← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 128

Sashe 98

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*******
Washe gari da safe kamar yadda Dr Amir ya fada ya dawo ya duba Nihal har a lokacin bata farfadu ba Basmal dake bakin gado tana rike da hannu Nihal se matsar kwalla take Ammar ne yace, "abar kauna ta kukan da kike ya isa haka, ko break ba kiyi ba addu'a zaki mata Allah yasa ta samu lafiya," juyowa Basmal tayi tana goge hawayan idanuwan tace, "my love tana bani tausayi ne, me tayi har za'ayi mata wannan mugun abun kona ta fa akayi, kuma a fuska baka tunanin fuskar ta ta lallace ban san wani hali zata shiga ba, ta wayi gari fuskar ta, ta samu matsala, koma waye ya aikata haka ba karamin azalumi bane" Basmal ta ida zancan tana jan majina janyo Basmal Ammar yayi jikin shi yana shafa kanta shima ji yake kamar ya zubarwa Nihal da hawaye cikin sigar lallashi yace, "insha Allah ba abinda ze samu fuskar, in Allah ya yarda kunar bazata shiga cikin fuskar ta ba, addu'ar mu take bukata kin ji abar kauna ta, muje nayi feeding naki abinci na lura yau kina so ki wahala min da baby" ya ida zancan yana shafa cikin ta shigewa jikin Ammar Basmal tayi tana dariya tace, "Waya ce ma akwai baby a ciki na, ba wani baby" ja mata hanci Ammar yayi yana cewa, "zaki ganine da idanuwan ki soon" haka dai Ammar ya lallaba Basmal dan ta ci wani abu.

**********

Wanna karan da sultan ya tashi bayan allura bacci ta sake shi da sauri ya mike zaune drip din hannu shi ya banbare, a hankali ya sako daga saman gadan yana dingishi dan ya daukar wa kanshi alwashin yau ze koma Nigeria dan ya ga wani hali Nihal take ciki saboda hankali shi ya kasa kwanciya Alex ne ya fado mashi a rai, murda kofar da akayi ne ya sasa waigowa da sauri herry ne ya shigo yana rike da handle din kofa yana bin sultan da kallo tunda sultan ya dage se ya bar kasar se fa ya bari kara kawai a fadawa Mr President ya sanar da shi gaskiya magana kara kawai ya sani ko kallan herry sultan beyi ba yace, "I need some cloth"
"sultan you need to get much better before you leave, oh my goodness sultan why can't you see your self sultan, you are serious sick"
herry...! Sultan ya ida zancan rai had'e fita herry yayi ya dawo rike da suit da waya hannun shi ya mikawa sultan yace, "mr president..! jim kadan sultan yayi sannan ya amshi wayar ya kara a kunne Mr president ne keta magana wanda bame jin me yake cewa hakan ne ya haifarwa sultan zama saboda jirin dake dibar shi har wayar Hannun shi ta subuce ta fadi, bugun zuciyar shi na karuwa kamar zuciyar shi zata fasa kirjin shi ta fito, saboda abinda Mr president ya fada mashi hawaye ne kawai ke bin kumatun shi, jikin shin ya mutu murus haka sultan ya shirya cikin suit na shi yana kuka shi kadai ya san zafi daya ke ji ya zama dole ya koma Nigeria, sai daya fara biyawa dakin Alex kwance yake har yanzu a Como sultan be san sanda kuka ya kubuce mashi ba saboda tausayi Alex ganin saboda shi ya shiga wanna halin Allah sarki Alex, lallai Alex ya fi dan'uwa a gare shi yayi abinda dan'uwan shi baze iya ba, kuka sultan ya kuma saki zuciyar shi na kara zafi da takaicin abinda kunna shi ya ji da kunyar abinda kunnuwan shi suka ji mashi yau, cikin zuciyar kuwa cewa yake Allah ya kare mashi Nihal din shi saboda abinda ya ji yafi ko mai daga mashi hankali Nihal ba komai ba ce sultan ya kara sakin kuka da kyar ya samu ya tsagaita kukan da yake, ya dade yana kallan Alex shigowar herry ne yasa sultan fitowa, kaitsaye gidan Mr president suka wuce duk yadda Mr president ya so sultan ya tsaya ya warke amma fir yaki dole tasa Mr president bada umarni akai sultan airport, kaitsaye airport suka wuce haka sultan ya fito yana ingishi dan kafar ba warkewa tayi ba ga wani kuna da zuciyar shi ke mashi hawaye na zubo mashi a haka jirgin su ya tashi zuwa na Nigeria.

*********
Da yamma Amir ya dawo ya duba Nihal yana kokarin cire mata dressing din da yayi mata yana cire mata hawaye na sulalo mata gabaki daya mutanan gidan na dakin Nihal ban da Nazili da Aziza mom ko addu'a take Allah yasa kunar bata shiga cikin fuskar ta ba Dr Amir yana gama cirewa ya mikawa Nihal mirror, jikin ta na rawa ta amsa a hankali ta kara mirror din a fuskar ta wurgi Nihal tayi da mirror din hannu ta ji kake taratsatsa..! glass din na tarwatsewa cikin daki wani irin kuka Nihal ta saki da karfi ta furta, "ya Allah wannan wace irin cutar wace..! da gudu Nihal da dankara...

```Taku har kullun salma mas'ud nadabo```
[1/23, 10:27 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*Story*
*And*
*Writing*✍🏾
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
(```We are the best among the rest```)

*Page: 115_116*

Da gudu Nihal ta dankara zata fice daga dakin Ammar ya tsafko ta wani irin marayan kuka Nihal ta saki tana kokarin kwace kanta daga rukwan da Ammar ya mata duk wanda ke dakin sai da zubar da kwalla, kokarin kwance kanta kawai Nihal take alama Ammar yayi Basmal da ido ta miko mashi allura bacci a hankali ya yayi mata allura lukus Nihal tayi tana kuka mara sauti a hankali bacci ya dauke ta Ammar ya shifid'e ta saman bed, Ammi kuwa kuka takeyi kamar me Adda tace, "na rasa dalilin bibinin rayuwar yaran nan da ake kiri-kiri ana so a maida yarinya karama mahauciya, Allah ya toni asirri koma suwaye" gabaki daya dakin aka dauka da Amin, Nazili dake gefe Hannun ta nad'e a kirji cikin zuciyar tace ba Amin ba kiran sallah magrib ne ya tashi kowa dan zuwa gabatar da sallah Nazili na fitowa taci karo da Aziza fisgo Hannun ta tayi suka shige cikin daki.

suna shiga ta sake mata hannu tana cewa, "ni fa wannan aikin be mun ba fuskar bata kone yadda ya kamata ba, ya kamata ace tafi haka lallacewa,"
"ran ki yadad'e har da ihu da tasa ya firgita mu, kuma kinga da sinbul be je da wuri ba har ita kan sai ta kone ba fuskar ta kad'ai ba,"
"kuma fa amma dai wannan sinbul ya watsa min aiki i wish dukan ta ta kone, zan so ace sultan ya dawo na kusa ya ga fuskar abar kauna shi yadda ta zama, se yasha mamaki, bari na baki kudin ku kuje ko raba amma next idan na saku aiki bana san shirme..,! drewar Nazili ta bude ta ciro badil din 1k har hudu ta mikawa Aziza ta amsa tana godiya ta fice.

Misalin karfe 7:00pm flight din sultan ya sauka Nigeria a hankali yake takowa daga stairs din jirgi har ya sako gabaki daya taxt ya tara driver taxt din ne yace, "yallabai dama irin ku na shiga motar haya? kamar na so na san ka a gidan TV ana fira da kai ba kai bane Dr sultan dan sarki kano" murmusawa sultan yayi yace, "nine" ya ida zancan tare da shigewa motar yana cewa, "dan ina Dr sultan ba shi ze hanani shiga motar haya ba dani daku duk daya muke a wajan Allah"
"haka ne yallabai har dakuma kai din na daban ne cikin alumma, amma sai na ganka kamar baka da lafiya dan naga kamar da rauni a kafar ka, ko mu wuce asibiti ayima dressing,"
"Ah na gode ba sai mun je ba idan naje gida zan duba da kai"
"toh shikanan yallabai Allah ya karo sauki"
"Amin" suna tafiya driver motar na jan motar yana jan sultan da hira sama-sama sai dai sultan ya bi shi da eh a'a a haka har suka karaso gida da kan shi driver taxt ya budewa sultan kofar motar har sultan na cewa, "ya bari baya san irin haka" shi kuma yana cewa dan yaga kafar shi da raunine sai da sultan ya fito sannan yace, "sai dai ban san suna ka ba?
"Au suna na yallabai suna na mudi..!
"malam mudi gashi ban fito da kudi a jiki ba yanzu haka daga ni sai kayan jiki na, na iso kasar nan amma gobe ka dawo zan baka kudin ka"
"yallabai daka barshi kawai kayi ma tallakawa abinda yafi haka ko motar nan daka gani cikin ta cikin motocin da karabawa matasa ne kwanaki,"
"A'a baza'ayi haka ba komai ga nayi inayin shi dan Allah kuma hakkin ka ne kamar yarda nace ma gobe to goben ka dawo"
"toh yallabai na gode Allah ya kara ma lafiya da daukaka" sultan yace amin sannan ya shige gida fadawan dake bakin geta suka fara sakin baki suna bin sultan da kallo zubewa sukayi suna gaishe shi, daga masu hannu sultan kawai yayi kaitsaye part din Ammi ya wuce.
Chapter 98 · 0% Book details