Sashe 2
Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sallamar Nihal ce ta katse masu zancen su ko ta kanta basu bi ba, sai hirar gaban su da sukeyi, gaishe da Talai dillaliya tayi cikin ladabi kawar da kai tayi kamar bata ji ba, ganin haka yasa Nihal aje bokitin koko, ta Ciro kudin dake habar zanin ta tace, Gwaggo gashi , wartar kudin tayi ta irgasu tsaf sannan ta kalli Nihal tace, wallahi naso ace kuɗin nan kabo ta bace kiga yadda zan kusa kashe ki a gidan nan", Sun kuyar da kai Nihal tayi tana wasa da yan yatsun hannu ta sannan taja jiki zata shige daƙin su, tsawa Gwaggo ta daka mata tace, "baki gamamin aiki ba ai da har zaki Shiga ciki, kayan Sara nan na jiran ki idan kin gama ki Shiga ɗakin Mudi ki gyara inda yayi amai fes, sannan ki kwaso kayan shi masu dati ki wanke, idan kin gama ga alalan rana najiranki kuma duk Wannan aikin da zakiyi karki wuce karfe ɗaya da rabi 1:30 na rana
Sara Gwaggo ta Shiga kwallawa kira fitowa tayi tana miƙa tace, "Gwaggo ina bacci duk kin bi kin dameni da kira dan Allah, kawai kin katsemin jin dadi ko kallon Talai bata ishe ta ba, bale kuma gaisuwa, murmushi gwogo tayi tace, "haba ƴar lele aini ban san bacci kike ba dama kayan wankin ki zaki ɗauko Wannan yarinyar ta wanke maki," tsaki taja sannan ta shige ɗaki ta dauko kayan ta watsawa Nihal a fuska tare da gyara tsayuwa tace, "kuma ki wanke min kaya da kyau kin ji na faɗa maki sannan ta shige daki abin ta
```Taku har kullun salma mas'ud nadabo```✍🏻
[1/7, 2:22 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*Story*
*And*
*Writing*✍🏽
*By*
*Salma Mas'ud Nadabo*
*Edit by*:
*Aliyu Miko Muhammad*
🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
(```We are the best among the rest ```)
https://mobile.Facebook.com/Real-hausa-fulani-forum-RHFWF-17394973194167/?refid=52&ref=opera_speed-dial&-tn_-H-R
*Email*:[email protected]
*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com
*Page:* 3_4
Duƙawa Nihal tayi ta kwashe kayan wankin da Sara ta Watson mata, ta kai bakin rijiya, ta ɗau guga ta soma jawo ruwa a rijiyar, kasancewar lokacin na damuna ne hakan yasa garin yayi lulumin, gashi garin hadari ya haɗu sosai, Gwoggo ce ta buɗi baki tace, "Allah yasa kar ruwan nan ya sako ya hanani cinikin rana," dillaliya ta amshe zancan da cewa, "aiko dai kinyi asara ƙullin wake gashi shi wake baya kwana," kafin ta ida rufe bakin ta aka fara yaiyafi, "a'a" Tatare kaya dillaliya ta fara tace, "to ni dai na wuce", Gwoggo da haɗa ƴan kayan da ke waje, tare da juyowa ta kalli Nihal tace, "ban ce kuma in ruwa ya sako ki shige daki ba nama faɗa mi ki, dan sai kin gama aikin ki tsaf" sannan tayi shigewar ta cikin ɗaki,
Haka aka fara tsuga ruwa kamar da bakin ƙwarya, babu yarda Nihal ta iya haka take wankin nan cikin ruwan, ga wani sanyi dake ratsa ta wasu hawaye ne suka sulalo mata masu zafi, ga kyarma da take hakuran ta na haɗiyewa, sallamar da'aka rangada ne ya sata waigowa, ba kowa bane sai Baffa, ko kallo bata ishe shi ba, sai ma Nihal dake gaisheshi, ta ƙaraso dan ta amshi kayan hannu shi, "Baffa sannu da zuwa" ta fada tare da miqa hannu zata amshi kayan, wata uwar tsawa ya daka mata, wadda tasa Gwoggo fitowa tana gyara tsayuwar zanin ta ita da Sara.
"In ban da iskanci daga dawowa na zaki tasani gaba kina cikani da surutu mara anfani, wannan ai iskanci ne," Gwoggo dake bakin kofa tace, "haba malam kayi haƙuri ka barmin ita daga dawowar ka ta saka surutu da hayaniya, ai haka take ba hankali kamar uwar tata," ta idda zancan tana shu'umin murmushi,
kallon banza ya aikawa Nihal sannan ya miƙawa Sara kayan hannu shi, Gwoggo kuma ta janyo Nihal ta fara kila "dan uban ki daga dawowar miji na zaki tare shi da bakin hali dama haka bokan naku yace kuyi kenan,? shine aikin dana saki ne,? kuka Nihal take tana cewa, "wallahi gwoggo kayan hannun Baffa kawai naje amsa ba wani abu ba," uban ki ne da zaki amshi kayan shi" sai da ta mata lilis sannan ta hankaɗanta kan ta ya daki bokitin wanki, ƙarfin kukan Nihal ne ya tsananta saboda zafin da ya ziyarci ƙeyar ta kafin kace mi jini ya fara zarya, gwoggo kuma ta shigewar ta cikin, duk irin azabar da Nihal ke sha cikin gidan duk a kunnan Umma, babu abinda Umma ke anbata sai sunayan Allah, ga wata irin yunwa da ke dawainiya da ita gashi fitsarin jiya da kashin yau duk sun hade mata guri guda.
Jan jiki Nihal tayi ta miƙe duk da jirin dake ɗibarta, baƙar ledar dake gefen ta ta kalla wadda ta debowa umma danwake gashi har ruwa ya cima ledar, kauda kai tayi ta cigaba da wankin, haka ta gama wankin tana diga, ta dauraye su ta shanya, sannan zubar da ruwan wanki ta debo wani ta aje,
Ɗakin Mudi ta Shiga in banda tashi kayan barasa ba abinda ɗakin keyi, sai tabar wiwi da ke yawo da kalbar giya a dakin, haka ta Shiga ta fara gyara dakin ga wata dauɗa dake cike a ɗakin haka ta share dakin tas, ta kwashe aman da yayi na barasa dakin ya fita fes, ta tattaro kayan shi ta wanke su tas har amai sai da tayi saboda tsabar warin giya da kayan maye.
Bayan ta kamala ne ta shige ɗakin su har lokacin ruwa bai tsaya ba, ɗakin ta Shiga gyarawa ta janye Umma ta cire mata kaya ta fidda su waje, da ƙyar ta iya jan Umma ta kaita waje ta wanke ta tas, da dan ragowar sabulun wankin, sannan ta age ta gefen rumfa ta shige dakin ta wanke duk inda umma ta bata, sannan ta dauko mata wasu kayan ta sa mata, in ban ido babu abinda Umma ke bin ta da shi gata yarinya ƙarama sai aikin manya, wasu hawaye ne suka zubo ma Umma, girgiza mata kai Nihal tayi sannan tasa hannu ta share mata hawayan ta, da ƙyar ta iya janta ta mai data ɗaki ta jinginar da ita, sannan ta ɗauko danwaken Allah yaso ruwa bai Shiga ledar ba, ta bude ta fara bata a hankali tana amsa itama tana ci sai da suka koshi sannan ta bata ruwa itama ta sha da fita ledar waje.
Dawowa tayi ta wanke kayan umma, da ta fido su duk irin qazantar dake jikin su haka ta wanke su tas ta shanya tana gamawa wani irin zazzabi ne ya lullube ta da kyar ta iya komawa ɗaki ta canza wasu kayan ta shanya jiqaqun, sannan ta zo ta kwanta kusa da Umma tana rawar ɗari,
Anyi ruwa sosai kamar da bakin ƙwarya dan ruwa bai tsagaita ba sai gab da magriba, garin yayi lum sai kukan kwaɗi dana tsintsaye ke tashi.
Kiran sallah magriba ne ya fidda ta daga ɗakin su tana kallon Baffa ya gama alwalar shi ya wuce masallaci, sannan itama ta duƙa tayi alwala ta shige ɗaki, yau dai kusan ruwa ya hana ta zuwa tallan rana dana dare dadi fal a cikin zuciyar Nihal.
Ɓangaran Gwoggo ji take kamar ta tsayar da ruwan, tsarabar da Baffa ya kawo ko har dillaliya ta dabar mawa, amma ko su Nihal bata warewawa ba, dan bata ƙiba a wayi gari sun mutu ba, da sai tafi kowa murna da jin hakan.
```Taku har kullu salma mas'ud nadabo```✍🏻[1/7, 2:22 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA* 🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*Story*
*And*
*Writing*✍🏽
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑
🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
(```We are the best among the rest```)
https://mobile.Facebook.com/Real-hausa-fulani-writers-forum-RHFWF-17394973194167/?refid=52&red=operaspeed trial&-tn_-H-R
*Email*:[email protected]
*Facebook*:www. Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com
*Page: 5_6*
Tun kafin asuba yau Nihal ta tashi, babu abin da ta soma yi face tsaftace muhallinsu sannan ta fito da Umma tayi mata wanka, ta shirya ta sannan ta jinginar da ita jikin bango, sai da ta kammala komai sannan aka fara kiraye kirayan sallah asubahi a lokacin ne al'fijir ya soma ketowa, wani irin dadi ya lulluɓe ta yau zata tafi talla ba tare da fargabar ta bar Umma cikin wani hali ba.
Fitowa tayi daga ɗakin dan daura alwala, da Baffa ta ci karo shima yana alwalar, gaisheshi kawai tayi ta cigaba da tsayuwa har ya gama alwala, banza yayi da ita kamar be ji ba har ya idar ya fita, yana fita ta janyo ruwa a rijiya tasa abuta tayi alwala.
Bayan ta gabatar da sallah tana zaune tana lazimi, duk wannan abinda takeyi Umma na jingi ne tana bin ta da idanuwa, murmushi Nihal ta zaki tace, "Umma na ina kwana," A hankali umma ta budi baki tace, "lafiya lau," matsowa tayi kusa da Umma tare da ɗora kanta saman kafaɗar Umma tace, "Rabin rai na kullun sai nayi mafarkin Abba na, yana cewa na kula mashi dake a duk halin da muke ciki," ta idar da zancan cikin sanyi murya, jin ɗigowar ruwa a fuskar tane ya sata ɗagowa, girgiza kai Nihal tayi tace, "Umma na bana so a duk lokacin da nake baki labarin Abba na ki rinƙa kuka" hannu ta kai a hankali ta share ma Umma hawayan ta ta cigaba da cewa a duk lokacin da nake baki labarin Abba na, so nake ki kasance cikin farin ciki, babu abinda Abba ke buƙata a wujen face addu'a, kuma hakan shi zai sa yayi al'fahari damu kin ji Umma na,"
Allah sarki Umma ji take dama hannuwata na motsawa da ba abinda zai hanata rungume ɗiyar tata, buɗe baki tayi tace, "Allah yasa maki Albarka Nihal,". "amin umma na,"
"ko bayan ba rai na ina so ki kasance mai aika ta aiyukan ki na alheri karki canza daga halin dana sanki dashi ƴata,"