← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 128

Sashe 12

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Innalillahi wa'innailaihiraju'un ko wanne mai rai yakan zama mamaci Umma dake bakin ƙofa ce ta sulale sumammiya, Gwoggo tayi kanta da maƙota malam Jafaru ko kankame Habu yayi yana shara ƙwalla babu Wanda yayi tunanin Habu zai iya furta Kalmar shahada a halin da yake ciki, babu wanda beyi kuka ba ko Tanimu sai da jikin shi yayi sanyi saboda bayan asarrin yaci Habu baƙin cikin yasa ya haɗiyi zuciya ya mutu, gabaki ɗaya gida ya rikice da koke-koke Umma ko ana kai ta ɗaki sakwamakwan suman da tayi, tayi bari Wanda ko ita kanta bata san da zaman cikin ba, Nihal ko gabaki ɗaya ta gigice kafewa kawai tayi saboda tunda take bata taba ganin mutum yayi irin mutuwar da Abban ta yayi ba, har sai da aka sheka mata ruwa sannan ta dawo dai-dai ta daɗe tana zarana, malam Jafaru ne yayi ma Abba wankan gawa sai dai muce Allah ya jikan Abba ya gafarta masa ya saka mai abinda Tanimu yayi mai har aka kai Habu makwancin shi na gaskiya manyan unguwa na kuka yaran shi kuka ba irin Wanda basuyi ba, Wanda be san gaskiyar mutuwar su Abba ba sai suka shiga tausayawa Tanimu tare da fatan Allah ya tsare shi labari na isa wajen malam baƙin ciki da takaici ya sanya shi haɗiyi zuciya ya mutu wani saban kuka ne ya ɓalle, Umma ko har akayi kwana uku da rasuwar Abba bata san inda kanta yake ba gata nan kawai kullun cikin kuka take Nihal ko, ko bacci batayi na kirki data kwanta zata tashi a razane, Gwoggo da Tanimu duniya tayi masu daɗi dan ji suke kamar sun sauke wani nauyi a haka har akayi bakwai da rasuwar Abba da malam sannan kowa ya tafi gidan sa.

Tunda Abba ya rasu suka fara ganin SAUYIN RAYUWA duk wata dukiya da Abba ya malaka Tanimu ya Tattare ya mallake, Gwoggo ko tayi babakere a kowani ɗaki na gidan sai ɗaki daya na Abba nan Umma ke zama tana takaba, sannan Gwoggo tayi zama na musanman ta fara hure wa Sara kunne da Mudi gabaki ɗaya yanzu Sara ba ruwan ta da Nihal kowa har karshi yake ko makaranta zasu komai ya cakuɗewa Nihal gashi books ɗin ta na makaranta duk sun fara ƙarewa, dan a lokaci suna aji huɗu (4) ita da Sara.

Yau a gajiye likis ta dawo daga makaranta daƙin Umma ta shiga, Umma ta hango zaune tana sana'ar kuka wadda ta zamar mata jiki tunda Abba ya rasu faɗawa jikin ta Nihal tayi ta kwaɓe fuska ganin hakan ne yasa Umma share hawayen fuskar ta tana murmushi "Rabin rai na har kin dawo? " na dawo tun ɗazu amma naga kina ta kuka Umma dan Allah ki dai na kuka kinji" "insha Allah ba zan sake ba kin ji" cire uniform din ta Nihal take tana cewa, "Umma gabaki ɗaya books ɗina na makaranta sun ƙare dan Allah kiyi ma baffa magana ya siya min naga ya siyawa Sara sababbi kuma fa nata basu ƙare ba kuma naga idan Abba zai siya mani Abu tare yake siya min da Sara amma naga baffa ba haka yakeyi ba" ta idda zancan idanuwan ta sun cuko da ƙwalla, janyo ta Umma tayi jikin ta tana murmushi "haba Rabin rai na karki damu insha Allah idan Baffa ya dawo zan faɗa mashi nima ina buƙatar kuɗin kashewa ina so na wanke makin kayan ki masu datti," murmushi Nihal ta saki mai nuni da jin daɗin ta, ko da Baffa ya dawo da yamma da dare yayi Umma ta same shi ta mai bayani sai ya hauta da masifa da bala'i har abin ya ɗaure mata kai su da hakkin su amma ze rinƙa ci mata mutunci dan ta tanbaya haka Umma ta dawo ɗaki tana sharar ƙwalla, ga wata masassa data rufe ta ko da Umma tatashi da safe ko miƙewa bata iyawa saboda ciwo hakan yasa Nihal bata je makaranta ba tun daga wannan rana Umma ta daɗe bata tashi Nihal kuma ta fara ɗanɗana kudarta ta koma kamar baiwa a gidan ƴar makarantar boko da allo Gwoggo ta kashe mata zuwa saboda wahala gidan da talla, Umma ko in banda kuka babu abinda take, gashi Baffa Tanimu yasa an kullewa maƙota baki a wurin boka haka yasa bame tanbayar su wannan kenan.

*CIGABAN LABARI*

A hankali Nihal ta raba gefan Umma ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya.

*Asuba Ta Gari*

Yau ma kamar kullun tun kafin asuba Nihal ta tashi tayi aiyukan da ta saba na yau da kullun bayan ta kammala ta hura wuta ta ɗaura ruwan koko, yana tafasa ta sheƙa tana ƙoƙarin ɗaukar bokitin Gwoggo ta fito tana muzurai, har ƙasa Nihal ta duƙa ta gaishe ta harara ta aika mata, ",da ban kwana lafiya ba ai baza ki ganni ba, tunda nasan har fata kike mubi sahun uban ki Habu mstww, tashi ki ban gu ban san munafunci" simi simi Nihal ta ɗau bokiti ta fita, a hankali take takawa saboda fasan kafar ta dake mata zafi, tun daga ne sa ta hango yaya zaune a ɗaya daga cikin kujerun dake harabar wajen da yace ta same shi yau, tattausan murmushi ta saki tana jin yaya har cikin ran ta shima dake zaune hango ta yayi yana ta sakin smile sanye yake da jallabiya black mai hula yayi kyau har ya gaji gashin kan shi sai sheƙi yake da walwali kana gani Kasan ankashe mata kuɗi, tun da Nihal ta taho yake binta da kallo tausayin ta na ƙaralulluɓe shi ganin ta zo kusa da shine ya lumshe idanuwan shi, kamshin turaran shine ya doki hancin Nihal sauke ajiyar zuciya tayi tare da dukawa ta gaishe shi har ƙasa, "ƙanwata mi ya sami idanuwan ki sukayi ja bayan nace karki sake zubar da hawayan ki" rausaya kai Nihal tayi wasu hawayan na sulalo mata daga ta yaya, yayi yana kallan fuskarta wadda tayi ja saboda tsabar kuka janyo ta jikin shi yayi ya rungume ta tsam kamar jira take ta saki kuka mai cin rai lallashin ta ya shigayi cikin sanyin murya, " "haba sister tun jiya fa nake lallashin ki amma har yau kin kasa daina kuka please ki dai yin asarar hawayan ki Nihal" ya idda zanca yana ɗago ta daga faffaɗan ƙirjin shi yasa hannu yana share mata hawaye ,murmushi ta saki Allah sarki RAYUWA ba wanda ke damuwa da ita sai yaya ita ko a duniya da mai zata saka mai tana wannan zancan zucin baba mai gadi ya amshi bokitin dake hannu ta , zama su kayi bakin ruwa suna hira mai daɗi Nihal sai dariya take kamar ba ita ke kuka dazu ba.

*fan's am too busy kuyi haƙuri da wannan page ɗin Please*

```Taku har kullun Salma Mas'ud Nadabo ```[1/7, 2:25 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊

💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞

*Story*
*And*
*Writing*✍🏽
*By*
*Salma Mas'ud Nadabo*👑

*Edit by*
*Aliyu Miko Muhammad*

🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
(```We are the best among the rest```)

https://mobile.Facebook.com/Real-hausa-fulani-writers-forum-RHFWF-173973194167/?refid=52&red=opera-speed-dial&-tn_-H-R

*Email*:[email protected]
*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com

*Page: 29_30*

Nihal ce ta kalli yaya Wanda shima kallan ta yake tace, "gaskiya yaya wajan nan yana da kyau sosai, ina san wurin nan dubi yadda tsuntsaye ke shawagi yaya ga wata ni'ima da sanyin daɗi, amma nasan duk daɗin wurin nan bai kai birni ba yaya ko, ina so naje birni naga ƴan gayu abba ya sha faɗa min cewa wata rana tare zamu je birni naga gari amma sai ga..." lumshe idanuwa Nihal kawai tayi saboda rawar da muryar ta keyi, "ƙanwata kenan shiyasa na zaɓa mana nan dan kirinƙa samun hutu da natsuwa, maganar zuwa birni ko ki kwantar da hankalin ki insha Allah zaki je birni har ki zama wani Abu na alfahari," "yaya na kenan bana tunanin akwai ranar da zan zama haka, ka duba ka gani tallan safe da ban na rana da ban na dare da ban kabata ganin in da dan talla ya samu cigaba sai dai ya ƙare a yawo a titi" Nihal ta idda zancan hawaye masu zafi na wanke mata fuska, girgiza kai yaya yayi, "Nihal ba'a fidda rai ga rahamar Allah ƙanwata ki daina saurin yanke ƙauna akan rahamar ubangiji ki rubuta ki aje komin rintsi komin wuya zaki samu cigaba a rayuwa Nihal" murmushi Nihal ta saki tana tila dutse cikin koramar dake gudana, a gaskiya kalaman yaya na mata daɗi ko ba komai a duk sanda tana tare da shi tana samun nutsuwa, Yaya ne ya katse mata tunani da cewa, "ni ko ƙanwata ina jummala ƙawar ki? " Jummala nan bamu haɗuwa shiyasa saboda bana samun wani lokaci bale har mu haɗu da ita kuma makaranta ta boye ta, duk da nasan Jummala tsoran Gwoggo ke hana ta zuwa wuri na" "duk sanda kuka haɗu kice mata ina gaishe ta" zata ji insha Allah."

Baba mai gadi ne ya ƙaraso da bokitin Nihal ya aje yana jerawa Yaya godiya sannan ya miƙawa Yaya kola dake hannu shi mai kyau ya koma wajan zaman shi miƙawa Nihal kula yaya yayi yana cewa, "ga wannan idan kin koma gida ki samu ki ci ke da Umma karki barmin kankin da yunwa" Yaya ne ya faɗi hakan cikin sanyin murya, idanuwan Nihal ne suka kawo ruwa jikin ta na rawa tasa hannu ta amshi kular, idan zata iya tunawa raban su da abinci ita da Umma tun jiya, girgiza mata kai Yaya yake alamar kar tayi kuka buɗe baki tayi da niyar gode mashi hannu ya daura saman lips din ta alamar baya so sun Daɗe suna kallon junan su sannan Nihal ta kauda kanta, ɗan sosa ƙeya Yaya yayi yace, "lokacin tafiya gida yayi ko? daga mai kai Nihal tayi cike da shagwaɓa miƙewa su kayi a tare maƙale ƙafa Nihal tayi saboda tsamin da ta mata ga fason ƙafar ta dake ta mata zafi, yayane ya lura da yanayin da take ciki, kwala wa Baba mai gadi kira yayi yace ya siyo mashi silifas da Sauri baba mai gadi ya ƙarasa shago ya siyo yana miƙawa yaya yayi godiya sannan ya miƙawa Nihal wani irin daɗi ne ya lulluɓe ta godiya ta shiga jera masa tana tsalle tsalle dariya ta ba shi sosai saboda yadda takeyi.
Chapter 12 · 0% Book details