← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 128

Sashe 117

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

lokacin da Sara ta farfado daga doguwar sumar da tayi koda taji labarin mutuwar baby tayi kuka wanda bata iya gane na bakin cikin ne kona farin cikin, wani bangaran na zuciyar ta kuwa ce mata yake kara da baby ta mutu saboda kyara da zata sha cikin al'umma ma kad'ai ya ishe ta, Dara nata lallashin ta da su Ammi sannan Dara ta tashi ta share gidan kwal da daki da Sara zata zauna wankan jego sannan suka shige gabaki daya su, Sara dai na zaune har a lokacin tana matsar kwalla su Ammi nata ban baki Nazili kuwa zaman duk ya ishe ta haka nan take daurewa duk ta matsu su tafi, kayan haihuwar Dara ta wanke tas, ta shanya ta hura wuta ta daura ruwan wanka, mom ce ta fita ta shedawa bafade ya samu masu ganyan bedi sai da suka gyara gidan tsaf ko ta kan su Baffa da gwoggo basu biba, sannan mom tace bari su je asibiti duba lafiyar Nihal Sara dake kwance ji take tamkar ta bi su taga lafiyar Nihal din, da sauri Nazili ta mike tayi gaba ga wayar ta dake ta faman ringing ta rasa wake kiran ta da new number yana takura mata cikin wanakin nan, suna fitowa waje suka sami Ashad yana waya da Nana sai zuba mata soyayya yake har yana cewa da sun dawo ze turo manya cike da shagwaba tana ce mashi ya bari sai tayi candy Ashad na cewa baze iya jira ba har nan da shekara daya ganin su Ammi ya sashi katse wayar yana smile, sannan suka shige mota gabaki daya dan zuwa asibiti aka bar Dara da Adda a gida suna kula da Sara.

Nihal ce zaune sultan na feeding nata abinci hankali kwance sai shagwaba take zuba mashi sai ya zo bata abinci sai ya kauda spoon din yana dariya tana bin hannu shi tana turo baki, Ammar dake zaune Basmal ta daura kanta saman fafadan kirjin shi yana game da waya sai dariya suke masu suna cewa, "wallahi lafiya ta samu ya kamata su bar asibitin haka kafin yan kauye su ce an kawo masu yan iskan patients asibiti dama dazu da wata nurse ta shigo sai kallan su take tana zaro ido" dan shari na Basmal cewa tayi sultan ne ya mata" turo baki Nihal tayi tana cewa, "wallahi ya Ammar ta gani dama ta lura tunda ta shigo ya Ammar ke bin ta dana mujiya" dariya sultan yake yana kokarin cirewa Nihal drip din hannun ta ya ce, "to kin ji darling mijin ki ne ke kallan ta" zaro ido tayi tana kallan Ammar tace, "wai da gaske? Ammar zaro ido shima yayi yana cewa, "daga taya ku jinya sai a fara a hadi da matata tashi mu tafi mu kyale su tunda abin nasu har da sheri" dariya Nihal take har da hawaye musanman yarda Ammar yake magana a susuce dariya sultan yake tare da cewa, "hayaty kin hada mata da miji kina dariya ko, sai na ci je ki" sultan ya ida zancan yana dan ji ne mata kunnu ne yar kara ta saki mai cike da shagwaba, lakace mata hanci sultan yayi yana kissing din ta ko ta ko ina tana dariya, Ammar yace, "wallahi sultan baka da kunya na rasa ina ka aje kunyar ka" ya ida zancan yana wurga mashi bedsheets dake kusa da su dariya yayi yana cewa, "ai tana samun rest zan dauke abita mu cala ko hayaty? daga mashi kai Nihal tayi tana rike da hannu sultan sallama su maimartaba ce ta katse masu tunanin da sauri Ammi ta karaso bakin bed din tana cewa, "ya jiki Nihal sai muka ji ba kya jin dadi," Nihal da kanta ke sunkuye tace, "da sauki sosai,"
"masha Allah" nan mom da Gimbiya jalila suka matso suna mata sannu har da Nazili Ashad ma ya mata ya jiki na suka zauna suna ta nan da Nihal ko motsi tayi kad'an a tanbaye ta lafiya ko tana jin wani abu musanman mom dake tatalin cikin Nihal, haka Nazili ta saki jikin ta sosai wannan karan ba wani girman kai da nuna isa cikin su ta shiga anata zuba hira kiran sallah magrib ne ya tashi mazan zuwa masallaci matan ma suka fara haramar dauro alwala.

Kwana biyu Nihal ta kwashe a asibiti saboda bed rest da aka bata suka dawo masaukin su bayan sun dawo ne Gimbiya jalila ke bama Nihal labarin cewa, Sara ta haihu abinda ta haifa be zo da rai ba Nihal bata jin dadin hakan ba, amma ta wani fanni taji dadi hakan dan tana bakin cikin a nuna yar uwar ta tayi cikin shege bare kuma ace ga diyar na raye mutuwar shine jin dadi su su duka duk da ba lalai fentin ya goge a zuri'ar su ba, amma bata jin zata iya zuwa gidan duba ta saboda har yau bata daina jin suyar abinda Baffa ya aikata ba Gimbiya jalila kuwa dama gulma ce ta ciwo ta, ta fesawa Nihal ganin ba'a da niyar fada mata shiko sultan bari yayi ta samu natsuwa sosai sai ya fada mata.

Bayan kwana biyu abubuwa da yawa sun faru ciki har da shirye-shirye komawa kano da suke amma Dara shanono za'a barta har sai Sara tayi arba'in zata dawo, cewan Baffa kuwa ya kara tsanani, gwoggo kuwa hauka ba kama hannu yaro.

Yau dai kam Sara ta gwadawa Dara tana san zuwa taga Nihal kodan ta kara neman gafara ta, tayi mata bankwana tunda gobe zasu wuce kano duk yarda Dara ta so ta hana ta sai ta gama wanka zata fara fita, amma Sara ta gwada tana san zuwa kodan tafiyar da zasuyi, ganin haduwar ta su nada mahimmanci yasa Dara cewa "to idan bala driver ya zo kawo min kaya na sai ki bishi ku je," cike da murna ta shirya cikin kodadiyar atamfar ta da hijab din ta tasha ruwa ta gaji bala driver yana zuwa kawo wa Dara kaya Sara ta bishi.
Chapter 117 · 0% Book details