← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 128

Sashe 89

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Nihal ta na fita Basmal ta rugo ta rungume Nihal washe baki Nihal tayi tana cewa, "saukar yaushe amma na ji dadi dawowa nan taki" dariya Basmal tayi tana cewa, "akwai story baza ki gane bane shigowa ta kenan ko part din mu ban wuce ba, ba yadda my love beyi dani ba na bari na huta sannan na shigo amma na ki," Ammi ta shiga kwallawa kira, fitowa Ammi tayi daga bedroom tana cewa, "tunda naji kira da ihu nasan ke ce, haka ake se kin wanke kafafuwan ki, kin taho nan bayan mun bada ke gidan waziri zaki sauka ko part naku, shi Ammar din yana mi kika taho na" turo baki Basmal tayi tare da karasawa wajan Ammi tana cewa, "na lura tsohuwar nan bakiyi missing nawa ba, ko dai kishi kike mazajan naki sunyi aure sun barki" dariya Ammi ta saki tana cewa, "ka jimin ja'ira ai ni ina tare da su mutu ka raba ni ce on top" dariya Nihal da Basmal suka saki Basmal na cewa "ina zasu kai ki kin zama cus"

Rufe mashi ido da akayi ne yasa sultan saki murmushi yana cewa, "rigimame ya dawo" dariya Ammar ya saki yana cewa, "wato har wani lakabi ka min"
"Eh mana rigimar ka tayi yawwa amma fa nayi missing naka"
"Ai dama na fada zakayi missing nawa kace a'a"
"uhm naji ban da cika baki ai kad'an nayi" sun dade sultan da Ammar suna hira yau she gamo kiran sallah la'asar ya sasu wucewa masallaci.

Bangaran Nihal da Basmal bayan sun gama fira part din Ammi suka wuce part din Basmal suka dasa wata sabuwa hira Basmal se zuba takewa Nihal har tana ce mata Ashe haka soyayya take ya kamata su ware lokaci ita da sultan su je honeymoon tunda akayi auran su basu sha iska ba kullun suna cikin family house, Nihal ko a zuciyar ta cewa take idan da wannan zan je honeymoon to za'a dade ba a je ba har duniya ta tashi kuwa, ruko hannu Nihal Basmal tayi tana cewa, "kinyi shuru Aunty Nihal ya kamata ki fadawa yayana, shigowar ki rayuwar yayana kin sauya shi da yawwa aunty Nihal, kuma na san ze amince da maganar, shifa yayana a kanki ya fara soyayya kuma yana ji dake sosai, aunty Nihal ya kamata kuje yawan bud'e ido ko saboda ke,"
"Basmal kenan zamu je ne karki damu aiki ne yama sultan yawa shiyasa"
"uhm aunty kenan shikenan" sannan suka cigaba da hira su ta yaushe gamo

Nazili ce ke shirya cikin duguwar riga ta peach colour rigar ta mata kyau sosai ta kama jikin ta Aziza ce ta turo kofa ta shigo Nazili dake shafa tana hango Aziza ta mirror cikin ladabi tace, "Gimbiya ki na da bako" tsayawa cak Nazili tayi da shafa huda da take tace, "bako wannan wani irin bako ne ya zo min ba tare da izinina ba,?
"ba wani bako bane na mu zo mu gani ba Gimbiya, Alex ne ya zo neman ki da alama ya zo da muhimmiyar magana dan har ce mashi nayi baki da lokaci wani bako yanzu tunda weekend ne" murmusawa Nazili tayi tace, "ki ce mashi ina zuwa zan so naji mi ya kawo shi, kuma dami ya zo ina nan tafe na same shi"
"to ranki ya dad'e" sannan Aziza ta ja mata kofa ta fice.

Bayan fitar Aziza da yan mintoci Nazili ta fita a main parlour ta sami Alex zaune yana sanye cikin suit din shi black ta kama jikin shi sosai yayi kyau da shi gashi kan shi se shining yake Nazili na isowa Alex ya mike tsaye cikin ladabi murmusawa Nazili tayi tace, "mike tafe da kai ne, naji ance kana nemana lafiya dai ko,?
"ba wani abu bane ya kawo ni dama kwanaki biyu da suka wuce a wajan dinner kin yadda fost naki, shine na gani kuma naga akwai abubuwa masu mahimmaci a ciki" d'aga kira Nazili tayi tace, "amma ka kyauta sosai ka san kan aikin ka, kamar kasan na dad'e ina nemanta amma na rasa ina na aje ta ashe, na yarda ita ban sani ba" mika hannun Nazili tayi ta amshi fost din tana jujuya ta bude fost din Nazili tayi komai nata na cikin babu abinda aka taba har Alex ze fice Nazili tace, "dan tsaya mana, ina zuwa" daki Nazili ta shiga ta debo kudi a drewar sannan ta fito ta karaso inda Alex ke tsaye tace, "ga wannan ka samu na kashewa..! tsare Nazili da ido Alex yayi yana kallo sannan ya tako inda Nazili take ya amshi kudi ya juya yace, "bana bukatar kudin nayi maki ne kawai saboda Allah"
"Ka amsa ni na baka sometime tallakawa nada matsala nasan cewa kana bukatar kudin nan, amma saboda taurin kai irin tallaka baze bari ka amsa ba" Nihal ta ida zancan zata wuce dan ba karamin haushi Alex ya bata fisgo ta Alex yayi har sai ta fada saman fafadan kirjin shi ya matse ta gam SNA jin saukar numfashin juna zuciyar na harbawa lokaci daya cikin nuna isa Alex ke magana da nunawa Nazili ita ba komai bace yace, "ke kudi ya dama bani ba, of coz ni ma'aikaci ne, dan ina aiki karkashin sultan bashi ze baki damar dauka ta matsiyaci ba, idan ma kina tunanin haka kinyi kuskure, kasata ke biya na albashi, albashi na na wata daya shine albashin ki na rabin shekara, I hope you get me right akwai mabuka ta a waje da yawa kina iya basu" murmusawa Nazili tayi cikin sigar raini wayau tace, "wow..!hakan be mun ba da mari na kayi sannan zan gane ka ji zafi, maganar da na maka anyway ka ci lokacin ka" Alex be ida saurara zancan ta ba ya fice, zancan zuci Nazili ta cigaba dayi ji yadda yake magana se ka ce jakin kano kamar ba bature ba, anyway koma dai minene matsiyaci ne kai, saboda ba a canzawa tuwo suna, a kasar takuma ba wani dan shege bane amma se fihila mtsww sannan Nazili ta wuce bedroom din Ammi.

Da daddare bayan kowa ya gama dinner ya wuce part din shi kamar yadda aka saba, Nihal ke sanye cikin kayan baccin pink riga mai dogwan hannu da wando, tana tsaye gaban dressing mirror tana sharce gashin kanta murda kofar da akayi ne yasa Nihal juyowa sultan ne ya shigo shima ya shirya cikin dark blue kayan bacci shi riga mai dugwan hannu da wando kallo daya Nihal ta mashi ta dauke kai system din shi sultan dauka ya hanye saman bed sannan yace, "Nihal..! Na kamala komai naki na fara zuwa makaranta insha Allah gobe zaki fara zuwa" a razane Nihal ta juyo tana kallan sultan tace, "makaranta..? Ni ba zan kara zuwa ko wace makaranta ba"
"amma ai ke kika ce dole na maida ki makaranta idan ba haka ba zaki fadawa Ammi irin zaman da muke ko kin mata, sai kuma yanzu ki ce a'a"
"Oh ta nan ka bulo kenan idan kai ka manta abinda ya faru dani ni ban manta ba, ba makaranta da zani aunty abiola ta dawo ta cigaba da min lesson kamar yadda aka saba, tunda fita wajan ya zamar min matsala" Nihal da ida zancan ta kokarin goge hawayan fuskar ta karasowa gaban Nihal sultan yayi ya ruko hannuwan ta yace, "duk abinda kikaga ya sami bawa kadara ce, kuma mutum baya gojewa kadara shi, Nihal karatu na da anfani sosai insha Allah babu abinda ze same ki zan baki kulawa yadda ba abinda ze cutar dake" sultan ya ida zancan yana dago da habar Nihal cikin sanyi murya Nihal tace, "promise..!
"promise" sultan ya fada murmushi Nihal tayi tana cewa, "shikenan zan je makaranta Allah ya tsare"
"amin.! sultan yace
Chapter 89 · 0% Book details