Sashe 7
Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai yamma likis Tanimu ya dawo daga gona yana shigowa yaga saban babur fake a kofar gida mamaki ne ya cika Tanimu ko
Babur ɗin waye wannan ya faɗa yana ƙarasawa ciki, da Haulatu ya haɗu da ita tana tsalle-tsalle zata fita yace, "ke" tsayawa tayi tana raba idanuwa yace, "wake da wannan babur ɗin,? wangale baki Haulatu tayi tace, "na yaya Habu ne" take annurin Tanimu ya ɗauke bangaje Haulatu yayi saura kaɗan ta kife ya shige ɗakin su yana shiga Indo ta miƙe tare da riƙe ƙugu, kallon ta Tanimu yayi yana ƙoƙarin ajiye fatanyar dake hannun sa Indo ce ta jeho masa tanbaya dacewa, "anya Tanimu kai ɗan gidannan ne kuwa,? juyowa yayi a razane yana binta da kallo kawar da kai tayi ta cigaba da cewa, "na lura a gidan nan baka da wani gata, kai da karen gidan nan baku da maraba, Tanimu babu abinda ka iya sai dai kayi noma da kiwo kayi naka kayi na Malam, shi kuma ɗan gata ya je shanono ya samo kuɗi ya dawo a rinƙa rawar ƙafa a kan shi, yanzu haka yana nan cikin gida ana ririta shi ana tatalin shi sannan dan wani ƙarin wulaƙanci wata ƴar leda ya ɗauko ya miƙa min wai ga tsaraba, sauran ya shige da ita ciki tunda ga matsiya ciya matar faƙara'u ga ladan ganin Indo, to wallahi bazan ɗau irin wannan iskancin ba, da akeyi idan kai ana maka kana shanye wa to ni ba zan ɗauka ba," ta idda zancan tana haki, idanuwan Tanimu ne suka kada sukayi ja yace, Indo kenan baki san gabar da ke tsakanina da muta nan ba ni da kai na nayi alƙawarin sai naga bayan su, ki zuba ido kiyi kallo Indo kuma da kike cewa ni da karen gidan su bamu da maraba lokaci na zuwa da Habu zaiyi haushi kamar kare, naji daɗi sosai da kika gano gabar da ke tsakanina da ahalin gidan nan tunda mahaifiyata ta, ta bar duniya uwar Habu ta maida gurbin mahaifiya ta kina tunanin zan bar sune, bari nayi ya gama Tara mana arzikin sai na kawar da shi na share tarinhin sa a duniya Habu Jatau ya faɗa yana sheƙewa da dariyar mugun ta zaki ga yadda ake tarwatsa iyali Indo" ya idda zancan yana shafar tulelan cikin ta murmushi ta saki tace, "ai gara ka ƙwato mana ƴancin mu mai gida" "shiyasa nake sanki ido"
*Bayan Shekaru Goma (10)*
Abubuwa da yawa sun faru ciki ko har da auren da Habu yayi , auri kyakyawa kamila kuma haziƙar matar sa Hansatu sannan yayi ginin shi mai kyau, na gani na faɗa a shanono don duk shanono ba gidan bulo kamar na Habu, Hassan ma yanzu ya dawo shanono yana taya habu aiki saboda yanzu Habu ya buɗe garejin shi na kanshi.
Kamar kullum yau ma ya dawo daga gareji, ɗauke da baƙar ledar shi da Hassan, wata ƴar yarinya ce da baza ta wuce Shekara biyu ba a duniya, tana sanye da English wear's Jean's and t-shirt rugowa tayi dagudu tana cewa, "oyoyo Abba," caɓe ta Habu yayi yana ɗagata sama yana cewa, "ƴar Abban ta, cikin tsamin murya tace, "kawu ina alƙawarin mu"
"yana nan Nihal amma ki bari ina komawa gida na dawo,"
"yaushe zaka tafi kawu?
" yau insha Allah" ya ida zancan yana ja mata hanci , "ka gaishe min da Inna" "to zata ji Nihal," Umma ce ta fito daga madafi tana murmushi tace, "daga dawowar Ku ta fara cika ku da surutu, ban san ranar da Nihal zata dai na surutu ba" murmushi Abba yayi tare da ɗaura Nihal a cinya yana cewa, "zata bari ne da zarar, ta girma" "Allah yasa to,"
Ɗauke da jakar shi Hassan ya fito Umma tace, "Hassan ina zuwa kuma,? "La Umman Nihal ba jiya na faɗa makin zani ƙauye ba," "eh na tuna bari na baka wasu kaya daza ka kai wa maman Saratu tare na siya masu da Nihal" "to shikenan" haka Umma ta jido kaya kusan kala Biyar ta baiwa Hassan ya kai ma Indo.
Sannan ya ɗau hanyar ƙauye, lafiya lau ya isa gida ko da ya tanbayi Inna ina Husaini sai tace, mai yana Gona ɗakin Indo ya shiga ya miƙa mata kayan da Umma ta bashi sai murna take da washe baki da godiya, yana fitowa ɗakin su ya shige ya rage kayan jikin shi dan shiga wanka, yana fitowa suka haɗu da yaya Tanimu ya dawo daga gona, murmushi Tanimu ya saki yace, "Hassan har an dawo ganin gida kenan,"
"Eh wallahi yaya" "ai hakan na da kyau" "dama yaya Habu ya bani saƙo na baka bari na ɗauko ma," ayi haka kai da zaka shiga wanka," "ai yanzu zan ɗauko ma" ɗakin su ya koma ya irgo kuɗin da yaya Habu ya bashi yayi ya kawowa yaya Tanimu sannan ya ƙara mai da nasa a kai, godiya yaya Tanimu yayi ya shige ɗakin su.
Hassan na shiga kewaye, wata irin ƙara akaji wadda gabaki ɗaya gidan sai daya amsa, baki ɗaya ƴan gidan fitowa sukayi Tanimu ne yayi ƙoƙarin buɗe ƙofar kewayan, kwance yaga Hassan ya kakafe kwayar idon shi tayi fari fat sallati Tanimu ya ɗauka tare da sabar Hassan sai ɗaki ya kwantar da shi kafin ka ce mi gida ya ruɗe hankali duk ya tashi, Tanimu yace, "bari nayi Sauri na kira malam ata ya duba shi ko lafiya da Sauri ya shige ɗakin su yana shiga ya bushe da dariya yace, "yanzu muka fara indai wannan wasan ne yanzu muka fara, saura Husaini ya ƙara kecewa da dariya daga shi sai Haulatu daga Haulatu sai Inna daga Inna sai ya ƙara kecewa da dariya, jin an taɓa shine ya sasa razana ganin Indo ce ya san ya shi murmushi dariya indo tayi tace, "aikin ka yana kyau mai gida"
```Taku har kullun Salma mas'ud nadabo``` ✍🏻🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*Story*
*And*
*Writing*✍🏽
*By*
*Salma Mas'ud Nadabo*👑
*Edit by*:
*Aliyu Miko Muhammad*
🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
(```We are the best among the rest```)
https://mobile.Facebook.com/Real-hausa-fulani-writers-forum-RHFWF-17394973194167/?refid=52&red=opera-speed-dial&-tn_-H-R
*Email*:[email protected]
*Facebook*:www.Facebook. com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com
*Page: 17_18*
Labari na iske Husaini yana gona, ko ɗaukar keke bai tsayayi ba saboda tsabar ruɗewa, a rikice ya iso gida yana isowa ɗakin Inna ya shiga wanda ya cika da maƙota ture su ya shiga yi kamar sabon kamu, ya isa gaban Hassan dake shinfiɗe kamar gawa sai launin idanuwan sa da suka sauya, duƙawa yayi gaban shi yana cewa, "Hassan dan Allah ka tashi wannan wani irin ciwo ne Inna" yana faɗi hawaye na sulalo masa bayan numfashi da Hassan keyi baka taɓa ce mai rayayye ba, Malam Atta ne ya iso shi da Tanimu lokacin ne mutane suka fara fita sunayi ma inna Allah ya sauwake, magunguna Malam Atta ya shiga haɗawa tare da addu'oi ya shafawa Hassan sannan Husaini ya talaɓo shi aka bashi nasha wasu na shiga wasu na fita, haulatu ko ba abinda take sai kuka Gwoggo na bata haƙuri da Inna bayan malam Atta ya fito ne yaba inna addu'oin da zata rinƙa yima hassan, dan ya lura kamar gamo yayi a kewayan godiya Inna ta shiga jera mai ita da Tanimu kamar gaske, Allah sarki ba su san makashin su yana tare da su ba.
Sallamar Habu da Hansatu ne ya katse masu zance Nihal na kwance a kafadar Umma da alama bacci take, har ƙasa suka duƙa suka gaishe da Inna amsawa tayi cikin kulawa Habu ne ya miƙe ya shige ɗakin da Hassan ke kwance, shi kanshi Habu abin ya firgita shi ya tausayawa halin da Hassan yake ciki tare da yin alƙawarin duk inda magani yake zai nemomai, Gwoggo ce tasa hannu ta ɗauki Nihal tace, "ƴan'mata ana ta bacci," "aiko dai bata daɗe da dawowa daga makarantar allo ba muka taho to iskar mashin na kaɗawa bacci ya ɗauke ta," inji Umma, "Allah sarki" Gwoggo tace tare da cigaba da zancan zuciya,"lallai dole iskar mashin ke kaɗa ta tunda ga ƴar gata sannu a hankali zaku shugo hannu," mutsu mutsun da Nihal keyi ne ya katse mata tunani murmushi ta saki tare da cewa, "bari na dako mata damamiyar fura da Malam ya sha ya rage ta sha" "alalai Gwoggo kina ji da Nihal" inji Inna mudi da shigowar shi yanzu yace, "ko dai ta cuceta ba," bige mai Baki Gwoggo tayi tace, "kai dai duk wani tunani namasu hankali baka ciki"taja tsaki ta wuce ƙurya.
Ciwo hassan ko kullun ƙaruwa yake ba raguwa yake ba, komai sai amai gashi yayi wata irin rama da fari kamar ana ɗibar mai jini duk Wanda yaga halin da Hassan ke ciki sai ya tausaya mai, Malam ma duk wata addu'a da sauka ba wace ba'ayiwa Hassan ba amma kullun ciwo tsanani yake, haka rayuwa ta cigaba da tafiya wasu na farin ciki wasu na baƙin ciki, idan Habu sai samun buɗi yake yana kula da iyalan shi da ƴan uwa haka kuma duk inda yaji wani magani sai ya nemo ya kawo wa Hassan a gwada, sannan duk ya kwashe yaran Tanimu daga saratu har mudi ya zubasu makaranta da Nihal dan sun isa a sasu, duk wani jin daɗi na rayuwa haka Habu ke ma yaran ya ɗauke su tamkar shi ya haife su ko ƴa ƴan me gari baza su gwada masu jin daɗi da Hutu ba saboda Habu na zuwa birni duk wani Abu na birni na birgewa zaka Ganshi a gidan habu ko a hannu ƴa ƴan shi dan gabaki ɗaya su Mudi sun tare gidan idan ka gan su a ƙauye to weekend ne ko kuma sun je ganin kawu Hassan.