← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 175

Sashe 44

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya zauna gefena yana fadin"Ki daina kuka Fa'iza jikin da sauki sosai.." Na dago idanuwana sharkaf da kuka ina fadin"Wa ke zama da ita..? Kai tsaye yace"Mariya ce..Asiya tazo ta kwana biyu ta koma to bata ma nan aka kai ta asibitin ammh naji Goggo tana fad'amin itama gobe tana Hanya" Jin haka sai na kara saka kuka ina fadin"Allah ya tada kafad'un ki Tamadina Allah ya baki lafiya" Ya amsa min da Ameen yana fadin"Ki tashi ki shirya sai na sauke ki a asibitin" Da sauri na mike jikina yana faman bari har na shiga d'aki na Sunkunci Ahmad dake barci na goya na zura Hijabi sai kamar an tuna min na tuna da su Amir sai jikina yayi sanyi na fito ina Raba ido na neman mafita yanzu in na tafi ina su Amir zasu zauna..? Ko gidan su Sa'adatu zan ce su zauna kafin na dawo..?Sai dai akwai D'awainiya acikin lamarin yara ba d'aya ba,ba kuma biyu ba har guda Hudu ganin yadda jikina ya kara Sanyi ne yasa yace min"Muje ko..? Ya fada Lokaci daya yana mikewa sai yaga kuma ban biyosa ba sai ya juyo yana kallona kafin yayi mgana na taresa da fadin"Ya Isa yara na..Su Amir bansan inda zasu zauna ba, in suka dawo daga makaranta ba" Kai tsaye yace"Su zauna gidan kakaninsu mana" Sai kawai na koma na zauna ina sharan kwallah Lokaci d'aya ina fadin"Ya isa kaje kawai sai gobe da Sassafe zan taho in sha Allahu" Shima kansa nasan mamaki yaji da mganata saboda yadda ya ke kallona sai na sake sadda kaina ina jan majina. Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace"Shikenan ki tabbata goben kin taho kin ji ko..? Yafad'a cikin alamun Tausayawa acikin lamarinsa na gyad'a mai kai sai ya kara kallona yana fadin"Kina da kudin mota ne..? Sai na kasa mgana shi kuma ganin haka sai ya cire dubu uku yan Dubu Sabbi ya bani yace nayi na mota na karb'a ina godiya na mike shi kuma ya wuce da sauri nace"Wani ma asibiti kace..? Bai juyo ba yace"Asibitin general da ke bakin asibiti Dutsenmah" Na gyada kaina ina fadin"Ka gaisheta ka fad'ama Goggo gobe da Safe ina tafe..Allah ya tashi kafad'an Tamadina" Ya amsa da Ameen ya fice bayan ya kare ma falon kallo lokaci da'ya yana girgiza kansa. Komawa nayi na zauna in da na tashi na Rushe da kukan,kukan bakinciki da takaiici ace Tamadina ta kwanta jinya tafi sati ban sani ba to ni a wani bingire zan saka rayuwata ne..? Ahmad da yaji ina kuka shima ya fara Rigimansa na kwantosa na Rumgumesa na cigaba da kuka sai kawai ya rika bi na da kallo. Haka na yini cikin wani yanayi motsi kad'an sai na daga hannuna sama ina fadin"Ya Allah ga baiwarka chan tamadina kafini sanin Halin da take ciki..Allah ka bata lafiya ka tashi kafadarta" Ko abinci da na kan yi ma yara da wuri ranar sai da suna gabda dawowa na dora musu farar taliya nace sa ci da mai da yaji,Domin bani da natsuwar yin wani abincin da zai bani wahala su kansu da suka Dawo sun ganni duk a sanyaye sannan fuskata da Idanuwana sun kumbura hatta Ahmad rigimamme yau bai yi min rigima ba kamar yasan bana cikin yanayi mai dadi. Sun dawo suna murnan an basu resit a makaranta na shedar sun biya kudin makaranta har na Team biyu,Alfarma akayi musu saboda naje wajen sau biyu ina basu hakuri sai wannan lekowar tasa ne yaran suka mai mgana inaga yaje ya biya musu, ko kuma ya tura musu. Ni dai da yake ba wannan ne a gabana ba ko duba Takardan ban yi ba,nace su adana cikin Littafansu. Amir ne mai wayau cikin su shi ne ya tambayeni Umma baki da lafiya ne..? Na kallesa cikin wani yanayi sai na kasa basa amsa,sai da daddare bayan mun idar da sallar Isha'i dukkanmu muna zaune sai na kallesu ina fad'in"Kowanne ku ya d'aga hannu ya ce Allah ka bama tamadina lafiya.." Sai suka tsaya suna kallona Anum ce tace"Umma wace ce? Da sauri nace"Ina wannan da ta taba kawo muku gyad'a da su masara har nace muku mamana ne kakarku.? Suka gyad'amin gabad'ayan da sauri nace"To mahaifiyata ce, bata da lafiya ku yi mata addu'a in dai kuka yi sallah" Fuskarsu ta nuna jimami Amir yace"Allah ya bata lafiya Umma" Na amsa mai da Ameen atare muka daga hannu muka yi addu'a da Fatan Allah ya bama Tamadina lafiya. Saboda tafiyata Dutsenma agobe da wuri nace su kwanta ko karatun Dare basu yi ba na kwana ina Tunanin inda zan kai su Amir su zauna kafin na Dawo na duba na hango ba su da inda yafi gidan Mama dole dai ko naki ko naso chan din zan ce Haruna ya kai su in suka dawo ban dawo ba. Da asuba da na tashi ban koma ba ina gama shirya su na tafiya makaranta na Dafa musu abunda zasu tafi dashi makaranta,Tunda bani da komai sai nayi Tunanin na Dafa wani abu na tafin ma tamadina dashi,Shiyasa da kaina na saka Hijabi na raka su Amir kofar gida muka gaisa da Haruna na fad'amai zai kai su gidan Mama in suka Dawo da yammah ban dawo gida ba,Mahaifiyatace ba lafiya zan je na Dubata ya yi min Fatan Allah ya bata lafiya. Na duka ina kallon yaran kafin nace"Zaku zauna gidan mama kafin na Dawo kun ji ko..? Amir ne ya gyadamin kai Anum ce ta kwabe fuska tana fadin"Umma ki tafi dani"Na shafa kumatunta ina fadin"Zaku je Anum insha Allahu ku dai ku yi ta mata addu'an Allah ya bata lafiya" Da haka na lallabasu suka tafi da Anum ta fara rigiman kayan sawan su ni kuma naga suna da kaya agidan mama bazasu rasa na sawa ba,Suna wucewa na shiga gidan Sa'adatu muka gaisa na gayamata abunda ke faruwa cikin tausayawa tace"Allah sarki wannan da kika kawo min ita muka gaisa ko..? Na gyada mai kai cikin wani yanayi cikin jimami ta yi min fatan Allah ya Tada Kafad'a,na amsa mata Daman Nama nake so na siya sai tace min sai karfe tara mai naman bakin titi yake fitowa, sai na zauna muka cigaba da Hira sama sama Ahmad na bayana yana barci,Taran nayi muka yi sallama Daga gidanta na gangara bakin titi daga cikin Dubu ukun da Yaya Isa ya bani na siya Naman dubu Daya na koma gida na Dora jallop din Shinkafa,da nama daman ina da Cabeji sai nayi amfani da shi kad'an sai da nagama komai,na samu wata Tsohuwar cooler dina na zuba abincin aciki,sannan na je nayi wanka nayi ma Ahmad muka shirya tare,Atamfa ta na saka wacce Yaya Asiya ta dinkamana mu hudu,na Zura Dogon Tsohon Hijabina da yasha ruwa,kan duk ya kod'e da Takalmina duk yaji duniya ya d'aga tun wani Takalmi da Anty Nasara ta taba bani ne, yafi shekara hudu ina moransa don ma ban cika yawan fita ba,ai da yanzu bani da nasawa. Rufe get din nayi da key din gidam,Na rike Dubu biyun da suka yi saura da abincin da na Dafa na shiga nayi ma Sa'adatu sallama sha daya da wani na isa gidan Mama,adaidaita na hau na sallame shi na shiga gidan ba kowa ina ta sallama Ashe Mama na falo tana faman kirga kudi sai dai ta ganni na shigo kamar daga sama hankalinta yayi sama bata ji sallamata ba. Tana ganina kamar taga mutuwarta ta wani zabura sannan ta saka kudin hannunta kasan cafet din datake zaune,Tana wani zare ido tun kafin na kariso ta tareni da fadin"Lafiya ke kuma daga ina yarkace yarkace kamar yar gudun hijira..? Gabanta na Duka ina gaisheta ta amsa a gaggauce tana kara fadin"Lafiya..? Kaina na kasa nace"Dama..dama zan je Dutsemah duba jikin Tamadina ne" Sai Mama ta gyara zama tana fadin"To ashe jikin har yanzu..?ni Goggon taku ta kira ni tace a fad'a miki na sha'afa tafiya ta kamani zuwa Yamai" Ina jinta ban ce komai ba sai ta cigaba da fadin"Allah ya bata lafiya" Na amsa da Ameen shuru dai taga ban tashi ba sai ta fara fad'a tana fadin"Wai ni kam sintirman me kika zo kika min a gabana..? Da Sauri nace"Dama ina so su Amir zasu zo nan su zauna ne in na Dawo da wuri to..inkuma naga jikin nata yayi tsanani zan kwana shine..Shine nace bari nazo na fad'a miki tunda Babansu baya nan" Har na gama Mgana Mama na bina da wani kallon banza sai da na Dire sannan ta karbe da fad'in"Daman ai tunda na ganki nasan banza bata kawo ki..so kike bayan na gama wahala dake na kuma dawo na ya'yanki..?to baki isa ba malama kije ki Dubata la'asar nayi ki kamo Hanya,Gida ba kowa Badariya ta shiga makaranta Jamal baya garin nima yanzu da kika ganni Hajiya Barira nake jira zamu fita ban san da wa kike so su zauna ba..Kuma Allah na gani bazan soke fitata saboda ke ba"Ta karishe fada tana tabe baki daman ai nasan za'a rina sai kawai na mike ina yi mata sallama ta bi kulan Hannuna da kallo kafin tace"Ke ke..Wannan abun fa ina zaki kai shi..? Sai nayi mata kamar ban ji ba kuma na jita naki juyowa ina ji tana fadin"Aikin kenan shiyasa kayan abinci ba sa wata suke karewa ga inda ake kwashewa ana kaiwa ashe " Daganan na jita sauran mganganun nata ban ji ba Domin na fice daga Falon Idanuwana na kawo ruwa naji Nadaaman zuwa ma. Sai dai na fita Hakkinsu daga ita har Yaya Ishaq din. Ni da naso naje tun da Wuri sai gashi sai azahar na isa Karofi chan na fara zuwa saboda ban san d'akin da suke ba,Ina ko zuwa na iske Yaya Isa zai kai su Goggo da matarsa da Anty Nasara Goggo na ganina tace"Ga ma Fa'izan nan ta iso..Sai mu rankaya muma asibitin zamu" Sama sama muka gaisa na shiga Mota sai asibitin General na Bakin asibiti Tamadina na Female ward ne babban Dakin Yaya mariya muka iske a wajenta da Maman isuhu sai matan ya'yan su. Muka gaggaisa da tambayan mai jiki sukace da sauki na Ubangiji. Na kara rud'ewa da naga Tamadina kwance bata motsi numfashinta na sama sama alamun dai tana jin jiki
Chapter 44 · 0% Book details