Sashe 76
Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Yauma kamar kullun Minal ce zaune tana feeding Nihal pepper soup din yan' ciki dan bata fuska Nihal tayi tare da ture boll din da hannun ta tace, "na koshi" murmushi Minal tayi tana cewa, haba aunty Nihal ki kara mana baki ci da yawa ba, ki daure ki kara" harara wasa Nihal ta makawa minal tace, "matsala ta dake kenan kullun kika zo se kin cika min ciki da abinci ko nishi ya zamana da kyar nake gaskiya na koshi" Nihal ta ida zancan tana turo baki nawwara da Minal dariya suka saki aje boll din minal tayi tana cewa, "Allah yasa yayana ya shigo se ya dura maki da kan shi, tun tea din safe baki kara cin komai ba kuma se mun fadawa mom" nawwara bata ida rufe bakin ta ba aka turo kofar dakin gabaki dayan su juyowa sukayi a tare sultan ne ya shigo ya shirya cikin wata suit ta kama jikin shi Ash colour da inner blossom dark ash colour necktie dinshi kala suit nasa ya saka gem stone rose, sajan shi ya kwanta yayi luf-luf ya wani kara kyau, tsare shi da ido Nihal tayi tana kallo tana kara jinjina kyau irin na sultan da sauri minal ta mike daga saman gado tana cewa, "yauwa yayana gara da ka zo taki cin abinci bata san cin komai" Minal ta ida zancan tana yamutse fuska janyo hannun shi nawwara tayi tana cewa, "gara da ka zo se kayi feeding nata da kanka" Minal da nawwara suka ida zancan suna jan hannu sultan zuwa bakin gadan da Nihal take zaune kallan juna minal da nawwara sukayi suna dariya suna kallan Nihal "suka ce ai yanzu dole ki ci abincin tunda ga yaya" bata fuska Nihal tayi tana kallan su dariya suka saki harara sultan ya maka masu yana cewa, "abokiyar wasan ku ce kuke mata dariya, nasan zata ci ni take san gani shiyasa ta ki cin abinci" sultan ya ida zancan yana tsare Nihal da ido tare da shafa sumar kanshi, zama yayi saman bed din gefan Nihal yana cigaba da cewa, "kalle su dariya fa suke maki za'a maki dure" sultan ya ida zancan yana daukar boll din pepper soup din turo baki Nihal tayi tare da sakin kuka dariya minal da nawwara suka saki aje boll din sultan yayi ya bisu a guje da gudu suka bar dakin suna yima Nihal gwalo ai se ta kara fashewa da kuka a hankali sultan ya karaso kusa da ita daukar boll din yayi tare da nufar ta da spoon din abinci bud'e baki Nihal tayi tana amsa ganin ba wasa a fuskar sultan tana ci tana kuka tana harara shi har ta cinye, sultan ko murmushi yayi tare da kad'a kai tissue ya zaro tare da goge ma Nihal baki tsare shi da ido Nihal tayi tana mugun mamaki sauyin sultan tsare ta da ido sultan yayi shima yana kallo kamar me neman wani abu a fuskar ta murd'a kofar da akayi ne ya dawo da hankalin su nawwara ce ta shigo wurga ido nawwara ta shigayi tana cewa, "am sorry handbag din na namanta bazan kara takurawa Princess ba" ta ida zancan tana ficewa juyowa sultan yayi karaf suka had'a ido da Nihal gashin ganta Nihal ta shiga gyarawa tare da kauda kai a hankali sultan ya daura hannun shi a wuyan Nihal wani irin yar Nihal taji tana kallan sultan wani saban yanayi na shigar ta matsowa yayi har suna jin saukar numfashin juna su ga kamshi turaran shi daya mamaye mata hanci me sanyi dadi, a hankali ya kama gashin kanta ya nanad'e mata shi kamar ganmu sannan ya dawo ya zauna cikin honey voice din shi sultan yace, "na san daga yanzu baze kara takura maki ba, tunda na nanad'e shi ko" har a lokacin Nihal na kallan shi kamar a mafarki take ganin sauyin sultan ruwa ya tsiyaya a glass cup ya mika mata da magani amsa tayi tare da shanyewa sannan sultan ya mike ze fice, har ya isa bakin kofa ya kama handle din kofar Nihal tace, "na gode," bud'e kofa sultan kawai yayi ya fice, kwanciya NIhal tayi tana tunanin sauyin sultan watsar da tunanin tayi tare da lumshe idanuwan ta bacci me nauyi yayi gaba da ita.
Bangaran sultan ko patients yaje yana dubawa yana dubawa su yana tuna cute face din Nihal, da moment din da suke kasancewa a yanzu murmushi sultan ya saki tare da cigaba da duba patients cikin kulawa da kwarewa.
Da yamma Ammi da mom suka zo duba Nihal cike da kayan marmari wani irin gata Nihal take samu wajan su da kulawa dan zama tayi kamar gold cikin su Ammi ce tace, "Masha Allah jiki yayi kyau sosai se dai mu jira ranar sallama," mom tace, "gaskiya ko Allah abin godiya kwanaki biyu da suka wuce kallo daya zakayi ma yarinyar nan ka zubar da hawaye," shigowar Basmal da Ammar ne ya katsewa mom zance har kasa Ammar ya duka yana gaishesu dauke da fara'a mom da Ammi ke amsawa Basmal saman gadan da Nihal ke zaune ta nufa ta zauna tana cewa, "aunty Nihal ni kyau ma da fresh naga kinayi kamar asibitin ya amshe ki" Basmal ta ida zancan tana daga gira dariya Nihal tayi tana cewa, "bana san tsoka na ni asibiti ma ya isheni" murmushi Basmal ta saki tana cewa, "nayi missing naki gidan ba dadi bame rakani siyaya da raba IV se ni kad'ai yaran nan ko fita da su headache zasu sakar maka" Ammi ce ta cabe zancan da cewa, "ko tana gidan ba rakaki zatayi ba oh sokike Gimbiya ta rinka gantali, kuma sannan maganar sa headache ki nemi me sa maki, daga dawowar yara za'a sa masu kahonzuka" turo baki Basmal tayi tana cewa, "kai ammi yanzu se ki hanata, kuma maganar yaran ai ba karya nayi ba ita kanta Nihal kawaici take Masu da Wannan surutun na su"
"Toh yayi maida min magana" Ammar dake kallan Ammi harara ta sakar mashi tana cewa, "katsare ni dana mujiya, ko rama mata fadan zakayi" dariya Ammar yayi yana cewa, "ni dai ban ce komai ba Ammi"
"kama ce yanzu na zaune ka" dariya Ammar ya saki yana cewa, "ni dai na gano ki kishi kike" Ammar ya ida zancan tare da ficewa.