← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 128

Sashe 111

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Asibiti aka wuce da Dara saboda ciwan ya wuce gida isar su asibiti aka shiga da Dara emergency dan bata taimakwan gagawa alamarin Dara ya faskara test sultan yasa aka mata, ba abinda ke damun ta result ya nuna, duk wata na'ura da ake duba cuta da ita ansawa Dara amma still lafiyar ta lau yake gwadawa, har sai da takai an tara meeting saboda ciwan Dara daga karshe bincike ya nuna ciwan Dara bana asibiti bane asirri ne.

Koda suka dawo gida daki aka kwantar da Dara sultan nayi mata karatun Al Qur'ani kafin malamin cikin gidan ya zo kusan duka gidan dauka yayi da karatu gabaki daya a ranar sai da akayiwa Dara sauka, Nihal dake ta sharbar kuka aje Al Qur'ani hannun ta tayi saman bedside drewar ta cigaba da kuka jawota jikin shi sultan yayi yana kissing forehead din ta sauke ajiyar zuciya Nihal take tace, "love duk nina ja mata shiga wanna yanayin, daga nuna mata hotan umma da Abba ta suma har yanzu bata farka ba, idan ina ganinta cikin wannan halin ina tunawa da umma na lokacin da ciwan ta ya same ta daga irin haka bata kara mikewa ba har ta rasu," sauke ajiyar zuciya Nihal take shafa bayan ta sultan yake yana cewa, "is okay hayaty ba insha Dara zata samu sauki..! Shigowar maimartaba da malam ne ya katsewa sultan zancan guri suka ba malam Nihal ta koma cikin su Ammi ta daura kanta saman kafadar mom.

Ruwa a cup aka ba malam ya dade yana addu'a cikin cup din ya tofa ya shafawa Dara a fuska, cikin kira ashi mai dadi ya fara yiwa Dara rokiya ana fara rukiya Dara ta fara juya kai kamar mai mafarkin ban tsoro zufa sai keto mata take kamar tayi tsere har sai da malam ya gama karatu sannan ta daina juya kai, magunguna malam ya bada na karya samu yace, "insha Allah akayi mata anfani da wannan magani cikin kwana uku zata mike da yarda Allah abinda yasa ma yanzu bata mike ba, ba karamin asirri aka mata akala asirri zai fi shekara daya a jikin ta, kuma asirrin anyi shine yarda zata manta kowa nata da ita kanta sannan aka kara mata da kurciya makarin asirrin shi ne duk sanda tayi tozali da wani nata ze kare to abinda ta gani jiya shi yayi yunkuri karya asirrin, insha Allah gobe zan dawo dan cigaba dayi mata magani" sallati su Gimbiya jalila suka dauka asirri kuma to waya mata suka shiga kallan-kallo har kusan fiye da shekara cike da gulma Gimbiya jalila tace, "na ga abinda ta gani ya sata shiga wanna hali..! dan har yau bata daina halin ta na tsegumi ba shiga safgar sultan ne kawai ta daina, Nihal jikin ta na rawa ta mikawa Gimbiya jalila hotan hannu ta, kallan hotan Gimbiya jalila tayi ta mikawa yakumbo, yakumbo ta mikawa mom haka suka rinka kallan hotan suna alajabi, maimartaba kuwa godiya yayi ma malam sosai sannan malam ya tafi, Nazili ce ta katse shurun da cewa, "hala na jikin hotan ne suka mata asirrin" wani irin kallo Nihal ta watsawa Nazili ta mike a hasale doke bakin Nazili tace, "iyayan nawa ne ke asirri" rike baki Nazili tayi ta kaiwa Nihal duka ta goce takalmin kafar Nihal ta core tana kokarin kaudawa Nazili, rike Nihal sultan yayi Ammi ta rike Nazili saboda kokowar dake neman balewa tsakanin su, Ammi tace, "baki gani bata lafiya idan baki iya bakin ki ba sai kin bawa kanki wulakanci" bama Nihal kunne sultan yayi yace, "hayaty 2days din nan kin fara zama mafadaciya wallahi" murguda mashi baki tayi tana aikawa Nazili harara

Da daddare bayan kowa ya koma part na shi sultan da Nihal suka wuce part nasu suna shiga, zuciyar Nihal ta fara tashi dan kwata-kwata bata san shiga part din toilet ta nufa da sauri tabar sultan a parlour, kwarara amai kawai take kamar zatayi aman yan cikin ta, wanke baki tayi ta kora ruwa a zing aman ya wuce shirt din sultan daya cire yau daya dawo daga office ta gani cikin basket din kayan wanki ta dauka tana shinshin nawa ta wani lumshe ido, sultan dake parlour yana kallan news jin Nihal shuru yasa ya bita bedroom kara ruwan daya jine ya sasa nufar toilet tsaye gaban zing ya hango Nihal ruwan famfo sai zuba yake ita kuma rike da riga shi a hannu har sultan ya kashe famfo zing din idanuwan Nihal na lumshe sultan yace, "hayaty na lura yau cikin good mood kike me sirrin" lumsasun idanuwan ta Nihal ta bud'e tana murmushi shafa kumatun ta sultan yayi yace, "hayaty mikike da wannan rigar me dati ce fa" amshe rigar sultan yayi yasa cikin basket din wanki, didira kafa Nihal take tana cewa, " ka bani abu ai na sani, kamshi rigar kemin dadi" ta ida zancan tana dauko rigar bata fuska sultan yayi yace, "hayaty rigar dati ce fa Allah kadai yasan germs din da kike shaka baki gani dana dawo gida nake canza kaya saboda warin asibiti, ki aje rigar muje mu kwanta kin ji" langwabe kai Nihal tayi tace, "please love ka kyale ni na kwanta da ita duk abinda na shaka ban jin dadin shi sai rigar da ita zan kwanta,"
"Ke kuma da wannan rigima ya zo maki muje mu kwanta na lura rigima baby na yake saki, oya muje" Nihal na gaba sultan na bayan ta suna fitowa bedroom ta koma toilet da gudu tana kara kwarara amai sultan ya rude sosai gani yarda Nihal ke kwarara amai da kan shi ya gyara wajan ya wanke mata fuska saman abin kwamin wanka Nihal ta zauna tana shinshi na riga shi cikin shagwaba tace, "love bazan kara zuwa bedroom ba bana jin dadi kamshi dakin, bazan kwana a part din nan ba"
"Hayaty idan bamu kwana ana ba ina zamu kwana" cike da shagwaba Nihal tace mu kwana ko ina amma banda part din nan," Nihal ta ida zancan tana kukan shagwabe, to sultan yace ya hada mata ruwan wanka yace, "ki fara yin wanka first kafi ki fito na gama tunanin inda zamu kwana tunda baki san nan din" daga mashi kai Nihal tayi sannan ya fice.

Koda Nihal ta gama wanka sultan ya mika mata pink night dress din ta ta saka sannan ta fito rike da rigar shi a hannu dogwan hijab sultan ya mika mata ya dauki car key yace, "muje..! har a lokacin rigar sultan na hannu ta sultan yace, "hayaty ki aje rigar nan mana" makale kafada Nihal tayi, amshe rigar yayi ya aje kuka Nihal ta saka mashi ganin kukan take da gaske yasa sultan mika mata da sauri Nihal ta bar part din.

suna fitowa parking space suka nufa Nihal tace, "love ina zamu je?
"Zamu je inda zaki samu bacci ke da baby na" dan karamin bakin ta Nihal ta turo tace, "baby kuma a ina" jawota jikin shi sultan yayi yana shafa cikin ta pack ya sakar mata a goshi yace, "thank you hayaty, Allah na gode maka daka azurta ni da babba kyauta," ita dai bin sultan dana mujiya Nihal take tana surprise wai ita keda ciki murmushi take saki tana bin fuskar sultan da kallo a hankali ta daura hannu ta saman na sultan wanda yake saman cikin ta tace, "Da gaske ni ina da ciki eeeh" Nihal ta fada tana washe baki ja mata hanci sultan yayi yace, "Eh mana.! Bude mata hannu sultan yayi ta shige jikin shi kamar ya maida ta ciki dan murna ya kusa zama daddy.

mota suka shige sultan ya ja suka bar harabar gidan asibitin shi ya fara zuwa, ya dauko allurai da magunguna da Nihal zata bukata musanman daya lura cikin me sata laulayi ne, cikin mota ya dawo ya sami Nihal ta dan kwanta jikin seat goshin ta sultan ya taba zafi rau tausayin tane ya lullube shi lumsasun idanuwan Nihal ta bude tana sakin smile, "sorry hayaty me zaki ci? cike da shagwaba Nihal tace, "tuwan dawa miyar kuka" yar dariya sultan ya saki yace, "ina zan samu tuwan dawa cikin daran nan,? na lura baby na da rigima ya zo" mota sultan ya ja, haka sultan ya rinka zagaye garin kano yana neman tuwo duk restaurant din da suka je ya kare da kyar ya samu akayi mashi kwatancan gidan jummala mai tuwo a nan ya samu tuwan shima na karshe.
Chapter 111 · 0% Book details