← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 128

Sashe 122

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Washe gari da safe bayan Nihal tayi wanka ta cancada ado cikin wata black after dress din da mama ta bata mai kyan gaske, kayan breakfast mama ta mika mata a tray ta kai wa sultan bedroom dan ta lura kunyar su yake ji tun jiya, cike da kunya Nihal ta amshi tray din ta nufi dakin.

Dauke da sallama Nihal ta shigo dakin sultan dake tsaye gaban dressing mirror yana shiryawa ciki wata white jallabiya yana kokari makala agogo a tsintsiyar hannu shi, murmushi mai kara mata kyau Nihal tayi tace, "ina kwana love"
"lafiya lau hayaty" sultan ya ida zancan yana amshe tray din hannu Nihal ya aje saman stool sultan ya jawota jikin shi ya ce, "wato ke dadi yan uwa yasa gabaki daya kin manta dani daran jiya na kasa bacci saboda missing na ki" dan murmushi Nihal tayi tana hada mashi tea tace, "nima nayi missing naka love"
"ba wani kinyi missing nawa na kira ki yafi a kirga baki dauka ba ko good night baki min ba"
"Love ni kai na ban san ina na aje wayar ba ina tunanin a parlour na barta" Nihal ta ida zancan a shagwabe "toh shikenan muna nan dake zan kwace su mama su zama nawa di kad'ai" dan karamin bakin Nihal ta turo cike da shagwaba mintsine mata baki Sultan yayi yar kara Nihal ta saki mai cike da shagwaba hada bakin su sultan yayi yana kissing nata sannan ya sake ta dan kan shi yana cewa, "yanzu ya daina zafi ko" daga kai Nihal tayi tana feeding sultan breakfast.

Bayan sun gama karyawa gabaki daya muta nan gidan suka dunguma zuwa gidan maimartaba, cikin mutunci da mutuntawa maimartaba ya tarbe su haka su mom su baba sani sunyi godiya sosai nan maimartaba ya kara gwada masu ba komai duk yima kaine, Ashad kuwa kan shi kato ya karayi dan gani yake tamkar ya malaki Nana a matsayin mata wunin ranar zungur cikin nishadi da jin dadi sukayi shi musanman Nihal tafi kowa murna wannan rana.

Bayan kwana biyu rayuwa ta cigaba da tafiya cikin jin dadi inda su Nihal suka kamala jarabawar su ta SSCE Nihal ta amshi kyaututu ka sosai ranar speech and prizes giving day Amal da nawwara ma sun dawo gida, gidan sai ya kara dadi ya kara kacamewa.

Bayan kamala jarabar su Nihal da wata biyu Basmal ta haifi baby boy din ta ranar suna ya ci suna waziri ana kiran shi da khalifa, murna wajan wannan family ba'a cewa komai Nihal kullun tana part Adda kasancewar a nan Basmal ke wanka, Sara ma ta zo suna a ranar suna ta hadu da wani abokin Ammar wanda matar shi ta rasu ta barshi da ya'ya hudu tunda ya kyala ido yaga Sara hankali shi ya kwanta da ita.

Washe garin suna koda zata koma shanono shi ya kaita har yana cewa shi bada wasa ya zo ba, so yake ayi bikin su bada jimawa ba tunda shi ba saurayi bane, Sara kuwa ce mashi tayi zatayi tunani a kai, dan tana jin tsoran sake mashi kar yan kauye su falasa abin kunyar data aikata ko shanono daya kawo ta bada san ranta bane, su Nihal ne suka matsa mata suna nuna mata Sunusi yayi ita kanta ta san yayi dan sunusi ba ajin ta bane kwata-kwata dan dai so ba yarda baya zuwa.

```Taku har kullun salma mas'ud nadabo`[3/10, 2:14 PM] salma😝: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA* 🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*Story*
*And*
*Writing*✍🏾
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
(```We are the best among the rest```)

*Page: 139_140*

Bayan suna da kwana biyu Gimbiya jalila ta sami maimartaba kan maganar Nana sosai maimartaba ya ji dadin zancan, dama Sultan ya zo mashi kan maganar Sunusi dake neman Sara sai a had'e bikin ayi lokaci daya, Gimbiya jalila ta dan jima a part din maimartaba suna tattaunawa da maimartaba kasancewar ranar girkin ta ne.

Nazili ce tsaye a bedroom nata da alama yanzu ta dawo daga wajan aiki wayar ta dake cikin handbag ce ta fara ruri, inda sabo ya kamata ta saba da wannan kira da ake mata da bakuwar number, ko ta dauka ba a magana d'an siririn tsaki ta ja tana kokari wurgi da wayar, turo kofar da akayi ne ya katse mata hanzari, Aziza ce ta shigo kai sunkuye ta ce, "ran ki ya dade maimartaba yace ki same shi a fadda" jim kadan Nazili tayi tana mamakin wannan kira da maimartaba ke mata a hankali ta furta, "gani nan zuwa" jiki a mace ta canza kaya zuwa duguwar riga blue har kasa ta saka silver alkyaba ta wuce fadda.

Zaune saman kujera mulki ta sami maimartaba zaune, ciki ladabi Nazili ta gaishe da maimartaba dake zaune, har sai da yayi mata nuni da mazauni ta zauna har a lokaci gaban ta na tsana ta faduwa ya ce, "Nazili..! Nazili...! yanayin yarda maimartaba ya kira suna ta yasa jikin ta mutuwa mudus dan maimartaba bai fiye kiranta da suna ta ba, kara kiran suna ta yayi karo na uku dagowa Nazili tayi ta maida hankalin ta kan maimartaba tana wasa da yatsun hannu ta ya ce, "sau nawa na kira suna ki?
"sau uku Abba"
"Ina fatan abinda zan fada maki zai zauna a kunna ki, tun ba yau ba nake maki magana kan ki fito da miji kiyi aure amma kin rintse ido ke a'a, har Ammi tayi magana ta gaji har ta zuba maki ido haka ni ma saboda bana san takura maki na matsawa d'iyar da tafi soyuwa cikin ya'ya na koda mahaifin ki na raye ba zai zuba maki ido haka ba, na sha baki lokaci dumin ki fido da wanda ya kwanta maki a rai kuka dai-dai ta kan ku amma naga alamar baki da niyar yin aure kin fi ganewa ki dinga fita zuwa kasashe kasuwanci kina neman kudi tamkar namiji..! abubuwan da kike sam ba al'adamu bace, ba tsarin mu bane na gidan saurata da mulki, anfi sannan ya'ya mu da zama gida da kamun kai duk abinda kike ina sane zuba maki ido nayi, naga yaushe zaki natsu amma naga ba rana to bazan lamunci hakan ba, na riga dana yanke hukunci zan hada ki da wanda hankali na ya kwanta da shi yanzu haka mun gama magana da magabatan shi....! tare za'a hada bikin ki dana Ashad" a razane Nazili ta dago tana kallan maimartaba wanda ba alamar wasa a fuskar shi idanuwan ta cike ta kwalla, kasa tayi da kanta maganar maimartaba ce ta kara katse mata tunani da cewa, "kina iya tafiya ki fara shirye-shiryen biki" Nazili da jikin ta ya mutu murus idanuwan ta cike da kwalla ta ce, "Abba yanzu wanda ban sani ba za'a aura min Dan Allah a karamin lokaci,"
"Zaki san shi kafin biki ni dai fata na kimin biyaya na yaba da hankali shi kuma ya cancanci abinda ya fi haka awaje na" zata kara magana maimartaba ya katse mata hanzari da cewa, "kin san dai bazan zaba maki abinda zai cutar dake ba dan haka na gama magana" Nazili da gwiwa a sage ta mike jiki a sabule cikin ladabi ta fice, hawaye na mata anbali tana jin tsanar wanda yayi wannan katobara na cewa ita yake so, aiko zai aurawa kan shi masifa da bala'i, kuka take sosai tana mamakin yarda rayuwa ta sauya mata daga farin ciki zuwa akasin haka, tir da irin wannan SAUYIN RAYUWA yanzu haka ma ko za'a tsare ta da wuka zaman da ake yanzu bata da wani saurayi sai dai friends da abokan kasuwancin ta, yaushe ma ta tsaya tayi soyayya ta riga da ta daurawa zuciyar ta san Sultan hakan yasa idanuwan ta suka rufe bata ganin samari a wata tsiya, gashi yau ta kare mata har ita za'ayiwa auran dole ko wani irin matsiyaci za'a aura mata da wannan tunanin Nazili ta wuce garden tana kuka fad'awa tayi saman resting chair ta zauna tana kuka tana cewa, "why me why Abba mai yasa ake so a rusamin farin ciki na," surutai Nazili kawai take, bata lura da wanda ke wajan zaune ba, ba kowa bane sai Ahmad dake shan iska hannu shi rike da cup da alama coffee yake sha sanye yake cikin shirt blue da wanda suit yayi kyau har ya gaji, ya kara haske ya fito zalan baturan shi kasancewar bai dade da dawowa naija ba, dan shirye-shiryan komawa US yake gabaki daya saboda kasar shi na bukatar shi kan wani aiki na kula da Mr President.
Chapter 122 · 0% Book details