← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 175

Sashe 82

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ni nace" Gefe ya koma yana numfarfashi Kafin yace"Bazan dake ki ba ammh bazan fasa fad'a muku wannan ba gaskiya muka taka ba.Ta yaya wannan abun zai yuyu Mama duk bayan fa Sati Biyu ina naga kudin motar..? Bude bakin Mama sai cewa tayi"Ba ga matarka nan na sana'a ba. tana da kudi sai ta rika baka Lokacin da kake da shi taci gajiyanka yanzu sai ta rama ma kura aniyarta" Ina duke ne sai da na dago ina kallon mama tako zabgmin harara tana fadin"Munafuka ta saka shegen kurman kunnuwanta tana ji tana Dariya" Sai na maida kaina kasa na cigaba da aikin Gabana shiko a fusace yace"Sai kawai saboda ina jani talau saboda zuwa na ganta sai na rika karban kudin mota wajen fa'iza wannan wani irin mutuwar zuciya ce?Haba Mama ki ma bar wannan mganar bazai yuyu ba wlh na jawo ma kaina bansan haka abun yake ba" Yafada cikin kosawa Mama tace"Da auran Zainab din ka jawo ma kanka..?kada ka manta sun maka komai..? A fusace ya katse Mama da fadin"Basu min komai ba Mama don Allah ki Daina fad'in haka me suka min.?da girma na ya ganni aikina Bashi ya nemamin ba,Auran yarsa da nayi nawa ya yafe min komai sai nayi Mama Dawainiyarta da yake mgana yaushe ya farayi..?ko da take aiki duk watan duniya 100+ nake tura mata nata da na Hidiman yara in adalci zan yi kudin zasu isheni..?nawa nake turo miki ke da Fa'iza da Dawaniyar yara sai kuma don yanzu Kaddara ta hau ni sai afini nuna iko Kan matata da ya'yana wannan wani irin kaddararran aure ne..? Ya karishe fad'a kirjinsa na Dagawa alamun bacin rai ganin ya birkice yasa Mama ta fara lallabasa tana fadin"Taho mu shiga ciki" Kin shiga yayi ya cigaba da fadin"Meyasa kuna ganin gaskiya bazaku bi bayanta ba.?In adalci zai yi bazai min uzuri ba..?ko bai san bani da aiki ba ne yanzu zaune nake nima lalurorina Dauke min su ake yi bai taba Duba Lokacin da nake wata biyu har uku a Abuja ya taba ko sau d'aya ya yi min fad'a cewa na rika zuwa gida akai akai ina da wata matar da ya'ya..?bai taba ba yana jin dadin haka sai yanzu don kaddara ta fad'amin na rasa aikina sai yace Dole duk bayan sati biyu sai naje na Duba yarsa..?bazan iya ba Mama wlh bazan iya ba gwara na zauna anan ko banza ina ganin gilmawar ya'yana da mahaifiyata tare da Matata,achan kuwa ban ma ganta ba yaran kuma basa yini a gidan ni kad'ai kamar maye ina musu gadin gida.wlh ban taba jin abunda nake ma Fa'iza Laifi ba ne sai yau kuma na Tabbata Hakkinta ne ya fara Bibiyata, na Danne mata tarin hakkokinta daya rataya a wuyana, ko da sau daya ban taba duba hakan ba nasani akwai hakkinta dake Bibiyata na sani har da Hakkin Fa'iza Mama" Ya karishe fad'a kamar zai yi kuka ban taba ganinsa cikin rauni haka ba inaji ajikina kallona yake yi ni kuma sai naki Dagowa sai ma na mike na Sauke tukunyar zobon na shige Daki Hawaye suna cika kwarmin idona. Rana ta farko da Yaya Ishaq ya taba Furta ya zalunceni ashe yana sane da abunda yake aikatawa..? Maganganun sa ya sanyaya ma su Mama jiki shi dai ina ji ya shuru takalmansa ya fice daga gidan, su mama kuma suka shige Daki jiki ba kwari. Ranar gidan haka ya yini ba walwala nice ma na dinga zirga zirgan girki da Hada zobo har na gama abincin na zuba ma su mama na sakamai na kai Dakinsa bai shigo ba,yara suka Dawo makaranta kusan Lokaci da'ya suka shigo da Hafsah daman aiki aka basu taje kaiwa sai kuma na fara Damuwa da rashinsa suna ta tambayan ina Daada sun leka baya dakin mama haka ma baya Dakinsa sai nace musu ya fita. Wasa wasa Yaya Ishaq bai shigo gidan nan ba sai Dare,kafafunsa Futufutu daga gani tafiyar kasa ya sha abunda yasa ya warware da ya dawo Jamal ya iske ya dawo shiyasa ya saki ransa. Ruwan wanka ma Amir ya aiko yace wai Daada yace don Allah Umma ki saka mai ruwan wanka. Sai ya bani Tausayi na tashi na saka mai na kai mai har Tiolet din dakinsa na aika Amir ya kirasa,sai da na baro ya shiga wankan nazo na gyara Dakin da Matarsa ta gama bata sa ammh bata gyara ba,araina in naji kamar tausayinsa zai yi min tasiri a raina,sai nayi Saurin na kauce ma haka sai wata zuciyar tace saboda su Amir bazan bar Babansu a wulakance ba. Koda ya fito dakin Tsab ya ganshi ga abincinsa a gefe,sai ya zauna gefen katifarsa yana fadin"Anya ban yi wauta ba..? Ko dai dai bakin Baba ne ya fara kamani..?. Ya tuna Baba yasha fad'amai ya rike Fa'iza Amana in ya wulakantata bai yafe masa ba,sannan yana tausayamasa ranar dazai san amfaninta lokacin kuma tayi masa nisa..' Tuna haka yasa yaji hankalinsa ya tashi bayan fitansa bai san ina ya nufa ba shi dai yasan yayi ta gagari a gari inda yaga masallaci ya tsaya yayi salla yasha a ruwa karon farko da ya tsaya ya fara Tunanin kuskuran da ya tafka a rayuwarsa tun farkon auransa da Fa'iza har zuwa yau..?sai a yau yake jin tabbas zai iya yuyuwa girman hakkin Fa'iza ko Bakin Baba ne sune suka yi Zaren Dabaibayi suka fara taba Rayuwarsa. lalle ko in hakane ya zama Dole ya fara gyara mu'alamansa da Fa'iza ya roketa ta yafe masa kila Furucin Baba zai sake sa. Yana cin abinci hawaye sun cika kwarmin idanuwansa Ya tuna burinsa na auran Zainab da ra'ayinsa sai gashi Burinsa bai masa komai ba, yau ta kawo Fa'izan da ya raina ya hantara ya wukalanta itace komai nasa ta dauki laluransa har da ta kannensa da ta mama daman Laluran ya'yansa tun yana da aikinsa ya bar ma Fa'iza ragamar komai kaicon sa" Cokalin hannunsa ya sauke abincin kamar yana cin mgani kansa ya Dafe dake juyamin cikin Fitan Hayyaci yace"Innalillahi yanzu ya zan yi..?ta wata Hanya zan gyara kuskurena..?duk da tarin laifukana a wajen Fa'iza zata iya duba na ta yafe min..? Tuna haka yasa yaji hawaye masu duni sun zubo masa yayi wauta rud'in duniya da Irin Tarbiyan Mama sun kai shi sun rabo duniya da mutanen cikinta sun saka ya hau keken bera ta kaisa tsakiyar kasuwar nadama ta gungurar da shi me Fa'iza tayi masa da ta chanchanci Tozarcin da ya shafe shekaru yana yi mata..? Da wani ido zai kalleta sannan da wani yare ko harshe zai fara bata Hakuri ta sauraresa..?Anya Lokaci bai kure masa ba kuwa..? *12/07/2023* *8:00pm* *Janafty* [7/12, 10:17 PM] +234 906 320 7298: *KNKB2007* *Ki biya ki karanta cikin salama,Kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta min littafi,Sannan kada ki yad'amin shi,Pay N500 regular ko kuma VIP N1000, Via Jamila Umar Gt bank 0552179550,ban da tsarin kati wannan karon, a turo ta POS, Shaidar biya ta wannan lambar 09069067488* Gabad'aya sai yaji abincin da yake ci ya koma masa mad'aci sai ya ture komai kawai ya koma ya kwanta rigingine,idanuwansa na kallon rufin dakin Lokaci d'aya rabin jikinsa da kafafunsa suna kasa ne daga kasan katifar. tunani ya farayi tunda ga zaman Fa'iza a gidansu har zuwa Had'a auran su da Baba ya yi shi da Hajiyar Karofi abubuwan da suka faru,Zaman auren su da Fa'iza yadda ya tafiyar da ita da kyara hattara tozarci da cin mutumci,sai ya koma yana tambayan kansa me ye illah Fa'iza da ya tsaneta..?ko miye laifinta da yaki karb'anta a matsayin matarsa meyasa bai darajata ya karb'eta ya daidaita sahun ta da matan maza nagari masu takwallali da sanin ya kamata ba.?Sai yaga bata da wani laifi Fa'iza mai Hakuri ce Fa'iza mai biyayya ce Fa'iza mace tagari ce, burin kowani Namijin kwarai zamowarta baka ko mara kyan fuska wani abu ne na bangaran Halitta in da ya jata ajiki ya sota ya tattaleta ya tattali lafiyanta da jikinta sai Fa'iza ta Daukemin Tunanin kowata mace duniya. sai bai yi ba yayi fatali da Umarnin Allah ya toshe kunnensa da furucin Baba a kansa ya zauna da Fa'iza cikin Takura iko,Umarni da Bauta cikin Tozarci da cin mutumci har da wulakanci ya tuna yadda yake barinta da wahala kan cikinsa da kuma ya'yan da shine Silan fitowarsu duniya. Ya tuna yadda ya kwallafa rai wajen ganin ya samu cikar Burinsa na auran mace mai kyau da gata da ilimi da nasaba, bai taba rokan zabin Allah ba shi dai kawai ya auri mace mai wadanan abubuwan sai Kuma ya basa,Domin ya jarraba imaninsa ya kuma sa ta haifa masa ya'ya daidai da Zabinsa sai kuma ya nuna masa ikonsa tunda ya auri zainab ba ga wani abu na armashi a auran shi da ita ba,sai dai eh! ya cika burinsa na auran mace mai kyau da nasaba ammh ba mutumci aciki ba ganin Darajan juna kamar yadda yake ganin yayi ma Fa'iza alfarma haka Zainab da Ahalinta suke ganin sun masa alfarma ya tuna yadda yake yi ma Fa'iza iko akan komai hatta akan ya'yan data Haifa ya tuna ya rabata da Danginta da yan'uwanta duk bata taba dagaa kai ba ,ya mu'amalanci yan'uwanta ta mummunan siga ba ta taba d'aga kanta ba,sai ya tuna Zainab gabadaya rayuwar auran su Mahaifinta ke jan ragamar shi sai abunda yace da shi Zainab take amfani in kuma yace a'a shi din banza bazata taba yin wani abu batare da cewar mahaifinta ba ko sanin ba,kan ya'yansa ma iko yake nuna mai babu shakuwa ta uba da ya'yansa tsakaninsa da su Fadil suna gidan iyayanta sai an ga dama ake kawosu ya gansu ko da yana garin in yayi mgana sai Zainab tace Daddy yace wajen sa zasu zauna gidan ba kowa Zuzu bata nan,A komai shi ke da ta cewa shi ya zama Hoto,yana Tuna sanda yake da kudi Fa'iza bata dora komai daga samunsa ba,ammh yau gashi ya rasa komai na shi biyar ma sha'awa take basa ta zauna da shi ahaka tana kuma Dauke da Laluransa ita wacce yake ganin ta fita ta kuma yi daidai da shi ta gujesa saboda bai dashi,bazata iya baro aikinta tazo
Chapter 82 · 0% Book details