Sashe 124
Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da ruwa a buta baba Sani ya dawo ya mikawa sultan ya daura alwala suka wuce masallaci, bayan sun idar da sallah suka dawo gida a tare suna tattaunawa sam baba Sani ba shi da wata matsala musanman yarda ya ga sultan nada natsuwa yarda suke fira tamkar sa'anni juna sun dan jima sosai a can daga nan suka wuce gidan Aunty Aisha a nan ne fa suka baje suna fira kasancewar weekend ne Abban Nana na gida suna tare da sultan a company suna fira, Nihal kuwa na cikin gida tana zuba sangarta Aunty Aisha na biye mata rike da plate din pepper soup din yan cikin aunty Aisha ta fito daga kitchen tana cewa, "yauwa daughter zo ga pepper soup din ya sauka" washe baki Nihal tayi tana lumshe ido ta amshe plate din tana cewa, "na gode mama tun yana kan wuta miyau na ke tsinkewa tun kafin na ci," murmusawa mama tayi ta ce, "ai yanzu ya sauka sai aita ci" Nana dake zaune gefe tace, "na lura yanzu an fi ji da Nihal ta kwace min gwabnati" dariya Nihal ta saki tana mata gwalo murguda mata baki Nana tayi tana kokari sa hannu cikin plate din pepper soup din mama tace, "kul naga kin kara kai hannu cikin plate din nan tsame hannu ki, ki wanke wannan na daughter ne, dan ita nayi shi idan kina so ki shiga kitchen ki dafa da kanki" turo baki Nana tayi Nihal na mata dariya tana mata kwalele.
Bayan Nihal ta cinye pepper soup din ta tas, suka baje a bedroom din Nana suna wata sabuwar hira, sai ku san bayan sallah isha suka dawo gida gajiye likis dan Nihal tun a mota ta fara jin bacci, a parking space drive yayi baki sultan ya bale murfin mota tare da daukar Nihal kamar baby suka wuce part na su.
A bakin kofa ya aje ta tare da daure mata ido da veil din ta, Nihal na murmushi Sultan ya ja hannu ta tana bin shi kamar rakumi da akala, wani bedroom suka nufa dake cikin part nasu wanda duk zaman Nihal bata san akwai shi ba, bud'e kofar dakin Sultan yayi suka shige dakin tare iya kar tsaruwa dakin ya tsaru kayan baby's ne birjik komai na dakin pink and white, ga kayan wasa na mure rayuwa gefe guda kuma drawer ce wanda kayan baby ke ciki kala-kala, a hankali Sultan ya cire mata veil din dake idanu ta kallan dakin Nihal take da surprise tana murmushi dan ko bakin magana ta rasa juyowa tayi tana facing Sultan tana murmushi rungume shi tayi tana cewa "thank you love bani da bakin da zan maka godiya" haka Nihal ta gama zagaye dakin tana murna.
Bayan kwana biyu abubuwa da yawa sun faru ciki harda shirye-shiryan bikin da ake ba kama hannu yaro tsakanin Nazili da Ahmad kullun shakuwa suke karawa sai dai sam Nazili bata san shine mijin da zata aura ba, d'an zaman da suke tare yasa sun shaku sosai, har takai ga Nazili ta fara jin wani abu game da shi musanman data ganu shi din musulmi ne yanzu, yau ma kamar kullun bayan ta dawo daga office wayar ta ta hau ruri ganin sunan Ahmad ya sata kai hannu da sauri ta dau wayar sun dade suna fira a waya har yace mata weekend yana so su fita su sha iska tare sannan idan bazata damu ba yana garden yana jiran ta, to Nazili tace mashi cike da murna sannan ta katse wayar tana smile cikin sauri ta shirya cikin kayan da suka amshi jikin ta, Ammi kuwa dadi ne ke lullube ta ganin yarda taga Nazili ta saki jiki ta da Ahmad.
```Taku har kullun salma mas'ud nadabo```
[3/10, 6:30 PM] salma😝: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA* 🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*Story*
*And*
*Writing*✍🏾
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑
🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
(```We are the best among the rest```)
*Page: 141_142*
Tunda biki ya rage saura wata uku Sara ta dawo kano tana shan gyara wajan Dara tayi fresh ta murje ta kara kyau ta bar gwoggo da wata datijuwa na kulla da ita, ana biyan ta duk wata tunda Sara ba shanono zata zauna da mijin ta ba.
Kamar yarda Ahmad ya bukaci su fita da Nazili weekend hakan yasa Nazili ke shiryawa ciki wata light brown gown din ta, ta kama jikin ta tamkar dan ita akayi ta tayi make up sosai tayi rolling kanta da cream veil tayi kyau, kafar ta na sanye da takalmi mai tsini, ringing din da wayar ta keyi ne ya katse mata hanzari, ganin sunan Ahmad a scream din wayar ya sata sakin murmushi tare da ficewa daga bedroom din zuwa compound
A compound ta sami Ahmad sanye yake cikin armini royal blue suit da white inner tie din sa kala suit din, ta kama jikin shi yayi kyau smile Nazili ta saki tana kallan Ahmad da shima din kallan ta yake dan ba karamin kyau ta mashi ba, a hankali ya bud'e mata murfin mota ta shige.
Park suka wuce kaitsaye a wasu madaidaitan kujeri suka zauna masu dauke da table suna shan ice cream suna fira, yanayin wajan yayi ma Nazili matukar kyau musanman yarda iska ke kad'a wajan da green flowers din dake kad'awa lumshe ido tayi tare da ware su ta sauke idanu ta kan Ahmad da tun isowar su ya kafe ta da idanuwan shi, a hankali ya daura hannu shi zaman Nazili wanda a halin yanzu jikin ta ya mutu mudus san Ahmad da kaunar shi kawai ke azalzalata haka shima nashi bangaran cike da gwarin gwiwa ya fadawa Nazili cewa shine mijin da zata aura yana mai cigaba cewa, "na san cewa ni mai lafiya ne na nemi auran ki ba tare da amincewar ki ba, ki amince dani Nazili zan nuna maki so da kauna a rayuwar auran mu wallahi Nazili ina san ki ina maki so wanda ni kai na ban san adadinn shi ba, san ki ya dade da mamaye duk wani lungu da sako na zuciya ta, ki daure ki so ni koda kwatan wanda nake maki ne duk da zuciyar ki na tare da wanda kike so, please Nazili ki bani dama na nuna maki san da nake maki, Dan Allah kada ki ce ba kya so na" numfasawa Ahmad yayi yana kallan Nazili wanda idanu ta ke kasa tana wasa da yatsun hannu ta wani irin farin ciki ne ya lullube ta ya kara mamaye zuciyar ta, ita kanta bata san da ta fara godewa Allah daya bata Ahmad a matsayin miji da zata aura, ji take tamkar an cire mata k'aya lokaci daya taji wata irin iska mai dadi da sanyi na shiga kofofin jikin ta san Ahmad da kaunar shi na kara narkewa a zuciyar ta, ita kanta tanbayar kanta take yaushe ta afka tarkon kaunar Ahmad, yanzu ta fara so yanzu ne ta san menene so wanda a rana daya Allah ya dasa mata san Ahmad a zuciyar ta yabi lungu da sako na sansan jikin ta da ruhin ta, shuru da tayi ne yasa Ahmad dan matse hannu ta yace "ki ce wani abu please" kayatancan murmushi Nazili ta saki wanda ita kanta bata san tayi shi ba, ta zubuwa Ahmad idanu ta wanda ko bata fada mashi sirrin zuciyar ta ba ya hango tsantsar san shi a kwayar idanu ta yanayin kallan da take mashi ne ya saukar mai da kasala lokaci guda ya shagala da kallan ta a hankali ta furta, "nima ina san ka Ahmad..! a da ba so nake ba a yanzu na fara so a kanka na san me so, ni dai fata na ka rike ni amana" katuwar ajiyar zuciya Ahmad ya saki wani irin dadi ne ya lullube Ahmad ya rasa ina zai sa kan shi saboda murna Nazili kuwa taga rawar kafa dan gabaki daya Ahmad ya rasa ina zai tsomata, a haka suka cigaba da nunawa juna so da kauna.
Baki dayan su zaune suke parlour a part din Nihal suna fira sai tafka musu ake tsakanin Nawwara da Minal parlour ya kacame da hayaniyar su, har da Nasim da Ashad ake hirar daga nan aka fada hirar program's din da za'a tsara Nihal dake zaune hannu ta rike da Khalifa baby dan wata uku sai wasa take mashi ta zakalkale ana tsara dinner da za'ayi tayi uwa tayi makarbiya Nazili na gefe itama kasancewar yanzu itama tana shigowa cikin su a dama da ita, har da ita ake tsara abubuwan da za'ayi, hayaniya kawai suke sai ka rantse da Allah an fara bikin yarda suka kacame parlour ana fira, shigowar sultan ne ya katse surutun dake tashi da kallo yake bin su daya bayan daya yana kallan yarda suka maida parlour, kamar yara ko gidan sha'ani a hankali suka fara tattare komatsan su suna cewa, "yaya sannu da zuwa" yauwa ya ce masu a takaice yana bin Nihal da kallo dake zaune da Khalifa ga tulelan cikin ta aje briefcase din shi yayi yana aika mata smile kamar yarda take aika mashi mai cike da tsantsar kauna ya amshi khalifa yana cewa, "amma dai Darling baki da kirki yanzu saboda Allah sai ki sakarwa hayaty wannan dirkekya d'an naki kamar dan shekara nauyin shi sai yasa ta haihu ba shiri," Nihal dake gefe tana murmushi tace, "ba ruwan darling nina matsa mata ta bani shi ba yarda ba tayi da niba na mikawa mai kula da shi ba naki," cike da zolaya Sultan ya ja ma Nihal kunne yana cewa, "oh dama keke wahala min da baby ko" yar kara Nihal ta saki mai cike da shagwaba tana dire-dire tamkar ba cikin jikin ta zaro ido Sultan yayi yana cewa, "ki bada himma ki samama baby na problem da kanki kiga yarda zamu kwashe a gidan nan" dariya Basmal tayi ta mika hannu ta amshe khalifa gabaki dayan su suka fice, Nihal kuma ta dauki briefcase din sultan ta bi shi bedroom kasancewar yayi gaba.