Sashe 78
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dubu Hudu,kada mutum ya raina ciwo komai kankantarsa,Yara sai dai suka Dawo makaranta suka iske sa rashe rashe ana masa karin ruwa,sai duk jikinsu yayi sanyi sai da nayi ta lallashin su sannan suka saki jiki yasha wahala rana zuwa dare duk ya fada abinci ma,ya kasa ci sai da Anty Binta tazo mai da Ferfesun kayan ciki ya samu ya ci kad'an yace bakinsa D'aci ga zazzabi ga amai da gudaawa. Anty Binta bata neman zaman lafiya sai da tayi korafin wai meyasa ba'a kaisa asibiti ba? Mama tace mugunta ta ta ce ta tashi kuma ina da kudin naki kaisa asibitin,ni bana biye musu sai na nuna ma ban jisu ba Mama fa sai ciwon d'anta ta taba shiga bangarena ita kuma Anty Binta in asibitin banza ne meyasa bata Dauke sa ta kai sa ba..? Wlh na yarda da maganan Hausawa da sukace in kana da abun yi,ba komai ke damunka ba. a baya ne in Mama ko Anty Binta sun min wani abu yake damuna nayi ta kuka yanzu na manta rabo na da kuka akan su,To ayyukan gabana ma sun isheni inaga naga Lokacin sauraransu ko suna yi baya Damuna, kamar irin na riga na zama Jan wuya a lamarin ballatana yanzu da nake yawan samun masu son Turaruka ta bangaran Hajiya sai ayyukana suka yi min yawa. Ashe sun raina kulawar da nake basa balle da suka ga kurajen baki sun fito mai yaba yaba na alamun wucewa Mura, sai Mama ta saka Anty Binta ta kira Zainab na ta fad'amata wai tunda bazan iya kula dashi ba,yana da wata matar zata zo ta kula da shi,Sanda akayi ma bana gidan naje kasuwa da na Dawo Hafsah take fadamin sai nayi mirmishi ban ce komai ba. Ashe ko sun kirata sun zuzuta abun Hankali tashe ta d'au alfarma a wajen aiki ta taso,ita da Fadil Farhan saboda makaranta ina tsaka da Hidiman Zobo na ta shigo,Direba na binta da kayanta A karamar a kwatinta kwata kwata ban yi mamakin ganinta ba, na tsallake komai na tarbeta sai dai Mama bata bari ba,ta janyeta zuwa Dakinta chan ta sauka a fili nace a gayyas. Na koma dakina na cigaba da aikin da nake yi,Chan ba jimawa sai gasu sun shigo ita da Mama,Zainab na rike da Fadil sai alokacin muka gaisa kallo na take yi tana kare ma falon kallo Mama tayi mata Jagora har dakin Yaya Ishaq ni dai ban bisu ba saboda ba wanda ya gayyaceni sun dan jima aciki sannan suka fito sai ta kalleni tana fadin"Maman Amir zobo kike saidawa yanzu? Ina yar dariya nace mata'"Eh wlh muna tabawa ya hanya..?ina Kika baro mana Farhan..? Kai tsaye tace"Yana wajen mommy saboda makaranta" Mama sai jiranta take yi daga waje ganin muna ta mgana yasa ta Dago labule tana fadin"Zainab muje ki yi wanka ki yi sallah sai ki ci abinci" Sai ta amsa mata kafin ta fitan sai da tace min"Ashe Honey haka yayi ta rashin lafiya..? Sai na gyada mata kai ina fadin"Ai yama ji sauki yanzu' Cikin jimami tace"Ayya Allah ya basa lafiya" Na amsa mata da Ameem sannan ta fice zuwa Dakin Mama ni ko sai da na gama zuba zobo na sannan na shirya ma zainab abinci daman da rana Shinkafa da miya nayi mana da Salat har dare saboda na gaJi bazan iya wani girki ba,har dakin Mama na bita da shi har da zobon na zuba mata Bata a falo kila tana ciki Mama sai Hararata take yi ban bi ta kanta ba na sauke abincin hannuna na fice abuna. Sai da na had'a kayan wanke wanke bayan yara sun dawo makaranta ni nace su shiga Dakin Mama su gaida Antynsu suka shiga gabadayansu suka gaisheta daganan bayan sun ci abinci suka shige Dakin babansu Fadil na Hannunsa suna ta wasa Amir ne kadai ke falo yana duba Littafansa na makaranta. Da kaina na shiga zan dauko kololina da wanda na kai ma Mama nata,na iske zainab na zaune tayi wanka ta sauya kaya waya a hannunta tana ta Dannawa sannu da gida tamin na duka ina kwashe kwanukan da suka yi amfani da shi Mama na gefe nasan hira suke yi da na shigo ne Maman ta Dauke mganar ammh saboda salon cin Mutumci sai ta gyara zama tana fadin"Zainab nace ba.." Sai ta Dago tana fadin"Na'am Mama" Mama tace"Daman so nake naji ko zaki d'an kwana biyu kafin ki koma..? Zainab ta yamutsa fuska kafin tace"Anya? hutun kwana biyu suka bani a wajen aiki" Mama ta kalleni ta gefen ido tana fadin"Gaskiya gwara ki tsaya ki kula da shi.ita wannan baya gabanta ta sana'arta take yi tunda ta fara wannan sana'ar nata bata kallon kowa da Daraja kema matarsa ce shiyasa nace Binta ta kiraki kizo ke kila kya kula da shi yadda ya kamata" Sai tayi Dariya batace komai ba ni kuma ina cigaba da Tattara kwanukana ina jinta daman tayi mganar ne saboda naji. Ganin Zainab batayi mgana ba yasa Mama ta cigaba da fadin"Ni dama in kin tashi tafiya zaki tafi dashi chan Abujan,zan fi samun kwanciyar Hankali zamansa anan bai da wani amfani" Na mike kenan Zainab tace"Mama naga Maman Amir fa na kula da shi"sai Mama ta wani yarfa Hannu tana fadin"Wlh bata kula da shi, wannan da kika gani ai muguwa ce ta sosai" Tafad'a Lokaci daya tana nuna ni da baki kamar zan fita na barsu sai na fad'a kamar an min wahayin mganar na Tsaya ina kallon Mama kafin nace"Aiko baki ce ta tsaya ta kula da shi ba tunda tazo, na sakar mata komai Tunda itama matarsa ce, kamar yadda yake da Hakki a kaina itama yana da Hakkin akanta" Daga haka na juya nayi ficewata Mama ta rakani da fadin"babu abunda ta iya yanzu sai rashin kunya har shi ta raina" ni dai bansan ya suka kare ba ina wanke wanke abun na dawomin ni kaina ina mamakin yadda bakina ya bude wani Lokacin na yarda ba shawara ko nuniya ke saka mace tayi baki a gidan mijinta ba Wuya ce mutanen duniya ke chanzata,batare da tama sani ba kamar yadda yake faruwa dani domin ban taba kawowa ma kaina zan iya maida ma Yaya Ishaq mgana ba ko shi ko Anty Binta ba sai ga shi shakkar da nake ji da yanzu wlh bana gani,wani abun ma ina raga musu ne saboda wasu Dalilai. Tunda Mama ta raina kokarina ni ko a raina nace sai na bata mamaki na tsame hannuna a kula da shi ai daman ba hakki na ba ne, ita da bai jingine auranta ba,yafi zama Dolenta ta kula da shi nifa daman taimako ne da Darajan ya'ya sai ta wani Fanni in na Duba zumumci. Sai ana mangariba na gama wanke wanken nan sai lokacin Hafsah da Badariya suka dawo,Amir da su musty sun bi babansu zuwa masallaci daya fara rarrafa d'azu,sannu da gida suka yi min kowacce ta shige inda tafi wayau. Ina komawa Daki daman na Dafa ruwan zafi nayi wanka,Hafsah kuma nace in tayi sallah taci abinci taje makotan mu ta Dauko min ninkan Ayan da dazu yaron gidan ya shigo Siyan zobo na bashi sai ta amsamun na shige Dakina nayi wanka nayi sallah na zauna ina azkar,ina ga sai da sukayi sallar isha'i suka dawo shi Uban Gayyar Dakin Mama ya shige yaran kuma suka dawo Daki Hafsah da ta dawo dauko nikan na saka ta raba sauran abinci nace ta diba ta kai Dakin Mama da yawa Saboda Zainab sauran su ci su da yara. Akace Namiji ya iya munafunci nidai tunda na shiga ban fito ba Hafsah na bari da hada kunin Aya,Ashe da ya gama zamansa Dakin Mama tare da Zainab suka dawo Dakinsa sai suka bar Fadil wajen Mama bakinta washe,Adakin nasa ta kwana ni ban sani ba ko da na tashi da asuba ban lekasa ba ina ma yara shirin tafiya makaranta,muna falo da ni da yaran suna cin abinci sai gata ta fito tana mika sanye da rigar barci Riga da wando masu taushi gashinta kanta ya bazu wata hula ce ta saka ana ganin kanta,sau daya na kalleta ban kara ba ita ta fara gaisheni na amsa ta cikin Sakin Fuska har ga Allah ban ji Haushi ba, to me zai dameni ai ba yau aka fara ba an dade ana haka. Abun karin ma na aika Dakin Mama basu ci ba Zainab ta basu kudi suka siyi kayan tea Badariya tazo kitchen dina ta soya musu kwai, ni ina Dakina Hafsah ke fadamin nace saji da shi dai. Sai da chan rana na shiga na Duba sa yana kwance sun yi kaca kaca da Dakin,daga nesa na tsaya na gaishe shi da jiki ya amsa sai naga yana karemin kallo sai na Tsargu da Sauri na kalli kaina Riga da sikat ne a jikina Atamfar ni na siyeta da kudina na Dinkata sai dai dinkin yayi min Cif a jikina ganin yadda ya kuramin ido ne yasa kawai na juya zan fice da Sauri ya yunkura ya mike yana kiran sunana na Juyo ammh ban karisa gabansa sai yace"Fa'iza kariso mana bana jin dadin yadda kike maida Dakina kamar bakon ki" Sai kalamansa suka bani mamaki kai tsaye nace"ai bakon ne a wajena.." Bai damu ba sai ya dan kalli D'akin yana fadin''Haba Fa'ita kwana biyu ba'a zo an gyaramin Dakin ba. sannan kuma ga kayana duk sun yi Datti wlh ko na sawa bani da shi" Na kura masa ido ina Dariyan sunan da ya kirani wai Fa'i ta abunda ban taba ji ba ko acikin mafarki har da wani lankwasa wuya yake yi na yaudara sai kawai nayi Dariya kafin nace"Ai wannan ba Hurumina ba ne Hurumin Matarka ce ka kirata ta gyara dakin sannan ta kwashe kayan naka ta wanke" Kai tsaye yace"Saboda me sai zeey.?ai ke kika saba yi Fa'iza kada ki bata ladan ki don Allah" Karfin Halinsa ke bani mamaki cikin gajiya da mganar na juya ina fadin"Ba bata lada ba ne, Itama Hakkin ka na kanta ta kula dakai tunda tazo ta amsheni daman ni taimako nayi ba Hurumina ba ne" Har zan fice ya kwalamin kira "Fa'iza..' Sai na juyo ina fadin"Wlh bazan yi ba ka kire