← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 128

Sashe 29

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sanyi-sanyin Asuba ne ya tashi Nihal a hankali ta mike tana waige-waige jakar ta ta janyo tare da fita daga cikin gonar da sauri ba kowa a wajan se sautin kiran sallah da kukan zakaru dake tashi, gudu Nihal ta cigaba tayi dan gani take kamar har yanzu su gwoggo zasu biyo bayan ta cikin sa'a ta isa tasha motar kano da kaduna taji ana kira, aunty Aisha ce ta fad'o mata a rai tasan taje kano ta koma cikin dagin mahaifiyar ta kuma Dama tana da number ta, 1k din da Aunty Aisha ta bata ita ta curo ta mik'awa kwandasta sannan ta shige, kallan na cikin motar take kamar yadda suma suke Kallan ta kauda kai tayi saboda ta San dalili baya wuce ganin ta kaca-kace, kasancewar dama mutum d'aya ake jira yasa Nihal na shiga mota ta tashi mota na tashi Nihal bacci ya kwashe ta.

Tsaye yake gaba dressing mirror yana shiryawa cikin wata armani royel blue suit da white inner tie d'in shi kala suit d'in, ta kama jikin sa sosai wando jikin shima pencil ne sannan yasa cufflinks masu diamond royel blue stone hannu shi na sanye da agogo silver, k'afar shi na sanye cikin cover shoe black, gashin kanshi se shining yake sajan shi yayi luf-luf yayi bak'i hakan ba k'aramin fido mashi da haskyan fatar shi yayi ba kallo d'aya zakayi ma Sultan ka sake masha Allah Sultan looks so...huh yayi kyau sosai, A hankali ya tako ya bude handle d'in kofar parlour, Barma da Sinbul na zaune zaman jiran shi briefcase din shi ya mik'awa Sinbul sannan ya fito suna biye da shi se da suka fito compound sannan yace cikin honey voice din shi, "Sinbul ka wuce da briefcase dina car zan shiga part d'in mom da ammi,"
"Toh" Sinbul yace, sannan ya k'arasa parking lot.

Cikin natsuwa ya iso main parlour Mom na zaune a dining area tana break murmushi ta saki ganin Sultan, k'arasowa yayi tare da yi mata pack yace, "morning habibty"
"Morning too habibi How was ur night"
"Calm mom"
"Good amma za kayi breakfast kafin ka wuce office? ta ida zancan tana tsare shi da idanuwa saboda ta San halin shi kwata-kwata Sultan be San cin abincin gida, ta wani fanin bata ganin laifin sa ta wani fanin kuma tana damuwa sosai tabas d'an ta na fuskan ta RAYUWA Allah ya kawo mashi *SAUYIN RAYUWA* cikin gagawa Sultan ne ya katsewa Gimbiya Nadiya tunanin da cewa, "um zanyi break amma kad'an zanci"
"Good boy ko kai fa"
Murmushi Sultan ya saki har dimple din shi na lomawa ya ja kujera ya zauna kusa da mom yana cewa, "Basmal fa"
"Tana school yau tana da lecture din safe" tana maganar tana saving din Sultan paper soup din chicken with Araf bread, tura mashi plate din mom tayi tana had'a mashi tea me kauri, Kallan abincin Sultan yake kamar me jin tsoro, a hankali yake juya spoon d'in shi cikin plate d'in, mom ce ta rike hannu shi cikin calm tune tace, "ya dai my son? tsoran cin abincin kake? Girgiza mata kai Sultan yayi yana murmushin yak'e yace, " Nop kawai bana so naci da kai nane" murmushi mom ta saki sarai ta gane tunanin Sultan cikin sanyin murya tace, "OK lemme feeding" murmushi yayi har dimple d'in shi na lomawa, a hankali mom ta gutsuro bread d'in ta kai mashi baki ya amsa se da ya fara ci sannan ya wani lumshe idanuwa yana cewa, "wannan abinci kamar habibty tayi shi " dariya mom tayi tare da ja mashi cheeks tana cewa, "Ashe dai my son be manta girkin maman shi ba" ware idanuwa sultan yayi yana cewa, "na manta girkin mom d'ina ai na manta kaina" haka mom ta rink'a feeding nashi har ya cinye ya goge bakin shi da tissue, yana k'ok'arin tashi mom tace, "Sultan"
"yes habibty"
"Mi yasa baka zuwa gaishe da second mom d'in ka,? zaka je gaishe da ammi da maimartaba amma baka shiga gaishe da momi ya kamata ka gyara," canza fuska Sultan yayi yana cewa, "ita ta fad'a maki bana Shiga gaishe ta? Girgiza kai mom tayi, "toh shikenan yanzu dai inna dawo naje na gaishe ta"
"A'a gaskiya yanzu nake so ka je"
"Toh" Sultan yace tare da kissing cheeks d'in mom ya fice, part d'in ammi ya shiga zaune ya same ta saman three star tana kallo, sallama d'auke a bakin shi ya shigo murmushi ammi ta saki tana cewa, "d'an halak yak'i anbato yanzu nake ma jakadiya maganar ka" smile Sultan yayi yace, "se kuma gani na zo baki abinda baki so" tabe baki ammi tayi tana cewa, "nasan kala maitar ka ko ka tafi se ka dawo ba dai k'waya bace a cigaba da d'irkamin ai ba laifin ka bane laifin shi tsohon naka ne da be damu da uwar shi ba ana maidata yar k'waya" dariya Sultan ya ke sosai yace, "Ashe dai ammi kin San kala maitata to masha Allah tunda kin sani, kinga ba anfanin tanbayar zanzo ko ba zan zo ba," jakadiya ya kwalawa kira ta kawo mashi maganin ammi haka ammi ta rink'a sababi amma sai da Sultan ya bata magungunan tasha, har ya mik'e ze fita ammi tace, "yauwa dama ina so naje gidan hakimi bari na shirya se ku aje ni," ware idanuwa Sultan yayi yace, "Ammi da safiyar nan zaki je wa mutane gida yanzu in soyayya suke se ki katse masu jin dad'i" harara ammi ta watsa wa Sultan tana cewa, "gidan k'anin nawa ne gidan mutane? Allah ya kawo mu toh yanzu shi hakimi har wata soyayya zeyi tsofai-tsofai da shi" dariya Sultan yayi yana cewa, "ammi ko ke ce na samu wani tsoho na lik'a maki Allah ka d'ai yasan soyayya da zaki zuba mashi" d'aga hannuwa ammi tayi tana tafawa tace, "Ni bilkisu na bani rarumo pillow kujera ammi tayi ta Shiga gefawa Sultan da Sauri ya fita yana dariya yace, "ki shirya inna dawo se muje.

Part d'in Gimbiya jalila ya Shiga tana zaune da d'an lelan na ta suna break dauke da sallama a baki shi Sultan ya shigo, Gimbiya jalila da Ashad suka bishi da idanuwa, k'ak'aro murmushi Gimbiya jalila tayi cike da munafirci tace, "yau za'ayi ruwa da k'ankara" ta ida zancan tana mik'awa Sultan hannu ta kissing din hannu yayi yana murmushi, "Aini wallahi son nayi fushi kwata-kwata Baka zuwa ganina ko dan ina mahaifiyar k'annan ka ai ka zo tunda ni ban kai matsayin mahaifiyar ka ba,
"Ba haka bane hidimomi ne sun min yawa but am sorry,"
"Amma ai hidimomin basu hanaka zuwa wajan ammi ba"
"Ammi ai patient ce"
"Toh shikanan naji ka zauna muyi break mana" ta fad'a tana murmushin gulma,
"Nayi break ai "
"OK"
Kallan Ashad yayi yace, "yau baka da aiki ne" tabe baki yayi tare da d'an jingi da kujera dining yace, "kowane a ka ce ma wahalale ai kaima d'in ina ganin k'ok'arin ka da kullun kake yawan zuwa, ni dai ban iyawa tunda ni ba bawa bane, murmushi Sultan ya saki tare da had'e rai yana cewa, "Allah yasa yau karka zo wajan aiki, ka ga aiki da cikawa I don't care kana k'anina what ever takarda sallama zan baka, Se ka dawo gida ka cigaba da zama, ya fad'a tare da watsawa Ashad Harara yace, stupid boy kawai kana girma kana cin k'asa, na baka just a second kafin na isa office na ganka if not a bakin aikin ka mtsww" Sultan yasa kai ya fice.

Jar uba amma wannan yaran anyi tsinane ko mutuwa na kunyar idananuwan uwa bale wannan, kwata-kwata yaran nan be da mutunci,
"Hmm fad'i b'ana baki" inji Ashad "rabu da shi inya tsinci kan shi a kabari ze gane kuran shi"
"Yanzu dai tashi ka tafi ai dan yasan takadun ka suna da yar Matsala shiyasa yake haka, ba kowani asibitin ne zaka samu babba matsayi ba se dai a baka k'aramin matsayi, yasan da haka shiyasa yake so ya sallame ka dan bakin ciki" tsaki Ashad ya ja tare da fita ya bar Gimbiya jalila nata kunfar Baki.

Motar su Nihal a tasha ta sauka ganin fasinjas nata sauka yasa Nihal sauka rungume da jakar ta tana raraba idanuwa mutane se hada-hada suke da kai kawo, kowa harkar Gaban shi yake ko yanayin tsarin tasha ya isa ya nunawa Nihal yau ta bar kauye ta bar mahaifar ta, ta dawo birni wani wuri ta hango ida mutane ke d'an zama da alama wajan me saida abinci ne k'arasawa Nihal tayi wajan ta zauna saman tebirin rungume da jakar ta, wata yar budurwa ce zaune gefen ta da alama d'aya daga cikin yaran me se da abincin wurin ce tana ta latsa waya, cikin sanyi murya Nihal tace, "baiwar Allah Dan Allah wata number nake so ki kira min da wayar ki, ki taimaka min" Kallan Nihal tayi da niyar ta mata rashin mutucin ganin kala tausayin da Nihal tayi da yanayin da take se yasa mero jikin ta yayi sanyi tace, "toh fad'i min number" jikin Nihal na rawa ta curo takardar number aunty Aisha taba mero, ko da mero ta kira Layin kashe, haka ta rink'a kira saboda ta tausayawa Nihal musanman da Nihal ta fad'a mata daga a kauye take ita bak'uwace, haka Nihal ta rink'a zama mero na janta da hira kusan tare suka ci abincin mero har yamma tayi shuru Layin aunty Aisha ba ya Shiga har su mero suka tashi.
Chapter 29 · 0% Book details