← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 128

Sashe 91

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Zaune yake cikin office idanuwan shi a lumshe yana dan juya kujera da yake zaune ya lula duniyar tunani duk yadda ya so ya cire tunanin Nihal ya kasa musanman yadda kalamanta na jiya da daddare daya ke mashi yawo cikin brain din shi, dan har ji yake tamkar yanzu take fada mashi, Ammar ne ya shigo office din hannun shi rike da files tsare sultan yayi da ido yana san gano abinda ke damun shi, dan ya kusa awa yana knocking kofa ba a bashi izini ba zama yayi ciki sanyi murya da nuna tsantsar damuwa yace, "sultan..! A dan razane sultan ya dago idanuwa ya zubawa Ammar tare da cewa, "da yaushe ka shigo? numfasawa Ammar yayi yana cewa, "ya za'ayi ka sani bayan kana duniyar tunani, mike damun ka,? Sauke nanauyar a jiyar zuciya Sultan yayi yace, "Nihal..! so take san ta ya min ila..! nan sultan ya kwashe yadda sukayi da Nihal daran jiya, dariya Ammar ya saki har da buka table galala sultan ya tsaya na kallan shi sannan yace, "amma baka da mutunci ina fada ma halin da nake ciki kana min dariya" tsaida dariya sa Ammar yayi yana cewa, "kai ma kasan ai dole haka ta faru ka manta irin zaman da kukayi, dama nasan wannan rana zata zo, shiyasa na rinka hana ka abubuwan da ka mata a baya amma ka rintse ido sultan, kawai kayi hakuri ka cigaba da lallaba ta, har ta amshi soyayya ka, na san cewa tana san ka sultan ka bar tada hankali" sauke numfashin sultan yayi tare da furta, "Allah yasa..! files din hannun shi Ammar ya mikawa sultan tare da cewa, "cikin files din har da takarda taran da za'ayi a Moscow gobe" bud'e files din sultan yayi yana cewa, "ni fa ban shirya ma wata tafiya ba, ina kokarin kashe wata gobara an kunnu min wata, ni dai ban ji dadin tafiyar nan ba" dariya Ammar ya tintsire da ita yana cewa, "kuma nima ba zuwa zanyi ba, dan ban gama cin amarci na ba, kai da baka fara ci ba sai ka lallaba ka je taran nan" had'e rai sultan yayi yana cewa, "dama wani yace ka je," ya ida zancan yana kokarin barin office din Ammar ya ruko hannun sultan ganin yadda ya bata rai sosai yace, "am sorry dude koma ze sama normal karka damu kaji kawai jan aji take ma irin nasu na mata" haka Ammar ya rika tausar sultan har suka wuce theater room.

Makaranta tayi ma Nihal dadi sosai musanman da ta gane cewa Nana na gane karatu sosai se ta su ta zo daya suka kara kulewa, dan kusan tare sukayi break Nana na kara wayar mata da kai kan karatun da akayi ba ta nan, bayan komawar su break anyi lesson sosai kuma Nihal ta fahimta misalin karfe 3:30pm aka ta she su Nihal tana fitowa daga class ta hango daleliyar motar ta da Abba ya bata fake driver na zaman jiran ta ji tayi zuciyar ta ba dadi ta so a ce sultan ne ya zo daukar ta Nana ce ta daga mata hannu tana kokarin shiga motar su ita da kanna ta tace, "ki gaishe da su mama"
"zasu ji Nana" sannan Nihal ta shige mota,

A gajiye likis Nihal ta dawo gida part din su ta wuce kaitsaye watsa ruwa kawai tayi ta shirya cikin wata yellow gown dai-dai gwiwa duk da ba wata kwalliya tayi ba tayi kyau sosai da ita, sannan ta wuce part din Ammi, Ammi dake zaune ce ta washe baki karasawa Nihal tayi ta sakarwa Ammi pack a kumatu Ammi tace, "yan makaranta har an dawo kenan"
"Eh..! zama Nihal tayi saman 1 star tace, "wash Ammi na gaji makarantar akwai dadi amma da gajiya, ji nake kamar anmin duka" murmusawa Ammi tayi tana cewa, "haka karatu yake sai hakuri bari Yasmin ta zo ta maki massage" dining Nihal ta nufa ta zuba jallop din taliya taji vegetable da naman rago Nihal ta zauna tana ci, bayan ta gama ta cigaba da rubuta note din da akayi bata nan.

************

Yau dai police station sun gaji da lamarin tanimu yau kwana uku kenan kafar shi na ruwa, tana wani irin wari mara dadi har wani baki kafar tayi tamkar abinci ya rube yayi funfuna, officer garba kiran aunty Aisha yayi ya shide mata halin da ake ciki dan shi a ganin shi tanimu shingin gawa ne nan Aunty Aisha ke shida Masu bata garin officer garba yace, to shi dai ze maida tanimu kauyan sun dan sunyi bincike iya bincike sun gano bashi da sa hannu a bacewar Nihal bashi da wata masaniya inda take, haka suka kwashi tanimu zuwa shanono suna isa shanono suka watsar da shi kofar gida Sara da fitowar ta kenan zata je neman masu abinda zasu ci cikin ta har ya dan fito tayi kamar lauge saboda tsabar rama da duhu da gudu ta karasa wajan Baffa tana cewa, Baffa..! Warin da Baffa yakeyi ne ya ziyar ci hanci Sara da sauri ta toshe hanci wani tukokin amai ya yunkuro mata take a nan ta hau amai tamkar zata amaye yan cikin ta tace, "Baffa wannan wace irin cuta ce a jikin ka, warin mi kake haka sai ka ce mushe ya mutu, ni Sara ina zan jefa rayuwa ta da gwoggo zan ji ko da kai ji yadda kafar ka ke ruwa kamar ma tsutsa ke bi, na shiga uku wannan wace irin musiba ce" kuka Sara ta saki tana kwalla wa gwoggo kira da kyar gwoggo ta iya fitowa da karka ta can bakin ta, kama baki tayi da sauri ta kara sa gaban Baffa wanda shi da matace babu mara ba ga hawayan wahala na bi mashi kunci ido duk kwantsa ga taban duka duk jikin shi ya farfashe, kuka gwoggo ta saki tana cewa cikin maganar ta wanda yanzu ta zama tamkar ta kutare, "malama haka ka koma, wannan wace irin cuta ce ta same ka mun shiga uku mun lallace, Allah na gode maka da baki nane kawai ya samu matsala," Baffa kuwa ko k'ala ya kasa cewa se tsiyaya hawaye da kyar gwoggo suka ja Baffa zuwa cikin gida hanci su na toshe bisa tabarma suka shinfid'e shi, da kyar ya iya cewa, "ruwan..! da sauri Sara ta debo mashi ruwa a randa ta talabo shi ta bashi wani irin ihu ya zunduma yana cewa, "jini..! jini..! ku taimake ni ku fitar da ni daga cikin gidan nan wallahi Habu baze barni ba, ku taimake ga hassan nan ze kashe ni, usaini ze shake ni, ku taimake ni" ja da baya Baffa yake yana cewa, "ba zan zauna ba ku fitar dani daga cikin gidan nan" Sara na kuka tace, "Baffa me suka maka abirni? gwoggo sun hauka ta mana Baffa shikenan rayuwar mu ta kara rushewa" kuka sara take tamkar ta shide gwoggo jin sunayan da tanimu ke kira ya sa yan hanjin ta kadawa tamkar mazari tana ja da baya tana zaro ido abubuwan da suka aikata ya fara yi mata zarya kamar yanzu suke aikatawa ihu da Sara ta saki ne yasa gwoggo sankarewa sakwamankwan sumewa da Baffa yayi.

******
Chapter 91 · 0% Book details