ina son zuwa,tsaikon ma da na samu Anty nasara ne suka dawo sun yi tafiya zuwa kasar Ghana inda dangin mijinta suke wajen watanta uku duk bata nan ma akayi aurena dayake kuma na tayata gyara gida da sauran su. itama da taji abunda ya faru tamin murna balle da taga yadda bini bini muna manne da Tosin di'na a waya yana min hira ina Dariya sai ta tsinke da lamarin balle kuma wajen kwana uku nayi a gidanta yana ta magiyan kada nayi aiki duk nagaji so yake kafin ya ganni na zama Tife, din gaske ina jin haka na mika ma Anty nasara wayar suka gaisa kai tsaye yace"Gaskiya Anty ki yi hakuri anemi wacce zatayi aikin zan biya. ke kinga ya kyautu ango na wata duniya yana kuma son in ya dawo yaga amaryansa tayi bulbul tayi kyau sai kuma ya ganta duk a jime..? A yankwane..? Anty Nasara na dariya tace"Ina fa
Chapter 159 · 0% Book details