Sashe 24
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
na Dibar musu sakwaran ni dai ko ban ci ba,su dai su samu su ci,daki na jasu sukaci achan kada su ci afalo su lalata Su shigo fada'n komai ya Dawo kaina na shiga uku. Bayan sun gama Daman sun yi sallar su a makaranta,Sai na saka musu Sabbin kayan su Anum nata Murna Amir ne yace"Umma anguwa zamu? Sai nayi masa shuru ban ce komai ba sai na Tuna naji wani malami yana mgana kan tarbiya yara yace kada yaro ya jefa miki tambaya ki yi shuru to a ransa zai saka wani abu. Sai nayi saurin cewa"Sabuwar Umman ku ne zata zo Amir" Dukkansu suka bini da kallo ban damu ba na cigaba da fadin"Tare da Daadan ku zasu zo in kuka ganta ku je ku gaisheta itama Umman ku ce" Anum da Amir suka Dagamin kai Musty na chan na wasa da kwalliyar jikin Yan kantin da na sakamai riga da wando. Hatta Ahmad da bai jin Dadi na sakamai yan kati riga da wando,nayi mai Napkin duk da zawon yayi sauki ba kamar jiya ba na goyasa Tunda baya jin dadin jikinsa har alokacin. Su dai yaran suna ta Tsalle tsalen wasan su ni kuma ina zaune nayi jugum ina Tunanin wani irin Tarba amaryan Ishaaq zatayi min..? Sannan wani zama zamu yi da ita acikin gidan nan..? Nayi zurfi cikin Tunanina naji Amir a saman kaina yana fadin"Umma wayarki umma." Nayi firgigit na kallesa wayatace a Hannunsa ana ta kira ya mika na karba sai da gabana ya fadi da naga Sunan Ya Ishaq na kirana cikin Rawan jiki na Daga kiran tun kafin nayi sallama naji muryansa cikin Kaushi yana fadin"Ina kika kuma jefar da wayar ina ta kiran ki baki D'auka ba..? Cikin yanayina nace"Ban ji ba ne.." Karamin tsaki yaja kafin yace"Ina fatan kin gyara ko'ina..? Yanzu zamu baro gidan Mama" Kamar yana ganina na gyada kai sannan nace Allah ya kawo ku lafiya Bai ko amsamin ba ya katse kiran ya barni da waya a hannu ina Tunanin mafita da farko wlh jikina bai saki ba sai da ya kirani yace gasunan zuwa naji gabbaina sun saki jikina ya fara rawa ina nan zaune ina fama da Faduwar gaba naji kamar ana taba Kofar falo ko Hon dinsa banji ba ballatana Shigowar Mota,to ina ma nake da karfin jin ballatana,yadda hankalina ya bar jikina raunannun kunnuwan nawa ba su saka naji ko motsin shigowarsu ba. Sai da naji Sallamarsa da mganarsa Su Amir na dago na kalla basu bi ta kaina ba suka fice da gudu suna kiran sunansa Daada kamar yadda suke kiransa. Ni kuma ina zaune na kasa tashi Jikina gab gab yake yi kamar mazari gabana ya fara Dif Dif kamar an sakamin Wutar lantarki ji na nayi na kasa motsi sai yanzu nake jin yanayi na ba Dad'i ina Tunanin da wani irin kallo Amaryan tasa zata karbeni,?Kamar acikin kaina naji yana Kiran sunana a kausashe kamar yadda ya Saba. Sai na zabura na mike da Hanzari Daidai Anum na shigowa Dakin ta fara jan Hannuna tana fadin"Umma Daada na kiran ki" Kamar rakuma da akala haka Anum ta rika jan Hannuna har Tsakiyar Falo inda Ishaq da amaryan suka samu mazauni saman kujera mai zaman mutun biyu Amir na jikin Babansa Musty na Dauke ajikin wata Farar mace Doguwa Lalle tsarki ya tabbata ga Allah shugaban Hallitun Duniya. Lalle gaskiyan su Anty Binta ne kada na Had'a kaina da zainab,tazaran kamar sama da kasa ne a wajen nisa ashe a Hoto ma an rage mata kyau da Haske kamar balarabiya tana sanye da Wani leshi daga ganinsa mai Tsada ne doguwar riga taci Daurinta gashinta ya zubo har gadon baya Fuskata Dauke da kwalliya mai kyatarwa kafafunta da Hannayenta Sun ci kunshi Lalle baki da Fari kamar don ita ma akayi zanen Saboda yadda kunshin ya haskata kafarta da Takalmi daga ita har Ya Ishaq basu cire takalmansu ba har zuwa Tsakiyar Falon. Kanta na kasa tana ma Musty wasa yana mata gauranci bata san da ni a Falon ba ni kuma kawai ita nake kallon Sakin Hannuna Anum tayi ta nufi Babanta tana fadin"Daada Umma" Shima sai Lokacin ya Dago yana kallona ina ganin sanda Fara'arsa ta Dauke kamar yaga mutuwarsa hararata yake yi kasa kasa ni kuma Chanzawarsa nake gani yayi kiba kamar bashi ba Daga gani ya samu kwanciyar Hankali sosai. Na kasa gaba ballatana baya sannan bakina yayi nauyi shine da yaga haka ya D'aga baki yana fadin"Haka ake tarban baki a karofi ko Fa'iza..? Sai alokacin ta Dago kanta muka Hada ido hudu da ita ni dai a bangarena sai naji na muzanta ni bansan yanayinta a bagaranta ba sai dai ban gane yanayin da take ciki a Fuskarta ba. Tayi saurin Shanye mamakin ganina ta kallesa tana fadin"Maman su Amir right..? Tafada tana bin sa da wani irin kallon da Sai da na kauda kaina kai ya gyad'a mata yana fadin"Yes Fa'iza" Dukkansu a tare suka sakarmin ido sai naji kafufuwana na rawa lojaci d'aya sun kasa D'aukana sai na bi ra'ayin su na Durkusa kaina na kasa cikin yanayina nake fadin"Sannun..Sannun ku da zuwa an zo lafiya..? Bakina har rawa yakeyi Ta kalleni ta kara kallona sannan ta kallesa ya gyada mata kai Cikin Zakin muryanta da ta karye da Turanci tace"Hy Am Zainab Nice to mee u Fa'iza" Tafad'a cikin wani irin Turancin da na kasa ma jinta ballatana na gane ina jin yana mata mgana kasa kasa ban ji me yace ba nadaj ji tace"Oh sorry Honey..Kiyi hakuri Fa'iza ban san bakyajin Turanci ba kina lafiya..? Yasu Amir ina Ahmad ko shi ne a bayanki..?.honey goye kada kafafunsa sun lamkwashe ita kuma ta samu problem da kirjinta fa" Duka alokaci daya ta fad'a,kunnina na kasa yasa naji wasu daga cikin mganar nata sannan na Dago kaina ina kallonsu jin nayi shuru yasa yace mata"Tun kafin mu taho na fada miki yanayin Fa'iza bebiya bataji sosai sai kin yi mgana da karfi sannan zataji jiki Honey" Kwabe Fuska tayi kafin tace"Really..? Kai ya gyad'a mata kafin yace"Yes bata ji ki ba sai kin d'aga murya" Ta kalleni cikin Tausayawa kamar taga mai bara tace"Ayya am sorry" Ni dai kaina na kasa ban ce komai ba kawai sai naji tace"Whta is bebiya Honey..? I did get u..? Da Harshen Turanci naji yana mata bayani bana jin me yakefadi sai dai ina gani tana kallona tana d'an kwabe Fuska gani nayi bazan iya jure ganinsu ba yasa na mike da Hanzari zan koma Daki Ishaq ya Dakatar dani da Fadin"Kin ga Kwantomin Ahmad" Ba musu na karisa na kwantomai na mikamai har ya fara barci su Anum kuma sun samu Chaculate basu ma bi ta kan mu ba. Kallona yayi lokacin da yake karban Ahmad yace"Ki bude shashena ki kwashe kayan zeey da nawa zuwa chan" Cikin rawan jiki na koma Daki na Dauko key din ina ganinta tana bina da kallo,ni dai na bude Dakin nazo na Rika daukan jakunkunan da suka zo dashi sai ta karshen ne zan Dauka tace"No.." Sai ta juya tana fadin"Honey tok to her kasan ban iya mgana da Karfi ba..Tsaraban Kids d'ina ne" Shi ya fadamin tace tsaraban yara ne sai na kalleta cikin yanayina ina fadin"Sun gode Allah ya saka da alheri" Ta amsa da fadin"My pleasure" Mganar abinci nayi yace sai sun yi wanka sun yi sallah tukunnah Jikin Ahmad dayaji zafi yasa yace min ba shi da lafiya ne na dagamai kai sai ya kalleni yana fadin"Meyasa baki fadamin ba.?ai da ko Jamal yazo kun je asibiti an dubasa". Nidai ban ce komai ba itama kuma wayarta ta Dauko a wata karamar jaka mai kyau tana Dannawa kafin ta mike tana Fadin"Honey am Tired ina son nayi taking Shower' Mikewa yayi yabi bayanta yana fadin"Me too duk a gajiye nake" Ina kallon su suka shige suna rangaji Jikinsu na Dukan juna karamar jakar Hannun Zainab Ishaq ya amsa ya rike mata ita kuma sai lamkwashewa take yi tana Turancin da bana ganewa. Su Amir kuma sun samu Chaculate basu lura ba na Dauki jakar da tace Tsaraban yara ne zuwa cikin Dakina na Bude naga kaya masu tsada Kala biyu biyu na Anum har da riga da wando da takalma ni ma har ni naga Doguwar riga da pakistan riga da wando sai naji kayan basu burgeni ba na Tattara na ijiyesu na fita nace su Amir su yi alwala an kira sallar mangariba. Tare da yarana muka yi sallar mangariba muna zaune muna azkar Ishaq ya leko ya sauya kaya zuwa Jallabiya yace na kawo abinci,da Hijabin da nayi sallah na shiga Kitchen na Fara Daukan abincin nasu zuwa Shashen megidan basa Falon suna ciki na gama jera musu komai na Fice na koma D'aki duk da cikina na jin yunwa ammh na kasa cin komai a fatar bakina nake jin abinci bazai iya shiga ba sai kawai na sha Ruwa na koma ma kishingid'a ina kallon su Amir nata wasa Ahmad yayi barci,ina zaune a wajen har akayi sallar Isha'i sai na mike nace su bar wasa su sake yo alwala suzo muyi sallah Bayan mun idar Anum nata rigiman zataje wajen Daada dakyar na lallasheta da yayi barci,kafin su kwanta sai da suka kara cin abinci sannan nayi musu shirin barci sai da sukayi addu'a na tayasu suka Tofa sannan na baro Dakin nasu na koma nawa Ko barayin Shashen Ya Ishaq ban kallah ba Tunda suka shiga Ciki ban kara jin motsin su ba. Ni kuma na kasa barci da ya fara Fizgata sai na farka gajiya nayi da juyi na shiga tiolet nayo alwala nazo ina ta nafila sai wajen uku na Dare na kwanta shiyasa na makara sallar asuba rana ta farko da Ya Ishaq bai fito ya tara su Amir sun tafi masallaci ba Amir sai fadi yake yau Daada bai je masallaci ba ne Umma..? Sai nace musu yaje yaga suna barci ya kyalesu har nayi musu shirin hadda nayi abun karyawa Haruna ya Dauke su ya kaisu basu fito ba yaran dakyar na janye su suka tafi batare da sun ce zasu je gaida Daadan nasu ba. Suna tafiya nayi ma Ahmad wanka na shiryasa nima nayi wanka sai nasha Tea