Sashe 90
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bazan yi ma Halisa ba,mamanta uwa daya uba d'aya muke da ita ballatana ba Halina ba ne" Sai na rike hannunta ina fadin"To miye na kuka tunda kinsan ba haka ba ne..? Sai ta kalleni tana fadin"Na shiga damuwa ne anty Fa'iza na kai minzali nima kawayena duk da muke tare sun yi aure,ga Raliya itama an saka mata rana,ni kuma gaskiya Halisa ta fada bani da wani Tsayayyan Saurayi, sai ka samu kana murna sai ka nemi mutun ka rasa ga halin da yaya yake ciki akallah dai nima na kauce sai wata Lalurar ta Dauke muku Anty Fa'iza" Sai kawai ta kara saka kuka ni ko na Dage ina ta lallashinta sai da tayi shuru sannan na kalleta ina fadin"Saurareni Badar.shi aure da kike gani na Allah ne,Sannan mutum bai isa yayi ma kansa aure ba. shi kamar zanen kaddara ne irin na mutuwa da haihuwa ne lokacin da Allah yace kun ya fakum ba wanda ya isa ya hana Faruwarsa,kada kice zaki saka damuwa don wance tayi aure wance batayi ba ki dai ki bar ma Allah zabi ki kama kanki ki Tsarkake mu'amalan ki da Allah da Mutane kina Zaune Allah zai kawo miki miji nagari kiyi auranki. kada Surutun mutane ya Dameki ita kuma Halisa ki kyaleta in dai namiji ne ai d'an Babansa ne kina zaman zaman ki sai nuna mata kalan da zata gane tayi kuskure ki kwantar da Hankali Allah na sane da bayinsa masu takawa da Hakuri" Sai da na Tabbatar da mganata ta shigeta kuma ta aminta da mganganu sannan na fito daga Dakin ni kad'ai a Tsakar gida ina aiki Tausayin Badariya ya cikani kowaani bawa da nashi kabulen Rayuwar in kana gida baka yi aure ba, ace kaki aure shi kuma mijin ba Tukunya ba ne balle ka tantance na gari,sai ga shiga gidan wani auran kaji gwara zaman ka agidan ku ma,ammh duk lalacewar aure yana da Daraja saboda Ibada ce ta Ubangiji. Nayi alkawarin a duka Khamsin Salawatul di'na zan saka Badariya aciki,domin Allah ya sama mata mafita alokacin ma sai da na daga Hannayena sama nace"Ya Allah ga Baiwar ka nan Badariya ka fi ni sanin Damuwarta a cikin zuciyarta Allah ka kawo mata mafita daga cikin kyawawan mafitan da kake bawa bayin ka Salihai,Allah ka turo mata miji nagari wanda zai share mata hawayenta" Sannan na shafa a raina ina jin Wani iri,rayuwa kenan kowa da irin tasa kaddaran. *Janafty* [7/17, 7:32 PM] +234 703 465 7829: *KNKB2010* *Pay N500 Regular,Via 0552179550 Jamila Umar gt bank,Vip 1000* *09069067488* Har ga Allah na taya Badariya damuwar halin data ke ciki,Saboda ina aiki in abun ya fad'o min a rai sai na tsaya nayi mata addu'a acikin raina ballatana da naga tafi kwana biyu kafin ta warware sai nayi amfani da wannan damar na kara jawota a jiki ina kara nuna mata in dai tayi yakini da Allah ke yi to ta saki ranta mun rokesa kuma shi Allahu Rahimun ne,yana share ma bayinsa hawayensa da haka na samu ta saki jikinta. sai ya kasance in yara sun tafi makaranta Hafsah ta fita zata fito taimaka min da aikin gida,wani Lokacin har da na sana'ata muna yi muna hira hakan sai ya rika debe mata damuwa. Ba'a fi sati da dawowarta ba ranar sai Yayan nata ya kirata,ina falon lokacin na shigo da bahon da na jera gorunan zobo zan shiga kitchen na jera a frezer ta ma shigo ta tayani ne ya kirata,Kasa kunne ba Halina ba ne ballatana da nake da raunin ji da nasan ko na kasa kunnen ba lalle bukata ta biya ba,sai ban damu da naji abunda yake tambayanta ba, na shige na cigaba da aikin gabana sai ita ne ta shigo bayan ya sallameta tana cemin"Anty Fa'iza kiji Anty Binta" Sai na dago ina fadin"Me ya faru da Anty Bintan..? Cikin yatsina Badariya tace"Wai yaya Ishaq ta kira tana fad'an wai daga mun yi hatsaniya da Halisa ko sani batayi ba na hado kayana na dawo gida"Mirmishi nayi kafin nace"To shi yayan me yace?baki ta tabe bakin tace"Me kuwa.?fad'a ya yi min wai na rika hakuri da rayuwa" Sai na cigaba da aikina ina fadin"Ya fada miki gaskiya. Ke uwa kike ga Halisa bamai sauya wannan sunan a wajenta har abada" Daga haka bata kara mgana ba illah hmm!da tace min ta zo ta kama min muna jera gorunan tare ganin haka nima sai na saki mganar muka kama wata,Yadda shi ma bai min mganar ba haka nima nayi kamar ban sani ba ni nasan ina da miskilanci kuma abun nawa ya had'u ne sanadin mijin da nake aure da irin yadda ya tafiyar dani wajen zamantakewarmu,shiyasa na zama ba komai nake mgana a kai ba.ballanta na nuna na sanin din na koya ma kaina ga duk abunda ba'a ce Fa'iza zo kiji ba, ko zo ki gani ba. na fahimci bawa zai fi zama lafiya in ya bar abunda ba ruwansa hadisi ne guda kan haka. Fargaba na d'aya shekara ta na neman kare mana acikin wannan gidan akwai Karin Dawainiya na kudin Haya,kudin makarantan yara,ga jamal da sai wannan shekaran zai gama ga abinci da Hidimdimun yau da kullum,har takai ga mun fara awon abinci saboda komai namu ya kare sai abunda ba'a rasa ba,da na rasa mafita sai na auno masara aka nika nayi Tsaki da gari yau tuwo gobe fate jibi dambu sannan na kira Goggo nace ta saka ayi min garin Danwake da Taliyan murji ,Hafsah zata zo satin karshe ta taho min da shi ban fito na gayamata muna cikin wani Hali sai dai hikimarsu ta manya yasa sai ta Fahimceni,sai tace ba sai na aiko Hafsah ba,Yaya Isa zai shigo katsina Ranar jumma'a zai taho min da shi Da haka muka rabu saboda na lura komai in baka Tsara ba sai ka kwana aciki,a kwana a tashi na fara yi ma dan jarin nawa Rugu rugu ga masu siyan zobo da kunin aya sosai ammh kuma ba da yawa nake yin sa sosai yanzu ba,Nafi son ma a bani aikin Had'in Turaruka nafi samu sai dai shi zobo da kunin Aya sana'a ce ta cikin gida da zata tallafi Hidiman da bata gaza dubu goma zuwa kasa ba,duk yadda Yaya Ishaq nake ganin yana cikin Damuwa iya wanda na gani ne acikin Ransa bansan zafin da yake ji ba koda yaushe cikin fad'i yake yi"Kiyi hakuri Fa'iza na barki da wahala.Kiyi hakuri" Ammh duk da haka ban barsa ya zauna bai je ya duba Zainab da yara ba,tun bayan tafiyarta yafi wata bai je ba ni na matsa mai sai kawai yace min"Kina ta matsamin naje naje..To ina naga ma na motan zuwa ko a kasa kike son na tafin..? Sai na kallesa kafin nace" A bun bai kai haka ba,Ko ita ka fad'ama baka da na mota ai zata turo maka ka tafi din" Wani kallo yayi min kafin yace"Sai na gayamata bata fiki sanin bani da shi ba ne..? Ina jin ya harzuka sai na kama bakina ni kadai nayi kulla kulla na, na had'a cinikina na kwana Biyu, dubi biyar nabasa nace yayi na zuwa na dawowa bazai gagara ba,Ranar naga fad'a kamar zai dageni ya watsar da kudin yace na kwashe su bazai je ba, naki jin mganarsa na barsa masa su a tsakar daki na fice. ina jinsa yana fadin"Fa'iza ki dawo ki kwashe kudin ki nace,Haba matar nan so kike hakkin ki ya kamani.?gabad'aya kin Lullube rayuwata da alherin ki,so kike na mutu Allah ya sakani a wuta ko Fa'iza ai shikenan kin kyauta" Ina jinsa sai da nayi dariya wai ina so ya mutu ne ya shiga wuta Allah na Tuba daga taimako ni bana so auran su ya samu matsala ne sannan na dandana rashin miji a kusa bana fatan itama ta dan'dana duk da rayuwata ba irin nata rayuwar ba ne, ita tana da gata gaba da baya ba irina bace da gatan kalilan ne. Bansan ya akayi ba bayan kwana Biyu ya shirya yace zai tafin duk da bani da Tabbas nasan Mama ce zata matsa mai tana chan ne ammh na tabbata hankalinta na nan gani take yi yanzu tunda bata nan to sai a hankali,da ya tafi kwana goma yayi ya dawo. Sai dai yazo da kudad'e sun kai dubu hamsin yace Mahaifin zainab ya basa sannan ana ta dai kokarin neman aiki a ma'aikatu Dabam Dabam a bangaran da ya karanta wato na'ura mai kwakwalwa, ni ko a raina da fili sallata da zama na ina rokar masa Allah ya kawo masa aikin da zai amfanesa da kasa bakid'aya. Da kudin da ya samo ya siya mana kayan abinci,duk da Goggo ta aiko mana har da shinkafa da Yaya Isa ya kawomin sakon nan kuma na bashi kudin yaki karba yace tace kada ya karbo na kirata ina ta godiya sai tace"Babu godiya tsakanin mu Fa'iza da ina da shi abunda yafi haka ma zan miki shi"na aminta da mganarta yanzu Goggo ba irin da ba ne mijinta Tuni yayi Ritire yana gida sai kudin Fashion yaran ne ke kula da komai harta kudin makaranta Hafsa sune ba abunda zamu ce da goggo sai godiya,Sauran kudin kuma ya ijiye amfaninsu zai iya zuwa kwanan nan sai yabi shawarana ya bar min kudin a hannuna na adana. Tunda ya dawo na lura ya dawo da Dama daman da yake yi dani,Sai na fara shan jinin jikina,wani abun ma Saboda Badariya na gidan ne yasa yake ragamin,daya fara shigemin nake zaraf na shige dakin Mama ko na fito Tsakar gida na kirkiri aiki,haka kurum bana so mu kadaice saboda gudun kada ya ruguzamin shirina. Da daddare kuma baya samun dama Saboda yara ina yi musu karatun Qur'ani saboda Anum ma ta shiga ajin Hadda Baban ma yana yi musu na boko duk dare in mun gama su yi shirin kwanciya,ko yana son mgana dani sai nayi saurin jan Anum mu shige Daki mu kwanta ba Halin kuma wani abu saboda idon yara,da kuma idon Hafsah tunda tare muke kwana da ita. Yau muna zaune bayan mun gama cin abinci da ni da yaran duka muna kasa ne ina musu karatun Qur'ani Anum tana izifi goma ne Amir kuma ya wuce ashirin,su Ahmad