Sashe 10
Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yau tunda safe Tanimu ya shirya ya wuce daji saboda sun yi da boka ya dawo yau, haka ya miƙe hanya yana bin daji ba motsin kowa sai tsuntsaye da mugayan haluttu, bukkace ƙwali ɗaya a dokar daji sai dariri ku dake tashi, da baya da baya Tanimu ya shige yana shiga ya zauna boka ya kece da dariya yace, "nasan komai Tanimu ka kwantar da hankalin ka nan da kwana uku Habu ya zama tarihi" ya ƙara bushewa da dariya, "yanzu haka yayi sanyi da addu'a sakamakon tunani da wasi-wasi da muka tura masa sannu a hankali zamu cimmasa, amma fa kasan idan na gama aiki na zaka bani kaso mai tsoka kuma duk abinda na tanbaye ka daga baya zaka bamu," ya ƙara bushewa da dariya, insha... Dakawa Tanimu tsawa boka yayi, "kamanta mu ba'a kira mana Allah anan, Tanimu jiki na rawa yace, " to to" "yanzu ka amshi wannan laya tayi kwana biyu a bakin ka ba tare da kaci abinci ba ko kayi sallah ba," sannan Tanimu ya miƙake da baya da baya ya fita tare dasa laya a bakin shi.
Tunda Inna ta kwanta ciwo ta fara Dan ɗan-ɗana kudarta saboda ko abinci Gwoggo ba ta bata sai idan malam na cikin gida idan ko malam nan faran faran bata samun wata kyakyawa kulawa, Habu ko be san meke faruwa ba, saboda gabaki ɗaya abubuwa sun riki ce mai suke, yau ma kamar kullun Inna ta fito daga kewaye tana tafiya a hankali, Gwoggo ta fito wani irin shu'umin murmushi Gwoggo ta saki kofar gida ta leƙa taga ba kowa sai malam shima ɗin yana ne sa da gidan, dawowa tayi ta zauna saman kujera ta yani gulma ta miƙe kafafuwa Inna ta ci karo da kafar gwoggo ta kife kasa ko kwakwaran numfashi bata sakeyi ba ɗaura hannu Gwoggo tayi a kai ta zunduma uban ihu Wanda ya jawo hankalin malam da maƙota kafin ka mi malam ya shigo gida tare da maƙota kuka Gwoggo take tana cewa, "mun Shiga uku Inna ki tashi, malam ka zo ka ga ikwan Allah," ko da malam ya ɗaga Gwoggo rai yayi halin shi take anan ya yanke jiki ya faɗi sumamme, malam Baraune da sauran muta nan dake tsaya ne suka ɗauki malam aka ida sa cikin dakin sa. Inna ko su liman ne suka ɗauke ta har aka kai Inna makwancin ta malam bai san inda kanshi yake ba, da labari ya sami Habu yayi kuka dan har kusan zaucewa yayi kafin ka ce mi gida ya kuma rikicewa da koke-koke Tanimu ko daɗi fal a zuciyar shi.
Sai da akayi kwana biyu da rasuwar Inna sannan malam ya fara dawowa dai-dai Habu ko tunanin duniya sun mai ca ga mugayan mafarke mafarke da yake wani lokacin a ranazane zai tashi sai Umma ta riƙe shi tana mai addu'oi sannan zasu koma bacci.
Kasancewa yau litinin tunda safe Umma ta tashi ta fara shirya Nihal da Sara domin zuwa makaranta bayan ta kammala shirya sune ta dawo ɗakin jingine jikin gado ta sami Habu hawaye na mai zarya a kunci, girgiza kai Umma tayi tare da dafa shi a dan razane ya waigo, cikin sauri ya fara goge hawayan fuskar shi, a hankali Umman Nihal ta fara murza mai hannuwan shi, kallan Umma Habu yayi ya aƙaro murmushin da iya karshi laban shi, buɗe baki Umma tayi zatayi magana idanuwan ta tap da ƙwalla ɗaura hannun Abba yayi saman laban ta tare da ƙara janyo ta jikin shi cikin sanyi murya yace, "mata na insha Allah bazan ƙara tada hankali na ba kin ji matata, " lamo Umma tayi a fafaɗan ƙirjin Abba tayi tana sauke numfashi a hankali dago ta Abba yayi, ya kallan ta sun daɗe a haka sannan ya ƙara matse ta a jikin shi kamar za'a sace mashi ita, "Umman Nihal wai ina Nihal ? Langwaɓe kai Umma tayi, " har ka manta yau Monday ko" murmushi ya saki yace, " mijin naki ne gabaki ɗaya ya ruɗe matana amma insha Allah zan dawo dai-dai ya ida zancan yana lakuce mata hanci, haka su Umma suka sha soyayya da Abba kamar ba zai fita wajan aiki ba amma haka ya shirya ya fita, ko da ya fita bai zame ko Ina ba sai makarantar su Nihal office din principal ya wuce tare da shedawa principal yana San ganin diyar shi Nihal principal ya sha mamakin hakan saboda ba halin Abba bane zuwa katsewa yara karatu ba, aika yaro yayi ya kira Nihal tunda aka ce mata Abba na nemanta sai jikin ta yayi sanyi, ko dai malam ne ya rasu ko kawu Tanimu duk hankali ta a tashe ta fito, tun daga nesa abba ke zabga mata murmushi hakan yasa ta saki ranta da Sauri ta ƙaraso tare da faɗawa jikin Abba, rungume ta yayi tsam a jikin shi sannan ya samu ɗaya daga cikin kujerun dake harabar makarantar suka zauna, kallon Nihal Abba yake cike da so da ƙauya na yace, "rabin raina" "na'am abba na" kin san miya kawo ni makaranta" girgiza kai Nihal tayi alamar a'a, "ba komai ya kawo ni ba sai dan na faɗa maki ki kasance mai haƙuri a rayuwar ki da ruƙo da addini rabin rai na duk halin da kika tsinci kanki ko da SAUYIN RAYUWA ne saɓanin abunda kika saba gani, bana su a duk sanda kika shiga wani hali ki manta da Allah na tare da ke Nihal " duk jikin Nihal sanyi yayi duk da a lokaci bata wuci shekara goma ba sai da hankali ta ya tashi da irin nasiha da Abba ke mata, a hankali ta buɗe baki tana sakin murmushi tace, "insha Allah Abba nama alƙawarin zan kiyaye , "yauwa ƴar Abba sannan a duk Inda kike ki zamu mai kula da Umman ki" "Abba na zan kula da ku insha Allah ko Abba" lakace mata hanci Abba yayi yace, "shiyasa nake ji dake Rabin rai na" "yeee Abba na" kyakyawar runguma ta kaima Abba ya rungume ta tsam ajikin shi wasu hawaye masu zafi suna sulalo mai saboda gabaki ɗaya ya rasa me ke damun shi, ganin Nihal na ƙoƙarin zame jikin ta yasa yayi saurin goge hawayan fuskar shi yana sakin murmushi, itama murmushi ta saki cikin shagwaɓa tace, "Abba na kaga duk kayan break ɗina sun ƙare, yaushe zaka siyo min wasu? kaga yau ma Umma kudi ta bamu ni da sara" "to shikenan Rabin raina idan na dawo daga gareji tare zamu je Ku zabi duk abin kuke so" " yee Abba bari naje na faɗawa Sara" haka Abba ya rinƙa Jan Nihal da hira mai cike da so daga nan yayi mata sallama tare da bata sweet da yawa ita da Sara.
Ko da ya isa gareji yaran shi na ta gyara, wata mota aka kawo gyara kowa ya kasa gyarata shitu ne ya ƙaraso da Sauri yace, "yallaɓai tun ɗazu Muke jiran ka an kawo gyara, yau baka fito da wuri ba," "wallahi ko Shitu Ina wurin ƴar lele tana ta zuba min surutu shiyasa ban zo da wuri ba," murmushi Shitu ya saki tare da shafa kai, suka ƙarasa har gaban motar gyaran ta suka Shiga yi, gyara motar suke sosai, kan Habu ne ya fara sarawa fitowa yayi daga ƙarƙashin motar yana dafe kai gabaki ɗaya yaran shi ca sukayi a kan shi suna tanbayar shi lafiya, shitu ne ya riƙe shi zai zaunar da shi Dan ya samu Hutu wata irin dariya ya saki yana Neman kwacewa daga ruƙon da shitu ya mai ganin abin ya wuce na hankali ya fara kiran sauran yaran gantsara mai cizo Habu yayi ya ranta a na Kare, da gudu suka bishi hauka tuburan Habu yake kamashi sukayi sai gida Umma dake zaune tana cintar wake ta juyo sallama a Zaure mayafi kawai ta yafa, mi zata gani Abba ne ke hauka tuburan su shitu sun ririƙe shi gashi ɗaure da igiya wani irin kuka ne ya kuɓucewa Umma tana kuka tana salalami, daki aka wuce da shi aka daure, sai sanbatu yake yana kecewa da dariya can sai ya fashe da kuka, Umma ko addu'oi Shiga jeramai, sallamar limana ce ta katse mata zance , shigowa yayi mai addu'oi ya bashi yasha sannan yayi shuru yana gurnani ni.
Ko da labari ya sami Tanimu yayi murna dan yau burin shi ya cika shi da Gwoggo baki har kunne Allah sarki Habu malma ne ka dai ya damu, shiryawa Tanimu yayi shi da Gwoggo zuwa shanono, kullin maganin da boka ya bashi ya zura a jaka shi da gwoggo suka ɗau hanya
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*Story*
*And*
*Writing*✍🏽
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑
*Edit by*:
*Aliyu miko Muhammad*
🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
https://mobile.Facebook.com/Real-hausa-fulani-writers-forum-RHFWF-17394973194167/?refid=52&red=opera-speed-dial&-tn_-H-R
*Email*:[email protected]
*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com
*Page: 25_26*
Ko da Tanimu suka iso shanono kukan munafunci ya soma yana mai cewa, "oh ni Tanimu wannan wane irin SAUYIN RAYUWA ne Habu, kai kuma taka ƙaddara da hauka ta zo munbani," Gwaggo ce ta amshe zancan da cewa, "Allah ya yaye mana," ƙullin maganin da boka ya bashi ya ciro a cikin jakar su yana cewa, "bari mu gwada wannan maganin muga ko zaiyi aiki" Umma dake gefe tana sharbar kuka ta miƙe ta dauko mai kwano yayi sulkulan shi ya matse bakin habu yana tirje-tirje ya ɗura mai wani malalacin murmushi ya sakar wa Gwoggo itama ta maida mai, ko da Nihal ta dawo daga makaranta taga yadda Abba ya koma tayi kuka kamar ran ta zai fita haka Sara kafin Gwoggo ta jata ta hure mata kunne, tunda Abba ya kwanta hauka komai ya lalace, shi ko Tanimu da ya zo jinya sai ya tare a garejin habu yana sa yaran habu abinda yake so, Gwoggo ɗaki guda ta hakince kafin su mamaye gidan duk wannan abinda ke faruwa Umma ko ta kansu bata bi ita dai fatan ta mijin ta ya warke.