← Book details Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 136 OF 175

Sashe 136

Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a karatuna ya'yana kuma ina mgana da su bani da wata damuwa. Jummala ta samo min wata yarinya Laure ta na tayata aikin zobon da kunin aya in bana gida,ko kuma aikin su Tarare,na riga mun yi mgana da Abba zan fara kwangilar girke girken sha'ani a gida zai siyamin manyan Tukwane da murahu da Kololi,daman alokacin na kara siyan wata Frezeer guda d'aya ta daina isa ta tuni kuma mata su gane bangaran kayan kamshi da Gyaran jiki tunda ina tallata kasuwancina a makaranta. Sai gidan Goggo ya zama wajen shiga da Fice gefe d'aya kuma ina kokari wajen karatuna ban yarda wani abu ya Daukemin Hankali ba. Sauka nake so nayi na zama Mahaddaciyar Alqur'ani mai girma. *Janafty* [7/27, 7:24 PM] Hauwa Galadima: *KNKB3008* *TASTED & TRUSTED* *GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE, MASU JEGO DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*. *AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*. *ABIN BIRGEWA DA WANNAN SAIWOWINRL ZAKI YI AMFANI DA SU SAMA DA SAU DAYA.* *AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*. *SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.* *DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*. *SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*. *KAYANA NATURAL NE DOMIN SAIWOWI NE DA AKE HAKOSU A DAJIKAN CHADI. BAYAN SAUKAR DA GAMSUWA HAR YAQI SUKE YI DA DRYNESS DA KUMA INFECTIONS.* *AKWAI NA TSUGGUNO DA YAKE HA'DE MACE TA MATSE.* *AKWAI HADADDUN DAKA NA SHA DA MADARA KO NONO WANDA BABU ALGUS*. *SANNAN AKWIA GADALIN MATA NA ASALI, WANDA SHA YANZU NE MAGANIN YANZU DA IKON ALLAH* *DUKKANSU TESTED & TRUSTED NE*. *TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU* *08032773332* *DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*. *NATION WIDE DELIVERY* *Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000.* *09069067488* *BAYAN SHEKARA D'AYA DA WATTANI* *KAROFI* Ko daga tsakar gidan Goggo in ka shigo Dariyata zaka fara jiyowa. saboda yadda nake faman kyalkyata Dariyan ba kakkautawa har ina Dukawa rike ciki na jin ya fara kullewa. Goggo ce ta dago labule ta Leko Dakin Lokaci daya tana Fadin"Ke kuma ke da wa kike ta Dariya haka har waje fa ana jiyoki"? Ina Dariya ido na har ya tara kwallah na Dago ina fadin"Goggo ni da Badariya da Anum ne. ina Dariyan sun je ziyara karnukan sun biyo su uwa da y'a sun ware kafa suna gudu" Na fad'a har ina kara Dukawa ga waya rike a gefen Kunnena na Hagu karamin Tsaki Goggo taja ta sakarmin Labule tana fadin"Shine abun dariya..?Allah ya shirya ki Fa'i" Ina jinta ammh na kasa daina Dariyan da nake yi ina jin Anum na fadin"Umma bafa abun dariya ba ne Anty Badariya har fad'uwa tayi ta gurje Gwiwa" Ina so na bar Dariyan na kasa cikin Dariyan nace"Garin ya kika bar uwar taki a baya..? Cikin sauri tace"Umma ni ban san ta fadi ba ina ta gudu ban juyo ba sai da na kawo kofar gida" Dariyan na cigaba da yi domin ta kasa tsayawa,Badariya ta karbe wayar cikin muryan Tausayi tace"Kai Anty Fa'iza ina fada miki duk na kurje kafa kina Dariyan mugunta..? Ina Danne bakina nace"Waya aike ki..?ai sai da mijinki ya hanaki nima kuma da kika fad'amin sai da nace karki je" Kamar tayi kuka tace"Wlh don Allah naje mata barka ko Anum? Bansan me Anum tace mata ba ganin yadda take mgana kiris tayi kuka yasa na danne dariyata ina Fadin"Hakane ammh dai da kin ji mganarmu da haka bata faru ba,ba sani nayi ba ammh nasan da gangan ta saka a sakar muku karnukan nan" Badariya na ta jinjina kai kafin tace"Tayi ma kanta Anty Fa'iza ni dai Allah yaga niyyata" Jin haka yasa nace"Allah ya baki lada Sannu .Anum ta Dafa miki ruwan zafi ki gasa kafar in taki sai kuje ko Chemist a duba miki. Da haka muka yi sallama ina cin dariyata a raina. Wattani biyar baya muka sha bikin Badariya tare da mijinta Alhaji Yusuf mai kudi ne shaharareen dan kasuwa mai harkan Safaran motoci daga kasashen waje zuwa Nageria,asalinsa Haifaffan Azare ne dake Bauchi uba da uba ammh kasuwanci yasa suna zaune a cikin garin Bauchi sai wasu dangin dake azaren. Ganin Farko soyayyar Badariya ta shige sa mai zafi a Lagos ya ganta yaje ganin motocinsa da suka sauka ta Jirgin ruwa ita kuma ta fito daga kasuwa suka had'u,Yana da mata d'aya ya'yansa Biyar kuma cousin dinsa yake aure,Badariya ta karbi Yusuf ganin yadda yake kaunarta Saboda Allah sai dai kafin auran su an sha Fama Tunda fafur mahaifiyarsa da Danginsa suka ki amincewa da har mganar ta sha ruwa, sai daga baya Babban yayansu da Dangin Mahaifinsa na azare suka zo har Karofi nema ma Yusuf auran Badariya. Shagalin Bikin da komai a katsina aka yi shi Tunda Ishaq ya siya gida ya gyara shi an zuba komai lokacin Bikin aka fara amfani da shi,na daki kirji na nuna ma Duniya ni yayar Amaryace ko da aure na ya kare tsakani na da Ishaq na shiga sha'anin sosai ba Domin kowa ba sai domin Badariya,ba kuma don taimakon da tayimin ba a'a ta kaunace ni saboda Allah,ni na siya mata Fridge,sai tv da Tv Stand sai cafet d'an Italiyan sannan nayi mata Turaran wuta na itace kwallacha da Humra,na kashe mata kudi ban san iyakaba sannan nayi mana Dinki ranar Bikin muka saka ni da ita Kowa ya ganni a wannan Lokacin da rayuwa ta sauyamin Gababadaya ya san ba waccen Fa'izan daya sani ba ce Fa'izan yanzu ta kama kudad'e a hannunta sosai ban sauya ba ina nan a Fa'iza ta y'ar gargajiyata ta. su Nana Fatima har sun gaji da magiyan na rika kwalliya sun kyaleni kayan kwalliya kuwa ko an bani sai dai su Hafsah su mora,bayan Shigata makaranta yanzu haka muna matakin Haddan Izifi Hamsin sauran mu izifi goma mu sauke,Tunda daman nayi sauka haddan ina wani bangaren sai ya kasance kamar tishi nake yi. bangaran islamiya kuwa mun yi nisa tuni mun gama wasu littafan mun Dora wasu,Sana'o'i na na rike sune suka zame min kashin takawana bayan Abba ya kasance bango gareni. Bayan girke girken da nake yi yanzu na suna ko biki ko walima ko wani Taro a biyani ina aikin Dambun nama ko na kaji Dari ne a biyani ladana,ga Dilkar amare da Halawa,ga aikin Turareka na amare da matan aure ga Zobo da kunin aya domin ban daina ba Sai dai bayan ma'aikatana jummala da Laure a kallah yanzu mata masu min aiki ina Biyan su sun yi goma sannan ga almajirai masu Hidimam wanke wanke na manyan tukwanen abinci da kuloli,kaf Karofi ,Dutsemah,katsina kano,kaduna da kewayanta sun san Fa'iza mai Turaren kamshi ko SAFMA,tunda har lokacin ina Buga Sticker kuma ina amfani da ita a Kwallaben Turaruka na. Ina da karfin jari a hannuna wanda Abba ya bani sannan ga Ribata shiyasa kafin Lokaci na sha kwana na mallaki kudad'en da ban san adadin su ba,Ni mutum ce mai kyauta hannayena suna Bude ne sannan ina yawan Sadaka da kyautata ma mutane ko matan da na Dauka ko da yaushe cikin min godiya suke yi na taimake su wasu mazajen su ba sana'ar sai wahala ni ko ba iya albashin ki ba in aka samu babban aiki aka biya da tsoka nima nakan yi musu ihisani. Kuma ban bari hakan ya taba karatuna ba in ba na gida aka kawo aiki duk sun iya jummala da Laure suke jagorantan komai, in na Dawo sai dai na Duba kawai na dan gyara wani waje a ajin Haddamu ni kadai ce babba sauran duka matasan yara ne,Ammh kwakwalwata naja tunda na saka abun a raina gwara ma ajin islamiya tunda ta matan aure ne akwai sa'i'o na da ma wad'anda suka girmeni ana ta gungurawa tare,Duk da ban yi karatun boko ba ammh yanzu ina jin kananun kalmomin Turanci sai dai in turancin yayi tsawo sannan na iya Lissafi ba Dole ma na iya ba Tunda na kama kudi a hannuna. Hatta su Yaya Asiya Abba ya basu manyan jari a hannunsu,sannan mazajen su ma bai barsu haka ba Mijin Yaya Asiya yayi mai hanya yanzu Vice principal aka basa ita kuma mijin Anty mariya aka kara ma kasuwancinsa jari Hafsatu kuwa ta zama yan kaduna wayayyiyar mace mai ilimi da gata sai kace ba ita ba. ita da Karofi sai dai da Hutu ko wani sha'ani. Ba wani abu tsakanina da Ishaq tun abun da ya faru tsakanin mu lokacin da yazo inaga ya Hakura ne,sai dai ina waya da ya'yana ko da yaushe,tun kuma daga Lokacin bamu kara haduwa ba sai a bikin Badariya bai min mgana ba ni kuma sai na gaishesa Darajan zumunci ammh bai amsani ba araina nace kan ka akeji,a sha'anin nan ko Zainab Mama bata rika sakata cikin lamarin bikin kamar ni ba, komai sai tace a yi ma Fa'iza mgana,Hatta da Anty Binta rayuwa ta saka tayi sanyi yanzu mijinta yayi Ritire ba wani arzikin yanzu Halisa kuma kannen miji da yayyinsa sun hanata zaman Lafiya. sau biyu tana samun ciki suna barar mata da shi,Duka sau biyu ga na miji ga na Danginsa igiyar aure saura d'aya kuma yaki ya saki duka Halisa ta rame ta Lalace kamar ba ita ba,Duk kushen Hajiyar Dala da Kallon renin ya'yanta yanzu sun san a inda suke yi,Sun kuma gane muma mun sha kwana Fiye da yadda suka sha barin ma ni shigar alfarma da kaya masu Tsada sai dai su nuna min kwalliya da gayu, yar wayewar nan ma ai muna da ita daidai gwargwardo. Kafin bikin Badariya su Amir sun zo min sun min hutun azumi har salla tare dani suka yi naji dadi matuka,har da su Farhan tunda ko'ina daman tare suke zuwa har yau ban taka kafata Lagos ba har kuma karin girma mijin Anty Fadila ya samu aka had'a walima ban je ba su Ammi sun je tare da su Nana Fatima. har da Hafsah sun kuma Biya sun ga su Amir suka dawo da labarin kyakyawan rayuwar da yaran ke ciki. Mama na tsaye kan su ita da Ishaq zainab kuma ba'a sakata a lissafi Fa'iza ma da suke kira
Chapter 136 · 0% Book details