← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 128

Sashe 110

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nihal ce rungume da sultan tana yawa da hannu ta saman chest din shi har a lokacin Nihal bata dai tsuma ba sultan yace, "hayaty yana ji bugun zuciyar ki na gudu da sauri da sauri ga jikin ki yayi zafi mike damun ki hayaty ko baki lafiya ne? Sultan duk ya rud'e yana tanbayar Nihal, idanuwan Nihal da suka ciko da kwalla ita kanta tsoran kanta take ringing din wayar sultan ne ya katse masu tunani Ammi ce ta kira shi daukar wayar yayi abinda Ammi ta fada mashi ne ya sashi mikewa a zabure yana cewa, "yanzu tana ina..! duk da Nihal bata jin abinda Ammi ke cewa ba ta san maganar Nazili ake da Aziza katse wayar sultan yayi Nihal dake kwance tace, "love mike faruwa? cikin sanyin murya yace, "Nazili ce ba lafiya, an tsice ta a waje an mata duka da alama yan fashine suka tare ta, ita kuma Aziza rabin jikin ta ya kone" sultan ya ida zancan yana saka jallabiya Nihal kuwa sauke ajiyar zuciya tayi tasa duguwar rigar ta suka fice tare.

Labari har yaje kunna maimartaba gabaki daya muta nan gidan suna part din Ammi, Ammi sai kuka take mom na bata hakuri Aziza kuwa asibiti aka wuce da ita Nazili kuwa fuskar ta ta kunbura kallo daya zakiyi wa fuskar kaji baka marmarin sakewa bakin ta ya kunbura suntun kamar yaja ruwa saboda tsabar duka daya sha a hannu Nihal, idan ka kalli bakin har dariya sai ta nemi ta kwace maka, Ammar ne ya bata taimakwan gagawa yasa mata drip, Aziza kuwa asibiti aka wuce da ita dan na ta matsala yafi karfin kula a gida, koda suka je asibiti sai da akayi wa Aziza theater Nihal kuwa ta jinjina rashin imani data tafka daga ita sai su Yasmin suka san tsiyar da suka shuka.

Washe gari da safe kasancewar yau ta kama Monday bayan Nihal ta shirya cikin uniform din ta ita da sultan suka wuce main parlour sukayi break a gwagwace kasancewar sun makara har sun fito company Nihal tace, "love ban duba Nazili da jiki ba bari na je na duba ta" kallan agogan dake makale a hannun shi yayi yace, "hayaty mun makara fa kiyi sauri ki fito" to Nihal tace, ta koma cikin gida kasancewar Nazili a dakin ta take jinya Nihal ta shiga ta maida kofar ta kule da key Nazili dake bude kunburarun idanuwan ta ta sauke kan Nihal, ganin Nihal ya sata ranaza tana kallan ta dan yanzu tsoro Nihal take bata takowa gaban ta Nihal tayi ta ciro wuka a schoolbag din ta tana kyali tayi kamar zata cakawa Nazili rintse ido nazili tayi hawaye na wanke mata fuska ko magana bata iyawa bare tayi ihu dariya Nihal ta tintsire da ita a hankali Nazili ta bud'e ido Nihal na zaune gefan gado tana kallan Nazili tana girgiza kai tana dariya can kuma ta daure tace, "somin tabi na maki idan har zaki cigaba da bibiyar rayuwa ta zaki ga abinda yafi haka muni idan kunne ya ji jiki ya tsira hope you get me right sannan Nihal ta fice.

Rayuwa ta cigaba da tafiya cikin jin dadi sosai Nihal ke maida hankali kan karatun ta, tsakanin Nana da Nihal kuwa sun kara kulewa dan yanzu haka Nihal bata da kawa sama da Nana itama Nana haka, har cewa ake suna kama saboda tsabar abota, idan Nana ta koma gida bata da wani labari sai na Nihal haka zata wuni tana ba mama labarin Nihal kawar ta mama kuwa har so take taga Nihal, ba komai ke sata jin haka ba sai tuna Nihal din yaya hansatu Allah sarki Nihal din ta wanda yanzu ta zama tarihi babu irin neman da basuyi mata ba, har aunty Aisha ta sare ta mika lamuran ta ga Allah.

So biyu Nana tana zuwa gidan sarki wajan Nihal a nan Ashad ya Kyala ido yaga Nana tunda ya ganta ya rasa suku ni tun yana karya ta abinda yake ji game da ita har ya yarda da cewa ya kamu da san Nana so mai tsatsani, haka ya samu sultan ya fada mashi kan yayi ma Nihal magana kan Nana tunda kawar ta ce sosai sultan ya ji dadi hakan dama Nana akwai natsuwa da hankali.

duk abinda Gimbiya jalila tayi yunkuri aikatawa Ashad sai ya hana ta har gwada mata cewa yayi duk abinda ya sami sultan ta rubuta ta a je kamar ya same shi ne, hakan yasa Gimbiya jalila ta zubar da makaman ta badan ta so ba sai dan farin cikin Ashad.

Nazili kuwa ta rage shiga sha'ani Nihal dan ba karamin razana tayi da barazanar kashe ta da Nihal keyi ba, gashi duk wani abinda ta aikata mata Nihal ta gwada mata ta sani kuma itama zata iya aikata mata mafi muni shi zaman su lafiya shine ta cire sultan a zuciyar ta ko kuma tabi dare ta kashe ta ko kuma ta tona mata asirri da irin wannan barazanar Nihal ta ci galaba a kan Nazili ga wani mulki da take shinfidawa cikin gidan.

Yauma kamar kullun bayan ta dawo daga makaranta part din Ammi ta wuce saboda tun a makaranta kanta ke mata wani irin ciwo komai ta kasa ci sai ruwa, duk abinda ta kai baki sai taji kamar za tayi aman shi ga wata kasala da take fama da ita tun ba yau ba ko part nasu bata san shiga tafi gane ma ta zauna a dakin ta na part din ammi, ko kayan jikin ta ji take bata san su sai wata yar shirt din sultan blue data saka, a parlour ta same Ammi tana shan fruit ciki fara'a Ammi tace, "har an dawo kenan? murmushi Nihal tayi tace, "Eh Ammi na dawo" kallan rigar dake jikin ta Ammi tayi tace, "Ah lallai soyayya ruwan zuma yau kuma rigar tashi aka dauko aka saka tunda baya gida" dariya Nihal ta saki duk kunya Ammi ta rufe ta daki ta shige Ammi na cewa, "dawo na ja'iri idan tayi tsami zamu ji ne," dariya Ammi tayi tana girgiza kai, Nihal na shiga daki ta kishingida saman sofa turo kofar da kayi ne ya sata mikewa zaune Dara ce ta shigo dauke da plate din danbu wanda Nihal tace ma mom ta naso idan ta dawo makaranta ta ci da kanta mom tayi mata danbun jin ta shuru yasa mom cewa Dara ta biyo ta da shi murmushi Dara tayi tace, "Gimbiya ga danbun nan da zafin shi sauko na baki" turo baki Nihal tayi tace, "umma wai yaushe zaki daina ce min Gimbiya ni fa bana so tamkar uwa na daukeke" Dara kanta dake sunkuye tace, "insha Allah zan daina cewa tun da ba ki so" murmushi Nihal ta saki ta sako kasa ta zauna Dara na bata danbu cike da zakuwa Nihal tace, "bari ma na gwada maki hotan umma da Abba tunda yau na samu dama" murmushi Dara ta saki tana cewa, "ki bari ki gama cin abincin na lura sam baki san cin abinci yan kwana kin na" bata fuska Nihal tayi Dara tace, "dako min na gani yau dai Allah yayi zan gan su kwanaki kiran da Gimbiya ta maki ne ya hanani gani" drewar Nihal ta bude ta ciro hotan umma da Abba tace, "gashi Umma..!Hannun Dara tasa ta amsa tana ta murmushi abinda ta ganine ya sata daskarewa hannun ta na rawa kwakwalwar ta na wani irin juyawa jirin na din barta nuna hotan take da yatsa tace, "ya Ha..! sulalewa tayi kasa sumamiya da karfi Nihal tace Dara....!!

```Taku har kullun salma mas'ud nadabo```
[2/3, 6:30 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*Story*
*And*
*Writing*✍🏾
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
(```We are the best among the rest```)

*Page: 127_128*

Jijiga Dara Nihal take amma ko motsi da gudu ta fito parlour jikin ta na rawa tace, "Ammi! Ammi..! Ammi dake zaune mikewa tayi tana cewa, "lafiya kuwa Nihal? nuna daki Nihal take tana cewa "umma.! Umma.!
"Me ya sami umma? nuna daki Nihal take tana kuka dunguma sukayi gabaki daya har da bayin dake parlour suka rufawa Nihal baya, koda suka shiga dakin Dara na kwance ko motsi batayi Ammi ce ta kalli Nihal tace, "garin ya haka ta faru ko dama bata da lafiya ne amma yini yau lafiyar ta lau ko ciwan kai bata ce min tanayi ba" ciki kuka Nihal tace, "daga na gwada mata hotan umma da Abba shine kawai naji tana wasu maganganu ta sume..!
"Maza kawo ruwa na yayafa mata, sannan ki kira sultan ya zo ya duba ta" ruwa Nihal ta debo ta yayafawa Dara amma shuru ko motsawa batayi ba, da sauri Nihal ta wuce zuwa part nasu dan dauko wayar ta, layin sultan ta shiga kira sultan dake duba patient ganin kiran Nihal ya sashi matsawa gefe ya bar patient da nurse, da kyar Nihal ta sai ta kanta amma hakan baya hana a gane taci kuka tace, love.!
"Hayaty meke faruwa naji muryar ki wani irin, jikin naki ne? cikin jan majina Nihal tace, "A'a love umma ce ka dawo gida we need your help Umma ce ba lafiya" Nihal ta ida zancan tana kuka sultan na jin haka yace gashi nan zuwa ta daina kuka everything will be okay datse kiran sultan yayi da sauri ya bar asibiti zuwa gida.

Koda sultan ya dawo gida da sauri Nihal ta tare shi tace, "umma na bedroom dina duk laifi nane love nina janyo mata haka please ka duba ta bana so wani abu ya same ta saboda ni" duk Nihal ta rud'e talabo da fuskar ta sultan yayi yana kalla wadda tayi jawur yace, "calm down hayaty zata samu lafiya insha Allah kin ji" hura mata iskar bakin sultan yake a fuska yace ta rinka jan numfashi tana saukewa a haka Nihal ta samu natsuwa suka wuce bedroom din Nihal.

Duk wani taimako daya dace a ba jakadiya sultan yayi amma abu ya faskara gashi tana numfashi amma bata motsi, hankalin mom ba karamin tashi yayi ba da taga halin da jakadiya take ciki, hatta bayin dake karkashin Dara kuka suke saboda Dara mutuniyar kirki ce.
Chapter 110 · 0% Book details