← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 128

Sashe 14

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Suna fita bayin Sultan suka shigo *Sinbul aga* da *Barma* wato ƴan tsali-tsali Sultan Dan kusan kullun se sun kusa sa mashi headache, harara ya aika masu sannan ya shige ɗakin shi shima dakin iyakar haduwa ya hadu royal bed yasha bedsheets me kyau da tsada gefe ɗaya dressing mirror tasha kaya kala-kala daga man gashi har na shafawa da turarur ka ba'a magana gefe guda kuma mirror ne babba tsayayye jingi ne Wanda idan ka tsaya kana ganin kanka a tsaye, dakin in ban da sanyin AC ba abinda ke tashi da kamshi, Gaban tagameman mudubin ya tsaya ahankali ya zare takalmin dake ƙafar shi bayin dake bayan shi suka ƙaraso cikin ladabi a hankali suka fara cire mashi rawanin dake kanshi masha Allah iya kar haɗuwa Sultan ya haɗu kamar balarabe sumar kanshi luf ta kwanta tasha gyara har ta gaji ga saje fuskar shi ya kwanta luf ga thick eye lashe, eye brown din shi kamar yayi carving looking extra ordinary black ga dimple kamar ansa nail da hammar anyi nailing cheeks nashi, Sultan mutum ne mai tsaho kuma murɗaɗɗe ne yana da faffaɗan ƙirji fari ne sosai har wani ja-ja yake yellow-yellow saboda tsabar fari da hutu, iya kar haɗuwa Sultan ya haɗu hannun shi ya miƙa aka zare mashi agogon dake maƙale a hannun shi da zoben shi, a hankali suka daga alkyabba dake jikin shi suka aje gefe ya rage daga shi se zabuni, daga masu hannu yayi alamar su dakata da kanshi ya idda cire zabunin ya rage daga shi se singlet itama cirewa yayi tare da miko hannu Sinbul aga ya bashi bathrobe yasa sannan yayi hanyar toilet biyo shi sukayi a baya wata uwar tsawa Sultan yadaka masu yana cewa, "wai Ku wace irin ƙwaƙwalwa gare Baku da hankali ne? Nasha faɗa maku ba yau ba, bana buƙatar wani ya biyo ni bathroom ni yaro ne da zaku biyo? Cikin rawar jiki Simbul aga da barma suke bashi haƙuri tsaki yaja sannan ya shige haɗaɗɗan bathroom ɗin shi.

Ashada na shiga part din Gimbiya Jalila yayi tili da rawanin shi yana huci juyowa yayi yana Kallan bayin shi dake take mashi baya yace, " banzaye ƴa ƴan matsiya ta ƴan iska," fisgo mawar yayi ɗaya daga cikin bayin shi yayi, ya kifa ma marwa mari har gudu uku yayi wurgi da shi gefe yace, " tsinanne kawai ni zakayi wa bariki kaga *Sultan Saleem* har da yi mashi kirari ko? fusgo shi yayi tare da matse mashi baki yana huci yace idan ka ƙara mai maita abinda kayi wallahi se na kashe ka nama faɗa ma banza" Gimbiya Jalilia ce tayi masu alama da su fice, da sauri suka fita har suna tuntuɓe, janyo shi Gimbiya tayi ta zaunar da shi tare da Koran bayin dake parlour gabaki ɗaya, wata uwar harara Gimbiya ta aika mashi tana cewa, "sokake ka gwadawa duniya halin da muke ciki ina anfanin wannan haukar da kake, dan farin jini da isa Sultan yafi babba abinda yayi ya cuce ka shine ya girme ka nace ka barmin komai a hannu na amma ka ƙi se wani zafin rai kake da na zuciya mtsww tashi ka bani guri" ta faɗa a tsawace da sauri Ashada ya tashi yana baza alkyaba yana huci.

Sultan na fitowa daga wanka ya shiryawa yayi cikin suit din shi Ash masha Allah yayi wani irin kyau har ya gaji barma ne yasa mashi cover shoe din shi black sannan ya ƙara gyara masa gashin kan sa Simbul aga ne ya miƙo mashi glass ɗin shi fari me kyau tare da ɗaura mashi agogo ya feshe shi da turare me kamshi da sanyin daɗi wani irin masifar kyau Sultan yayi, sannan barma ya dau ko briefcase din shi suka fito daga part ɗin security's na tsaye bakin ƙofa barma ne ya miƙawa ɗaya daga cikin security's din briefcake din Sultan, ajere suka fito da security's, fadawa ne suka biyo shi a baya cikin sweetest voice din shi yace, "kunsan bana buƙatar idan zani asibiti naje da fadawa ko" jin hakan yasa fadawa suka ja gefe.

Bude mashi murfin mota akayi har ze shiga ya juyo muryar Basmal tana cewa, "yayana!!. yayana!!.. tsayawa yayi cak da Sauri ta ƙaraso bayi na take mata baya, ɗan ɓata fuska tayi data zo kusa da shi tare da langwabe kai cike da shagwaba ɗaura hanuwan tayi saman face din Sultan tana cewa, " yayana baka ci abinci ba kuma har ka fito gabaki ɗaya kowa yana babba parlour yana jiran ka amma se ka fita, gashi tun ɗazu Ramlat ke San ganin ka yayana kuma na mata promise daka dawo ita zaka fara gani, daura hannun Sultan yayi saman na Basmal yace, "karki damu sweetheart zan dawo da wuri har muyi dinner tare, yanzu Ina da marasa lafiya da yawa kuma kin ga saboda su na dawo Nigeria kuma kin sani sweetheart, maganar Nazili kuma iskanci ne ya hana ta zuwa, fin Ku tayi da bazata zo tare da Ku ba part ɗina ba, ban San ranar da zata yi hankali ba mtsww," "yayana kasan tana daɗewa bata gama shiryawa ba shiyasa bata biyo mu ba" "ko" sannan yayi kissing goshin Basmal ya shige mota, a hankali motocin suka bar harabar gidan dan gwaɓe fuska Basmal tayi tare da juyawa suka shige ciki gida ita bayin ta.

```Taku har kullun Salma Mas'ud Nadabo``` ✍🏻
[1/7, 2:25 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞

*Story*
*And*
*Writing*✍🏽
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
(```We are the best among the rest```)

*_Ashe dai haka SAUYIN RAYUWA ya tara d'inbin masoya naji dadi sosai da kulawar Ku a gare ni kuma hakan ya qaramin karfin gwiwa yadda zan cigaba da suburbudo maku posting kamar yadda kuke so_*🤪

*Page: 35_36*
Chapter 14 · 0% Book details