← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 128

Sashe 18

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda Sultan ya shige asibiti ma'aikatan asibitin ke kwasar gaisuwa fuskar nan d'aure ba alamar wasa, yana isa bakin k'ofar office din shi Alex ya bud'e mashi kofa tare da mik'a mashi briefcase din shi, ya koma wajan sauran security's d'in, lumshe idanuwa Sultan yayi tare da bin office din da kallo komai neat yadda yake so, ba k'aramin haduwa office din yayi ba in ban da sanyi AC da kamshi ba abinda ke tashi, a hankali ya k'arasa bakin table tare da aje briefcase din shi ya zauna saman kujera ya lumshe idanuwa yana juya kujera a hankali ya ware idanuwan shi janyo briefcase din sultan yayi yana k'ok'arin budewa Knocking din kofar da akeyi ne yasa Sultan saki dan guntun tsaki yana ce wa, "ai fa na dawo yanzu zan fara yawo da headache saboda takura," a Dan hassale yace, "come in" a hankali aka bude kofar office din, kyakyawar budurwa ce ajin k'arshe fara take tas tana dauke d'an siririn hanci tana da yar doguwar fusaka me dauke da baki me dan girma Wanda yasha red janbaki sanye take da alkyabba white tasha aiki da Golding zare cikin alkyabbar doguwar Riga ce a ciki Golding me zananan flowers da dishi dishin stone's se kyalkyali take gashin kanta a bude yake sha gyara da wasu flowers masu kyalkyal kala-kala se kamshi take zubawa kirjin nan cike cif yake haka hips din tama cif yake ba k'aramin kyau ta zubaba k'afar ta na sanye da takalmi me tsini har se da ta shigo tsakiyar office din sannan tayi ma bayin ta nuni da su fita, kauda kai sultan yayi tare da d'aukar allura dake saman table yana k'ok'arin fita, dai-dai setin Nazili da Sauri Nazili ta fada jikin Sultan tare da k'ankameshi, kauda kai Sultan yayi ya k'ara had'e rai yana qoqarin banbare Nazili daga fafadan qirjin shi, dan murmushi ta saki tare da zamewa daga cikin Sultan tare da nad'e hannuwa ta a k'irjin ta, tana wani jujuyawa tana k'arewa office din kallo tana wani yauk'i tace, "fushi ko? dariyar gefen fuska Sultan yayi har dimple din shi na lomawa tare da k'ara matsowa kusa da Nazili har tana Shakar kamshin turaran shi da bugun zuciyar shi me rikitata yace, " "mi ze sani nayi fushi dake umm? Kawai Dan baki zo tarbana ba, idan kin ga ana fushi da Abu to an damu da shi kin gane," ya idda zancan yana killing smile din shi me rikita yan'mata, hade rai Nazili tayi tace, "kana nufin baka damu dani ba Sultan saboda ni ba Basmal ba ce ba ko , koma dai minene nima sister din ka ce kuma se na fadi ma ammi abinda ka ce," ta idda zancan tana bata fuska, ciki calm tune Sultan yace, "ba wai ban damu dake bane Nazili halin ki ne bana so," yana maganar yana shafa lalausan gashin kanta Wanda ya sauko har kafadar ta ya cigaba da cewa, you have to change your habit Nazili," tabe Baki tayi tare da zame hannu sultan dake gefen fuskar ta tace, " yanzu dai ba wannan ba ina *Ammar* tunda kayi tafiya shima yasa k'afa ya kama gaban shi Dan bana tunanin yana zuwa ma asibiti saboda da ciwo ammi ya tashi bashi ya duba ta ba," ta ida zancan cikin yanga," yamutse fuska Sultan yayi yace, "ban tanbaye ki wannan ba, kuma muyi magana da shi nasan da tafiyar kuma insha Allah ze dawo nan da 1 week ya ida zancan yana dagawa Nazili gira, fari da idanuwa Nihal tayi ciki mulki da nuna isa tace, " "to ai shikenan tunda ka sani na d'auka shirman nashi da shashanci nashi ne ya tashi," wata uwar harara Sultan ya watsawa ma Nazili yace, "look Nazili yanzu akwai aikin da nake kuma kin San bana bari ana biyo ni office da wasu surutu you have to leave and ammar ba mate din ki bane so ya kamata kisan irin maganar da kike a kanshi duk rashin kunyar da kika mashi nima zaki min so you have to be very carefully, idan kin koma gida ki ce ma ammi am so sorry da ban shigo ganina taba, am to busy shiyasa amma idan na dawo tare zamuyi dinner" ya ida zancan tare da yima Nazili light kiss a goshi ya ficewar shi ya bar Nazili kamar gunki tsaye zama tayi tana cije lips din ta, a gaskiya guy din nan Dan rainin senses ne wai yaushe ne Sultan ze daina mata wulak'anci tana fadin zancan cikin cijewar hak'ori dafe goshin ta Nazili tayi tana ce wa dole ka soni *SULTAN SALIM* dole " a fusace ta fito daga office din bayi na take mata baya kowa na asibitin bin ta yake da kallo se Sauri take alkyabba ta na tashi sama saboda Bacin rai inda sabo ya kamata ma aikatan asibitin su saba da hali Nazili dan kullun ta zo se sunyi fada da Sultan amma har yau ta kasa yin zuciya da shi maganganun kasa-kasa ma aikatan asibitin suke.

```Taku had kullun salma mas'ud nadabo```
[1/7, 2:25 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞

*Story*
*And*
*Writing*✍🏽
*By*
*Salma mas'ud nadabo*

🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
(```We are the best among the rest```)

*Page: 37_38*

Ba Alex ba hata bayin da ke bakin kofa se da suka tsorata da irin kiran da Sultan keyi ma Alex da sauri Alex ya bude kofar part din sultan tare da fadawa suka shigo, turus suka tsaya suna bin gawar Asiya da kallo suna kallan Sultan da sauri Alex ya k'araso gaban Sultan yana taba jikin shi wanda a lokaci Sultan ranshi a bace yake ko ufan ya kasa cewa Alex ne yace cikin damuwa, "Sultan hope dai ba abinda ya same ka? Katse shi Sultan yayi ta hanyar daga hannu ya fara magana cikin sanyin murya da nuna gajiya yace, "ina anfanin ku? babu ace duk security's din dake bakin part dinna har kofar daki na babu wanda yamin anfani, wai me yasa baza a barni na huta ba why tunda na taso da wayau na ake bibbiyata tunda ina 10 year na bar Nigeria saboda irin haka, aka kaini inda ba Wanda na sani se security's da na k'ara girma na fada ma yan'uwa inda nake tunda na fadi ban k'ara samun peace of mind ba, har rana me kamar ta yau mi yasa ake bibbiya tane why" Sultan ya ida zancan cikin sanyin murya Alex ne yayi hugging nashi yana shafa bayan shi yana cewa, "relax Sultan everything will be ok" sannan ya zauna da shi saman kujera lumshe idanuwa Sultan yayi yace, "miko min wayana iPhone din shi Alex ya mika mashi fadawa da bayin part din shi dake tsaye abin tausayi da security's Alex yace masu kowa ya koma bakin aikin shi sannan kada Wanda ya kuskura ya bari cikin gida sannan kowana su ya koma bakin aikin shi, DPO Sultan ya shiga kira bugu d'aya ya dauka tare da sallama dauke a bakin shi yace, "Ranka ya dade yau kai da kanka kake kira cikin daran nan Allah yasa lafiya" dan shuru Sultan yayi yace, "DPO Bilal ina San ganin ka ne yanzu a gida idan zaka so ka zo da yaran ka" ok kawai DPO yace, tare da katse kiran aje wayar shi Sultan yayi yana kallan gawar Asiya wadda ke kwance har yanzu cikin honey voice din shi yace, "Asiya mi yasa zaki min haka bayan se dana yadda dake cikin bayi na mata, har zuciya ta ta fara rayamin wani Abu a kanki sannan zaki min haka miyasa mutanan da nafi yadda dasu suke cutata, idan zan iya tunawa Asiya ke ce mutum ta ashirin dana kashe da hannun idan anzo kashe ni" yana yin maganar kamar Wanda ya zauto, wasu hawaye ne masu zafi suka wanke wa Sultan fuska a hankali Alex ya dafashi yana nuni ya kamata ya zama me dauriya kauda kai Sultan yayi shi kan shi yana ba kanshi tausayi yasan da cewa ko bayin dake gidan su da talakawan dake karkashin shi sun fishi kwanciyar hankali, yaushe ne zan samu *SAUYIN RAYUWA* yaushe goge hawayan shi yayi ya cigaba da kallan kyakyawar fuskar Asiya tare da lumshe idanuwan shi, shigowar DPO ce ta katse mashi tunani mik'ewa yayi tsaye tare da yima DPO iso turus DPO yayi tare da kallan Sultan ko ba'a fada mashi ba yasan tatsuniyar gizo mata wuce k'ok'i zama yayi sannan Sultan ya zauna tare da mika mashi hannu suka gaisa yace, " Bilal na taso ka dadare ko, haba-haba Sultan ai ba komai tunda dama aiki nane" nuna mashi gawar Asiya Sultan yayi tare da yi mashi bayani d'aya daga cikin yaran DPO ya rubuta statement akan abinda Sultan ya fada gyaran murya DPO yayi yace, "to yanzu ya za'ayi da gawar tunda nasan bakaso hankalin yan gida ya tashi,"
"da na yanke shawara ku tafi da gawar gobe se amata sutura a kaita makwancin ta, Hakan ma yayi Sultan Allah ya tsare ka daga sharin mak'iya"
"Amin Bilal"
"Amma fa gaskiya ya kamata security's din ka su dage, ya suke sake irin haka na faruwa" cikin honey voice din shi Sultan yace, "ba laifin su bane laifi nane dana ba Asiya yadda ta shiyasa tayi anfani da wannan damar, Toh shikenan kai ma ya kamata ka rage saurin yadda da mutane Sultan please wallahi aka rasaka anrasa babba mutum" dan smile Sultan yayi yace, "k'aramin mutum dai"
"Lalala kai ke ganin haka amma mu ganin babba mutum muke ma"
"Toh shikenan"
"Nifa Sultan jiki na bani yake kamar wani a cikin gidan nan ke bibbiyar ka" "I think so nima, amma har yau na kasa tabatarwa"
"Toh Allah ya shige mana gaba" "Amin Bilal"
"Bari na lalaba na wuce sani ku dauko gawar mu fita da ita" to suka ce tare da ficewa da gawar Asiya.
Chapter 18 · 0% Book details