← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 128

Sashe 69

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Babu abinda Ammar ya boyewa sultan a kan rayuwar Nihal yana bashi labarin yana mashi dressing a hannun shi daya ji ciwo Ammar ya ida zancan yana cewa, "Sultan Nihal tana bukatar ka, kai kadai ne gatanta duk yadda na so na fahimtar da kai a farko Sultan Nihal tace nayi mata promise bazan fadawa kowa ba ko ita wacece shiyasa na boye maka" sultan dake kallan Ammar jikin shi yayi sanyi idanuwan shi sun ciko da kwalla, shafa kumatun Sultan Ammar yayi yana cewa, "Nihal ta sha wahala rayuwa tana bukatar *SAUYIN RAYUWA* Sultan she need your help sultan," mikewa Sultan yayi tsaye hannu shi daya na cikin alhiju idanuwan shi sun ciko da kwalla, cikin zuciyar shi yana cewa, "Allah sarki Nihal na baki wahala na zarge ki a kan abinda ba haka bane ki yafemin, dafa shi Ammar yayi a hankali Sultan ya juyo yana kallan Ammar dake kallan shi zama yayi saman sofa saboda kan shi ya kule gaba daya be san ta inda ze fara neman Nihal ba ya kamata ya kira DPO Bilal shi kad'ai ne ze taimake su, Ammar ne yace, "Sulta...! be ida rufe bakin shin ba wayar Sultan ta hau ruri da sauri Sultan ya kai hannu ya dauka ganin bakuwar number yasa Sultan karawa a kunne yayi shuru Nihal ce rike da waya Tjee ya tsare ta da bindiga yana cewa, "idan kika bari sultan ya gane tirsasaki mukayi se na tarwatsa maki kai da harsashi zaki fada mashi abinda na ce maki koko..! wani irin miyau mai daci Nihal ta hadiye hawaye masu zafi na bin kuncin ta da kyar ta iya seta kanta tace, "hello..! sultan dake zaune mikewa yayi tsaye saboda ko a cikin magagin bacci ya ji murya nan seya gane bale kuma ido biyu, shima "hello..! yace, murya shi na rawa, marayan kuka Nihal ta saki me tsuma zuciyar me saurare ta kasa furta ko da kalma daya, ja mata gashi Tjee yayi tare da amshe wayar sultan na jin ihu Nihal zuciyar shi kamar ta fashe saboda jin kuka Nihal yake har cikin zuciyar shi, cikin daga murya yake cewa, hello..! Hello Nihal..! dif sultan yaji alamu an kashe wayar beyi kasa a gwiwa ba yayi saurin danna number amma me se ya ji kashe, a hankali Sultan ya dawo saman sofa ya zauna idanuwan shi sun ciko da kwalla yana jin kukan Nihal cikin ran shi, dafa shi da Ammar yayi yasa sultan dago idanuwan shi da kyar yana kallan Ammar da shima a rud'e yake yace, "muje police station Ammar! sultan ya ida zancan tare da mikewa yayi gaba Ammar ya bishi a baya,

fashewa da kuka Nihal tayi fisgo ta Tjee yayi tare da haska Nihal da wawan mari ji kake tas, tas, har se da ta kifa saboda taurarin da ta gani, azaba ma ta hanata kuka se haki da take ta faman yi, fuskar ta tayi butu-butu da kura fuskar ta tayi jawur saboda azaba, a hankali Nihal ta dago tana wani irin ni shi idanuwan ta sunyi jawur a hankali ta kai hannu gefen bakin ta dake zubar jini saboda tsabar marin data sha, dariya Nihal ta saki kamar sabuwar kamu tana kallan Tjee idanuwan ta jawur, ba komai yasa Nihal dariya ba se ganin shima ta bata mashi rai, janyo gashin ta Tjee yayi tare tura mata kan bindiga yana cewa, "shegiya me kama da aljanu i wish an bani damar kashe ki da sena aika ki wallahi, ni zakiyi ma taurin kai na ce ga abinda zaki fadi se ki hau kuka," Tjee ya ida zancan yana bankada Nihal kanta ya daki bango yana cigaba da cewa, "ke da Sultan ko se dai ki ganshi da wata ba dai ke ba, munafuka na tabata sultan ba san ki yake ba keke san shi mima zeyi dake me sufar aljanu mtsww, banza yar matsiya ta wadda ta gaji tsiya" Tj ya ida zancan yana jan Nihal kiii..! ya wurga ta daki me komatsai ya kule, yana ta masifa. da kyar Nihal ta ja jiki ta jingina da bango wani irin kuka ya kubuce mata ga sanyi dake shigar ta saboda yau yini tayi Tjee na sheka mata ruwan sanyi take a nan Nihal ta hau rawar dari hakoran ta na had'ewa.

A dai-dai bakin police station sultan ya faka motar shi abinda ya dade beyi ba driving da kanshi, a tare suka fito da Ammar suka shige police station, kai tsaye office din DPO Bilal sukayi masauki dauke da sallama suka shiga Bilal dake zaune yana duba file's ne ya dago fuskar shi dauke da fara'a yana cewa, "yau manyan baki ne a office din nawa" DPO Bilal ya ida zancan yana mikawa su Sultan Hannun suka gaisa tare da nuna masu mazauni kallan su DPO Bilal yayi tare da cewa, "Allah yasa lafiya dai dan naga fuskokin ku sun nuna akwai damuwa" numfasawa Sultan yayi tare da zayanawa Bilal komai ya ida zancan da cewa, "kafin mu zo nan an kira ni da number amma dana bi Layin kashe, please Bilal help me Nihal come back home save please Bilal" sultan ya ida zancan a raunane mika hannu DPO Bilal yayi tare amsar wayar Sultan ya duba number sannan ya kira office ya rubuta statement din sultan tare da rubuta number wayar, kallan sultan DPO Bilal yayi tare da cewa, "koma waye ya kira da Layin ze sake kira daga nan zamu sa tracker mu gane location din inda suke, yanzu zamu bika gida da tracker saboda kowani lokaci suna iya sake kira se muyi tracking wajan" kallan juna Ammar da Sultan sukayi sannan Sultan yace, "why not muje hotel bana so a sani a gida hankalin su ze iya tashi musanman Ammi" toh shikenan bayan sun gama tattaunawa a tare suka fito daga office din DPO Bilal da yaran shi guda biyar.

Ammi ce da fitowar ta daga bedroom kenan kallan Dara Ammi tayi dake jera abincin dare a dining ita da Aziza tana cewa, "sannu da aiki jakadiya," sunkuyar da kai kasa jakadiya tayi tare da cewa, "yauwa Gimbiya" kallan parlour Ammi tayi tana cewa, "Ni ko tun da safe ban karasa Nihal a ido na ba" Ammi ta ida zancan tana karasowa dining, Dara dake jera kayan abinci tace, "Nima tun da safe data min sallama zata je zana jarabawa ban kara data a idanuwan ba" Basmal da shigowar ta kenan jan kujera tayi ta zauna tana murmushi tare da daura Hannun ta saman na Ammi tana cewa, "Na san cewa Nihal na tare da yayana saboda yayana baya bari Nihal tayi nisa da shi ko kad'an, nima tun dazu nake cigiyar ta ban gantaba gashi ina so ta rakani shopping,"
"Allah yasa lafiya" Ammi ta fada daukar wayar ta Basmal tayi tare da fara kiran layin sultan Amma shuru be dauka ba janye wayar tayi a kunnan ta tare da ajewa, murmushi Basmal tayi tana cewa, "Ammi nafi tunanin yayana yana tare da Nihal saboda tun dazu ban gan shi a gida ba, kin gama yaki daukar Kiran hakan ya nuna suna tare suna shan soyayya" lumshe ido ammi tayi tana cigaba da cin abincin ta, mom da shigowar ta kenan taji zancan da su Ammi suke jikin ta kara sanyi yayi Dara ce ta ja mata kujera ta zauna Ammi ce ta tari numfashin ta da cewa, "Ni ko Sultan ya fadi maki ina zasu je shi da Nihal..! Da sauri mom ta dau ruwa a glass cup tana sha ta aje tana yak'e tace, "be fada min ba Amma na san suna taran ma..! Mom ta ida zancan tana kawar da maganar.

Turo kofar dakin da akayi ne yasa Nazili juyowa tana kallan Aziza hannu ta nad'e a kirji tana sanye cikin red shirt da black wando me kamar bagi kanta yasha parking tace, "kin kai ma Tjee kudin shi,?
"Gimbiya na bashi"
"ina fatan baki dau ko sisi ba,"
"Gimbiya ban dau komai ba, ya za'ayi na ci amanar ki"
"Da kyau..! aikin ki na kyau" bedside drewar Nazili ta bud'e tare da ciro bandil din 1k tace, "gashi wannan naki ne" murmushi Aziza tayi tare da amsar kudin tana juyawa tace, "Allah ya ja da ran Gimbiya insha Allah sultan ya zama naki," murmushi jin dadi Nazili tayi tana cewa, "yama zama nawan..! dama can nawan ne" Nazili ta ida zancan tana tsare Aziza da ido ita kuma tana murmushi taya Nazili samun nasara, har zata fice ta juyo tana cewa, "Gimbiya naji dazu da muna jera kayan abinci a dining Ammi na tanbayar ina Nihal? Murmushi Nazili ta saki tana cewa, "Nihal..! Ai yanzu babu wata Nihal se dai sultan da Nazili" bakin window Nazili ta tsaya tana cigaba da cewa cikin zafin rai, "zanga waze ceci wannan yarinya Nihal se na batar dake a cikin zuri'ar gidan nan.! Nazili ta ida zancan tana cije hakora sannan ta juyo tana kallan Aziza tace, "kina iya fita idan ina neman ki zan kira ki ki samin ido a kan abinda ke faruwa," daga kai Aziza tayi tare da ficewa cike da murya.
Chapter 69 · 0% Book details