Sashe 48
Kana Naka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yayi mata. Mutuwar Tamadina ta Dakeni matuka,sai dai na zauna nayi Tagumi ina sharan kwallah in Amir yaga nayi Tagumi sai ya cire tagumin yana fadin"Umma ki daina tagumi ummanki zata dawo" Sai ya bani dariya na jawosa jikina ina fadin"Aa bazata dawo ba Amir..Ai kasan mutuwa ko.?kuma a makaranta an fad'a muku duk wanda ya mutu ai baya Dawowa a rami za'a ha'ka a binnesa shikenan bazamu kara ganinsa ba" Cikin yanayin mganar sa yace"Ita Umman ki a rami aka sakata..? Sai na gyad'a mai kai Lokaci d'aya ina fadin"Eh mana..kowa zai mutu muma watarana zamu mutu a hak'a rami a binne mu baza'a sake ganinmu.Mu yi ma wadan'da suka rigamu mutuwa addu'a muma in mun mutu sai mu samu masu yi mana addu'a" Ya gyad'a min kai kafin yace"To Umma zan rika yi ma umman ki addu'a" Daman kuma ina yawan fad'a musu in sukayi sallan su rika cewa Allah ya gafartama iyayanmu da magabatanmu da yan'uwanmu,kuma suna yi,Har su Anum haka na koya musu nima in dai na yi sallah sai na Roki Allah ya jikan dukkan yan'uwa musulmai da suka rigamu gidan gaskiya mu kuma Allah yasa in tamu tazo mu samu cikawa dakyau da imani. An yi addu'ar Arba'in Tamadina,Ni ban je ba Hakama Yaya Asiya su Goggo ne da Yaya mariya suka koma sai dai daga gida nayi mata addu'a da Sadakan Allah yakai haske kabarinta na Rokar mata salama da amimci a wajen Ubangiji a kabarinta,Ni tunda Tamadina ta rasu komai ya fita kaina naji bakowani wani abu ne zai rika batamin rai ba,Na riga nasan na rasa dukkan wani bangare na jin Dadi, Dariyata kadai ya'yana ke gan. sune kad'ai yasa har yau nake tsaye kan kafafuwana,Saboda hakane yasa na Dage da shan mgunguna saboda in nazo na kasa ko nayi Rauni ya'yana baza su iya d'aukan maraici tun suna da kananun shekaru ba. shiyasa karfina da Kuzarina duk Ta dalilinsu ne shiyasa ita uwa ya'yanta kan zama gwarin gwiwanta sau da dama. Kwata kwata nama manta da mganar Form din da na cike na koyan sana'o'i da bada tallafi,na mikama Allah duka al'amarina,sai kwatsam Badariya tazomin da labarin an Turo mata sako Daga Kungiyar Women charity Foundation kan zasu tantancemu ranar asabar karfe goma na Safe a wata makarantar yan mata Dake cikin gari sai na rud'e na fara rawan jiki ina fadin"Bada..riya..To ni ya zan yi..?bansan ko'ina ba fa..? Sai tayi Dariya tace"Sha kurum ki zan yi ma Mama karyan makaranta sai nazo na rakaki" Sai da ta fad'i haka sai hankalina ya kwanta, tun daga ranar ko dayaushe addu'ata d'ayane in da alheri acikin wannan mafitan. Allah ya tabbatar min in ba alheri Allah ya musanya min da mafi alheri. Sai naji zuciyata ta natsu da al'amarin,Ranar jumma'a Dakyar na iya barci Saboda Zullumin abunda zai faru gobe,Da sassaafe na shirya yara suka wuce Tahfeez nima ban zauna ba na shirya tara da wani abu Badariya tazo na goya Ahmad na saka Dogon hijiba na mai ruwan kasa duk yasha ruwa na rufe gida muka tafi,Ita ta biya kudin adaidaita gaskiya akwai tafiya ba kad'an ba tsakanin gidana da Makarantar mun isa goma saura Haraban makarantar cike da manyan motoci daga gani abun na manyan mata ne. A wani babban hall na makaranta ake taruwa kai tsaye muka nufi chan mun shiga mun tarar da mata da yawa duk sunzo,muka samu waje muka zauna ina ta raba ido sai da goman tayi sannan Manya mata masu nasaba da ilimi da zati suka rika shigowa suka tsaya a gabanmu, ina ji Badariya namin Rad'a mai bakin mayafi mai jikan nan Hajiyar su Raliya ce na jinjina kaina daga gani kudi da isa sun zauna ajikinsu A she mu Talatin suka Dauka,Bayan sun kira sunayen kowa da kowa muka mike gabad'ayamu akwai yan rakiya ire iren Badariya,Wata Hajiya ce mai glass take kiran sunaayenmu,na kasa Raunanun kunnuwa a ina jin sunana na mike bayan Badariya ta rike hannuna muka mike tare sannan ta koma ta zauna, ashe Wani kati zasu raba na na shedar Training d'in da zamu yi sannan da wasu bayanan da suka danganci abunda za'a koyar damu. D'aya bayan d'aya aka rika kiranmu ana bamu wani karamin kati mai dan Fad'i.sannan akwai hoton kowacce ajikin katin har akazo kaina,na mike na kwanto ma Badariya Ahmad dake bayana na fita ina raba ido har gaban Babban ajin na mika hannu na karb'a ta kara kallona sama da kasa har na juya sai ta kirani da fadin sunana"Fa'iza Sidi karofi' Sai na juyo da Sauri saboda ina gabda ita naji ta fad'i sunana yasa Hajiyar su Raliya ta D'ago tana kallona sai na rankwafa na gaisheta da girmamawa sai ta amsa itama cikin sakewa Lokaci daya tana fadin"Kece matar Brother din Badar..? Sai na gyad'a mata kai cikin yanayi mganata nace"Eh hajiya tare..tare ma muke da ita" Sai na juya ina nuna mata Badariya ashe har tataso dauke da Ahmad tazo wajen mu,Ta duka ta gaida Hajiyar Raliya ta amsa tana tambayanta Mama tace tana lafiya sai ta kara kallona tana fadin"Ashe tare kuka zo..? Badariya tace"Na rakota ne Hajiya" Kai ta jinjina tana kara kallona nasan har da mamakin ganin yanayina sai matar nan mai glass ta duko tana mata mgana naga tana nuna mata Takardan hannunta sai ta amsa tana Dubawa kafin tace"Fa'iza abu hud'u zaki koya..?kuma a ka'ida biyu ne kina ganin zaki iya..? Da Sauri nace"Eh zan iya Hajiya.." Sai dayan Matar tace"Hajiya kinsan dokace Biyu ne ai hudu yayi mata yawa da wanne zataji..? Sai naga ta duka daidai kunnenta tana yi mata mgana sannan ta jinjina kai,Itama kuma Hajiyar Raliya sai tace muje mu zauna. Komawa mukayi muka zauna ina ta Raba ido,naga mata kala kala ire irena masu fama da rayuwa da zamantakewar aure,ni dai akasan raina ina jin yakinin zan koyi duka abunda za'a koyamin Saboda shi kad'ai nake ganin gatana a wannan duniyan. Bayan an gama bawa kowacce Katin ta, sannan suka fara mana bayanin yadda abubuwa zasu kasance zamu fara koyan abubuwan da zasu koyamana nan da sati d'aya zasu raba abun gida Biyu Mrning da Aftternoom,Da Safe za'a koyar da abubuwa Biyar da yammah ma biyar daman goma ne,Da Safe za'a koyar da girke girke da Had'a lemuka,Da yammah akwai koyan yadda ake hada halawa da dilka,Da yadda ake yinta,Da had'a Turaren wuta na Icce da Humra da su Kwallaca,sai na fara nazarin ya abubuwa na zasu kasance..?kenan sai dai na rika zuwa safe da yammah kenan..? Sannan sun yi mana bayanin awa Bibbiyu ne da Safe tara zuwa sha Daya da Yammah D'aya na rana zuwa uku na yammah,sannan sun bamu shawaran mu natsu zamu iya duka abunda za'a koyar damu tunda na wata uku ne tsawon sati goma sha Biyu ina jin duk abunda suke fad'i Saboda da karfi suke mgana kamar su san da masu Laluran rashin karfi ji irina. Sun tabbatar mana da cewa acikin mu za'a dibi mutane goma masu hazaka da aka ga sun chanchanta ranar da zamu gama za'a basu Jarin su a Hannunsu,sannan sun horemu da mu maida hankali komai daki Daki zasu koyamana duk abunda bamu gane ba mu yi tambaya. kada mu zama masu duhun kai,Sannan daga karshe sun ce zamu rika zuwa da Littafi da biro mu rika rubuta sunayen abubuwan da za'a koyamana saboda in mun koma gida mu yi bita,Sannan zamu rika rubuta sunanmu kullum inda muka zo da Turanci wato Attendence. Sannan ko da wani lokaci zamu rik'a zuwa da wannan katin shine shaidar an tantance mu sai mun nunasa za'a barmu mu shiga, zuciyata na cika da Farinciki har na fara tunanin ma na iya duka abunda nasaka raina zan koya,ajikin katina an saka Abunda nake son koya kamar yadda Badariya ta Rubuta, shi zai nuna inda ya kamata na tsaya sai Sha biyu na rana aka tashi sun tabbatar mana da cewa kwararun ma'aikata ne zasu jagoranci wannan tafiya tamu mun yi godiya sosai sukace mu yi ma shugabar wannan kungiyar addu'a da fatan nasara Rayuwa, ni ko araina nace duk Sallah sai na sakata nace Allah ya yi mata gatan Duniya da lahira kamar yadda itama tayi mana gata a duniya. Daga nan muka rabu da Badariya ta taremin adaidaita na Dawo gida zuciya ta cike da Farinciki,Sai dai na Fara Tunanin inda Zan rika kai Ahmad Saboda sun ce ban da yara saboda ba wajen da yara zasu zo ba ne,akwai abubuwan da bai kamata yara su shakesa ba yayin had'asa. Sa'adatu ta fadomin rai nako shiga na gayamata ta tayani murna ta kuma tabbatar min na rika barin mata Ahmad zata kular min da shi sai naji Sauki na Dauki damaran maida Hankalina kan damar da Allah ya aramin,Naji dadi tun Sha daya zan dawo gida nayi ma yara girki ko na kimtsa gida da la'asar kuma in na Dawo sai naji da girkin su kafin su dawo makaranta. Har wankin yaran sai da na kwashe na wanke na goge tare da nawa tunda zan fara fita ba lalle na rika samun Lokaci ba,Ranar Alhamis saura kwana biyu a fara koyar damu Yaya Ishaq ya dawo da Safe na sallami yara sun tafi makaranta kenan ina zaune afalo ina bama Ahmad kuninsa ya shigo ban ko ji sallamansa ba ina chan ina Lissafin duniya. Sai da ya kariso cikin falon ya kara yin sallama sannan na jisa,na d'ago na kallesa,kamar ba shi ba ya kara Kiba har da karin Saje da gemu ga Tumbi alamun yana samun hutu da jin Dadi. Kamar bakina na ciwo nayi mai sannu da zuwa bayan na kauda kaina. Ahmad kuma sai ya fara dagamai hannu yana gaurancinsa. Bakinsa na gogemai da Kyallen dake gefena shi kuma sai ya Duka ya Dagasa sama bayan ya sauke jakar Hannunsa, mikewa nayi ina kakkabe jikina zan wuce dakina araina ina fadin ka dawo adaidai kuwa. Sai dai ban karisa ba ya D'aga murya kirani na juyo cikin mganarsa yace"Kin yi min sannu da zuwa baki dauki kayana kin kai min ciki ba.kuma zaki wuce ni kamar kin ga wani banza Fa'iza..? Sai ban damu da kalamansa ba na koma na Dauki Jakar ya mike ina gaba yana baya ya bude shashen nasa. muka shiga a tsakiyar falon