Sashe 112
Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Kaitsaye hotel suka wuce dama sultan yayi bucking daki kafin su iso room key din kawai ya amsa suka shige Nihal na shiga ta zauna sultan ya zuba mata tuwan ta zauna tana ci tana lumshe ido sultan na kallan ta yana latsa wayar shi yace, "uhm wanna baby dan kauye ne, har ya fara maida min mata yar kauye" murguda mashi baki Nihal tayi ta cigaba da cin tuwan ta sai da ta gama cin tuwan tas sannan ta fara jin tashin zuciya da sauri ta mike sultan yace, "ya dai aman ne,.! da gudu ta shige toilet ta kwarara amai sai dai ba wani mai yawa bane, wanke mata fuska sultan yayi ya dauke ta cak ya maido daki ya kwatar da ita saman bed ya ja mata blanket ya koma toilet ya gyara wajan ko daya fito Nihal na kwance cikin blanket tana rawar dari, gwalbar magani ya dauka yasa sirinji ya zuko allura a hankali yace, "tashi na maki allura kin ji I now how you feel ki daure ki tashi" kuka Nihal ta sa mashi tace, "bana san allura ni dai ka bani magani kawai na sha"
"Sorry na san baki so bazan maki da zafi ba, a hankali zan maki" kuka Nihal ta saki tana cewa, "ni dai bana so" numfasawa sultan yayi yana shafa kumatun ta rike da allura yace, "inna baki magani yanzu aman shi zakiyi na sani, dana maki allura zaki samu sauki fever dake damun ki zata sauka aman da kike ze tsaya ko bakya so ki warke,
"Ina so na warke"
"Good girl ba zan maki da zafi ba kin ji, a kwance ma zan maki" daga kai Nihal tayi takoma ta kwanta ta rintse ido, a hankali sultan ya mata allura amma saboda tsabar rigima ta Nihal har da mashi kukan shagwaba jikin ta kuwa yayi rau a haka bacci ya dauke ta, sultan na ganin haka ya debo ruwa a boll da towel yana dadana mata a ko ina na jikin ta
*Washe gari*
Kamar yarda malam ya fada washe gari ya dawo ya karayyi ma jakadiya rukiya sai dai ta rinka zufa tana girgiza kai yana mata addu'oi.
yau ce rana ta uku da malam ya dawo sanyawa yayi aka dauki Dara aka fito da ita parlour aka jinginar da ita jikin kujera, yana kwararo mata karatun Al Qur'ani sannan ya bata ruwan addu'a tasha ya shafe mata jikin ta da sauran ruwan, wata irin atinshawa Dara ta saki har sau uku a hankali ta bude idanuwan ta, tana bin muta nan parlour da kallo daya bayan daya kasancewar kowa na gidan na parlour a hankali ta sauke idanuwan ta kan Nihal dake rab'e jikin mom hawaye suka sulalowa Haulatu ganin tsantsar kamar Nihal da Hansatu sai dai kawai Nihal ta gwadawa hansatu fari da murjewa kasancewar ita abirni take ko ba'a fada mata ba wannan jini tace jini yaya Habu ce, yanzu ta gane Nihal dawa take mata kama alama jakadiya tayiwa Nihal da hannu ta matso kusa da ita kallan-kallo aka fara a parlour Nihal da jikin ta ya dau rawa idanuwan ta sunyi raurau da hawaye, alama sultan ya mata taje jiki a mace ta mike ta karasa gaban jakadiya shafa kumatun Nihal take tare da fashewa da kuka tana cewa, "yarinyar dana bari a gida tana da shakara 4 itace ta zama haka Nihal..! rungume Nihal jakadiya tayi ta fashe da kuka itama Nihal din kuka take tana cewa, "Ashe ina da raban saki a idanuwa na aunty Haulatu, munyi kewar ki aunty Ashe ina da saura farin cikin a rayuwa ta" dago da fuskar ta jakadiya tayi tana murmushi a hankali ta sakarwa Nihal pack a goshin ta tana goge hawayan idanuwan Nihal kara rungume juna sukayi cikin murna jakadiya take cewa, "Ashe akwai ranar da zan tuna baya ashe akwai ranar da zan iya tuna ko ni wacece Allah na gode maka daga nuna min wannan rana tabas munga SAUYIN RAYUWA a cikin zuri'a mu munga iftila'i mara karewa..! kuka Dara ta saki tace, "Allah sarki rayuwa ina inna, baffa, yaya Habu, yaya Tanimu karki ce mun babu su suna sun bi su yaya hassan kwakwalwa ta baza ta dauki rashin yan'uwa na ba kuka Dara take sosai Nihal na girgiza mata kai cikin kuka tace Abba da umma rushewa tayi da wani irin kuka mutuwar su umma ta dawo mata zabuwa har wani shidewa take jawota sultan yayi ya rungume tsam dan baya fatan abinda ze samu Nihal da abinda ke cikin ta dan kukan ba karamar ila ze iyayi ma abinda ke cikin ta ba lallashin shin ta kawai yake be damu da mutane nan dake parlour
Kuka sosai Dara take cikin kuka tace, "A daran daurin aure ne na bar gidan mu cikin dare wanda a lokaci jina nake tamkar a kaya babu abinda na dauka daga ni sai kayan jiki na, hatta garin a lokacin bakin shi nake gani bana fata na kara waiwayar garin koda na fito daga gida jeji na yanka dan karma a neme a tasha saboda bana fatan waiwayowa gida, tafiya kawai nake ni kaina ban san ina zani ba daga wannan lokaci na manta kuni wacece, a haka nake tafiya ina wuce kauyi ka idan dare yamin na kwana a gona ki tunda Asuba na mike na cigaba da tafiya ko abinda zan ci be dame ni ba ni dai burin na na bar yankin...!
```Taku har kullun salma mas'ud nadabo```
[2/5, 1:51 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*Story*
*And*
*Writing*✍🏾
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑
🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
(```We are the best among the rest```)
*Page: 129_130*
"haka na rinka yanka jeji ina tafiya idan naji kishin ruwa na tsaya na sha na rafi ko na makiyaya bani na iso garin kano ba sai dare, a lokacin Gimbiya da maimartaba sun je ran gadi suna dawowa saboda tsabar galabaitar da nayi yasa ko gabana bana gani har na haura kan titi motar fadawa ta banke ni wannan dalilin yasa suka taimake ni suka kaini asibiti, bayan naji sauki na waware suka min tanbayar duniyar nan ko ni wacece na kasa furta ko da kalma daya saboda na manta kai na bana iya tuna komai ko suna na bana iya cewa gashi, ganin haka yasa Gimbiya Nadiya ta tausayamin ta dauke ni muka dawo gida ta mikani hannu Ammi na cigaba da yi mata aiki kamar yarda sauran bayi keyi duk sanda nayi yunkurin tunani mai zurfi game dani sai na wuni ina fa da ciwan kai wannan dalilin yasa bana yunkurin tuna ko ni wacece..! Dara ta idan zancan tana kuka maitsuma zuciya gabaki daya muta nan parlour tsit sukayi, Nihal da Dara nata sheka kuka Dara ta numfasa tace, "ina baffa ina inna yaya Habu yaya tanimu? ko baki fada min ba na san mutuwa ta cigaba dayi mana dauki dai daya kamar fari" kuka Nihal ta saki tana kara sauke ajiyar zuciya idanuwan ta sun kunbura tace, "Allah abin godiya duk da bani da wayau a lokacin da kika bar gida ina yawan jin labarin ki, a bakin umma na" nisawa Nihal tayi tace, "yau ce ranar data dace na falasa kuni wacece bayan miji na da ya Ammar babu wanda ya san kuni wacece, ku yafemi a kan karyar danayi maku a farko ba komai ya janyo nayi karyar ba sai dan gudun abinda zeje ya dawo da kuma fargabar komawa kauye" nan Nihal ta shiga bama Dara labarin irin bakar wahala data sha hannun gwoggo da Baffa har sanadiyar guduwar ta zuwa birni ta ida zancan tana cewa, "umma a gaban idanuwa na Abba ya rasu mutuwa mai firgitarwa wanda har yau na kasa daina tuna irin mutuwar da Abba yayi duk sanda na tuna sai na zubar da hawaye duk da bani da wayau a lokacin amma na dade ina razana tunda Abba ya rasu RAYUWA ta sauya daga ni har umma mun azabtu a hannu gwoggo sai da muka zama marasa gata ko abinda zamu ci gagara mu yake kullun nice yawan talla, ta safe daban ta rana daban haka ta yamma har umma ta rasu cikin kunci da bakin cikin RAYUWA" Nihal ta ida zancan tana marayan kuka kowa na parlour ya zubar da hawaye jawo ta sultan yayi jikin shi yana lallashin ta.
Nazili kuwa duk rigima da suke da Nihal sai data tausaya mata jikin ta yayi mugun sanyi tana jinjina bakar wahala da Nihal ta sha, numfasawa Dara tayi tace, "Allah ya ji kan magaba tan mu ya ji kan yaya da umma Allah ya gafar ta masu ya kai haske kabarin su, idan tamu ta zo Allah yasa mu cika da imani" gabaki daya aka amsa da amin Dara ta cigaba da cewa, "Amma dai yaya Tanimu ya cika mugun butulu mai saka alkairi da shari, baiyi amana ba yaci amanar yaya Habu ya tozarta mashi iyali bai kyauta ba ya tafka babban kuskure...!