← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 128

Sashe 80

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna isowa bakin kofa Dara tace a sanar da sultan ta maido mashi matar shi koda bafade ya shiga be dade ba ya fito tare da cewa, "yana maku iso" tun a bakin kofa Dara da su Yasmin suka juya a hankali Nihal ta shige parlour ba kowa se kamshi da sanyi AC dake ta shi a hankali ta taka har ta shige dakin tsaye ta hango sultan gaban mirror hannun shi na hard'e ta baya tsayawa Nihal tayi tana bin dakin da kallo ta kasan ido ko ba'a fada mata ba tasan dakin yasha gyara saman bed dima abin kallo ne duk an zuba red flowers a sama ga wani kamshi da dakin keyi, a hankali sultan ya juyo ya dau mintoci yana kallan Nihal a hankali ya sauke idanuwan shi saman santala-santalan kafafuwan ta dake waje farare tas da su fara takowa sultan yayi har ya zo dab da Nihal har suna jin saukar numfashin juna su a hankali sultan yasa hannu ya bud'e hula alkyabar yana bin fuskar Nihal da kallo wani irin yar sultan ya ji tun daga babba dan yatsan shi har kan shi, ga wani kyau na daban daya ga Nihal ta kara mashi, a hankali ya daura hannun shi saman alkyabar yana kokarin cire mata alkyabar, Nihal ko gaban ta banda faduwa ba abinda yake kirjin ta se sama-sama yake yana dawowa rike hannun sultan Nihal tayi ganin yana kokarin cire alkyabar tsayawa sultan yayi yana kallan ta ga wani fitinan kamshi ta na riki ta shi dan a wannan lokacin shi kanshi be san yana hakan ba, matso da fuskar shi sultan yayi dai-dai wuyan Nihal tare da sa hannu ya saki gashin kanta ya zubo har gadan bayan ta, a hankali sultan ya fara bin Wuyan Nihal yana shinshinawa har ya karaso fuskar Nihal yana kokarin hada bakin su waje daya, Nihal kuwa jikin ta rawa ya dauka take a nan idanuwan ta suka kawo ruwa, tsayawa sultan yayi cak yana maida numfashin a hankali da sauri ya zame jikin shi zuciyar shi na tsana ta harbawa Nihal da hawaye sun fara yi mata zarya jin shuru yasa ta ware idanuwan ta tsaye ta hango sultan ya juya mata baya, hakan ba karamin dadi yayi ma Nihal ba, zuciyar sultan kuwa gargadin shi take karya aikata abinda yake shirinyi lumshe ido sultan yayi wani bakwan alamari na shigar shi wanda tun tasowar shi a yau ya fara jin shi kuma kan Nihal, Nihal kuwa na ganin haka drewar ta nufa da sauri dan canza kaya jikin ta koda ta bude drewar duk irin rigar baccin ne se wayanda suka fita lalacewa, juyowa Nihal tayi tana kallan sultan dake kokarin komawa saman bed ya kwanta tace, "Sultan ina kayana mi yasa aka canza min kaya? juyowa sultan yayi cike da kasala yana kallan Nihal ya tsare ta da ido da kyar ya iya cewa, "ki zo ki kwanta please ki bar kowa ce magana se da safe bacci nake ji"
"bana iya kwana da wannan kayan ni dai ka fadi min ina kayan bacci na suke" takowa sultan yayi ya matso dab da Nihal tare da cewa, "to mi ya sami kayan jikin ki, idan ma saboda nine ba ki iya bacci da su ni da ke duk daya muke ni kallan hula nake maki" sultan ya ida zancan yana kauda kai zaro ido Nihal tayi tana cewa, "mi kace..! juyo da fuskar sultan Nihal tayi cike da bacin rai da tsiwa Nihal tace, "kalle ni" namujiya Sultan ya zuba mata tare da cewa, "Ni har yanzu kallan hula nake maki" hannun sultan na zube ciki aljihu yana kallan yadda Nihal ke maka mashi harara tsare sultan da ido Nihal tayi tare da cewa, "bari na nuna maka banbanci dake tsakanin hula da kalabi" dan a ganin Nihal sultan ba karamin ci mata fuska yayi ba ya kira ta hula ma'ana namiji nuna kanta da yatsa Nihal tace, "kalle ni da kyau ni da kai akwai banbanci, ni ba hula ba ce ka gane kalli kanka a mirror ka zo ka kalle ni" alkyabar jikin ta Nihal ta cire ta zame kasa tare cewa, "kallan ni da kyau" juyawa Nihal ta shigayi, gashin kanta ta barbaza tana juyawa sultan, ko ina na jikin ta, sannan Nihal tace, "yanzu ka ga banbancin" Nihal ta ida zancan tana kara juyi, sultan kuwa mutuwar tsaye yayi yana kallan na fulanin ta da hips din ta yadda take juya shi rintse ido sultan yayi tare da yin dana sannin kalma da ya fada dan iyakar rikitawa Nihal ta riki tashi, juyowar da Nihal zatayi ta fada saman fafadan kirjin sultan a hankali ya talabo da fuskar Nihal yana kallan ta itama Nihal kallan shi take, hada baki su sultan yayi waje daya yana mata wani rikitatan kiss, kissing din ta sultan yake kamar zakin daya shekara yana jin yunwa tsayuwar ma gagara su tayi kasa suka zube Nihal kuwa wani irin yana yi ta shiga na daban gaba daya jikin ta yayi sanyi gashi bata da karfin kwace kanta daga rukwan da sultan ya mata har suka zube kasa Sultan na kissing nata yana shinshina ta kota ko ina, a hankali ya daura hannun shi saman rigar ta yana kokarin rage mata rigar jikin ta tsayawa yayi cak idanuwan shi sun rine, kwace kanta Nihal tayi da gudu ta mike ta shige toilet ta kule kanta tana maida numfashin kamar wadda tayi tsare zamewa tayi kasan toilet dafe da kirji, jikin ta se rawa yake tsoran sultan ya lullube ta lokaci daya, sultan kuwa beyi yunkuri bin Nihal ba lumshe ido yayi yana sauke numfashin da kyar ya iya jan jiki ya hau saman bed yana jin kunyar abinda ya aikata Wanda shi kan shi be san mi ya shige shi ba, ba abinda yake bukata kusa da shi se Nihal lumshe ido sultan yayi yana cewa "Mi hakan yake nufi san ta nake koko dai sha'awar ta nake ya kamata nayi nisa da ita" rintse ido sultan yayi yana jin haushi kan shi.

har dare ya raba Nihal na toilet se da ta daina jin motsi sannan ta fito a hankali taje bakin drewar riga kawai ta gani ko dubawa bayi ba ta cire na jikin ta ta saka tare da lalabawa ta kwanta zuciyar ta na harba dan duk a tsorace take, sultan kuwa duk yana jin motsin ta ganin ta kwanta ne ya sauke ajiyar zuciya bacci ya dauke shi.

****

Bayan kwana biyu abubuwa da yawa sun faru ciki har da shirye-shiryen biki da ake ba kama hannu yaro

Amarya gyara take sha sosai ta murje ta kara kyau da haske kun san tare da Nihal mom ta hada su ana masu gyaran jiki wani kyau Nihal ta kara, Nazili kuwa kullun bakin ciki na k'ume ta musanman yadda taga Nihal ta kara murjewa ga zalla kyau da take karawa,

daga gidan waziri har gidan maimartaba hada-hada kawai ake na sha'anin biki angwaye ma ba'a barsu a baya ba suma hidama kawai su, sultan kuwa ban da tunanin Nihal ba abinda yake ko rintse ido yayi ita yake gani har mamakin kanshi yake da alajabi amma har yau ya kasa yadda da cewa ya fada kogin san Nihal.

Sultan ne zaune saman sofa a dakin Ammar ya lula duniyar tunanin Nihal wanda ya fara zamar mashi jiki ba abinda yake tunawa se moment din da suka kasance 2days da suka wuce, Ammar ne ya shigo daki hannu shi dauke da cup na coffee, murmushi Ammar ya saki yana kallan sultan yasan he's in a good mood zama kusa da sultan yayi tare da mika mashi coffee amsa sultan yayi yace "thanks dude" kara kallan sultan Ammar yayi yace, "I can see that you are in a good mood sultan, the truth is that you're in love with Nihal..! coffee din da sultan ke Shane ya kusa kware shi aje cup din sultan yayi tare da cewa, "What..! No, no, ni fa kawai ina tausayin tane and..!
"And what..! Sultan ya kamata mu fara serious magana I now kana san matar ka amma se turewa kake kana sama kanka damuwa" shuru sultan yayi tare da juyowa yana facing Ammar yace, "the problem is ban san ta yaya zance mata ina san ta ba kasan am not use to that stuff, I'm new in the system, kuma har da ina jin nauyi ta kar tayi tunani abinda ya faru 2days da suka wuce, kasan halin mata tana iya cewa ba san nake ba jikin ta nake so..! the truth is i love her from the bottom of my heart, i love Nihal so much Ammar bansan san da na fara san ta ba, I can't remember, I never thought it will be happen to me, not even in my dream Ammar"
"Please stop making this so diffcult just Architech that's normal you will soon get used to it, and I now Nihal zata so ka sultan kuma matar ka ce kana da damar fada mata ko wani lokaci, nasan ma baza tayi wannan tunanin ba" shuru sultan yayi can kuma yace, "toh shikenan zan yi trying but not now yet"

Yaune aka kawo wasu Nihal kayan ankwan da za'a sa na dinner material blue mai kyan gaske da head white daga kayan suke suna kalla kowa na gwada nashi, Basmal ce tace, "gaskiya aunty Nihal wannan rigar ta maki kyau dubi yadda ta kama jikin ki das kamar dan ke akayi ta" murmushi Nihal ta saki tana kallan mirror ita kanta kayan da dinkin sun mata dan ba karamin dinki aka mata ba minal tace, "wallahi kuwa riga ta zauna maki sosai, dayake aunty Nihal din me kyau ce" murmushi Nihal ta saki tana cewa, "kema naki sun maki kyau minal kamar dake akayi su"
"Saura mu jira lokaci" nawwara ta fada tana zuge zip din rigar ta, Aziza dake makale bakin kofa kwafa tayi tare da cewa naga yadda zaki sa kayan har ki je dinner anjima, kad'a kai Aziza tayi tare wuce wa daki Nazili.
Chapter 80 · 0% Book details