← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 128

Sashe 20

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gwoggo ce tsaye ke huci kamar kumurci tana bin Nihal da mugun kallo wadda ta jik'e sharkaf, cike da masifa gwoggo tace, "yo in ban da iskanci ke ma se kin kwanta kiyi bacci ki Hutu ko tunda ga abiyar wasan ki na bacci, maza-maza wuce ki daura ruwan koko kafin inci uban ki la'ada waje," jikin Nihal na rawa simi-simi ta rab'a ta gefen gwoggo zata wuce wani irin wawan k'uli ta sakar mata a baya har sai da Nihal ta gantsere ta fito da sauri waje kamar an tulo ta, Sara ce ta watsa mata harara cike da tsiwa tace, "wallahi tallahi naje makaranta aka min dukan lati na dawo gida kanki zan sauke, shashashar banza wadda bata San anfanin ilimin ba, mtsww kuma ga kaya na can sunyi dati ki tabata indan kin dawo daga talla ki wanke min su in ba haka ba jiki yayi tsami," idanuwa Nihal taf da hawaye ta duka tana hura wuta ko cikan ki bata ce ma Sara ba se ma umma ce da ta fado mata a rai, "Allah sarki umma na bata iya tashi bale har ta canza kaya ko ta tsane ruwan da gwoggo ta watsa masu, wasu siraran hawaye ne suka wankewa Nihal fuska da ace Abba nada rai da zasu kasance cikin gata da jin dadi Allah sarki rayuwa bayan hannun ta Nihal tasa ta goge hawaye da ke zubo mata a fuska kamar ruwa duk tana wannan zancan a zuciyar tane, a haka ruwa ya tafasa ta juyewa sara na wanka sauran ta shek'a koko da su.

Duk yadda taso ta lek'a dakin su kafin ta tafi talla abin ya gagara saboda gwoggo ta kasa ta tsare tana bin ta da mugun kallo mai cike da tsana, a haka ta ja yan'mata kafafuwan ta bakin kofa taci karo da baffa yana k'ok'arin shiga gida dukawa tayi har k'asa tana gaisheshi wani kallo ya watsa mata tare da Jan dan siririn tsaki, shi wallahi har mantawa yake iyallan Habu na raye se da yaga wannan maya sannan ya tuna, haka dai zasu k'are a rayuwar su wannan fadar malam ce ya ida shiga gida, wani irin kukane ya kubucewa wa Nihal zaman dirshan tayi a k'asa tana shekar kuka Wai ita yaushe ne zata samu *SAUYIN RAYUWA* Allah sarki Abban cikin yar siririyar muryar ta Nihal tace, "Allah ya ji k'anka Abba" sannan ta tashi da kyar ta fara takawa.

A harabar asibiti motocin Sultan suka faka kamar kullun, Alex ne ya zagayo ya bude mashi murfin mota a hankali ya zuro k'afafuwan shi tare da fitowa gabaki daya, cikin isa da mulki yake takawa Idan ka kalle shi se ka sake kallan saboda kyan irin na sultan da natsuwar shi Alex na biye da shi da briefcase din shi, suna isowa bakin kofa Sultan ya amshi briefcase din shi ya k'arasa cikin office.

Gimbiya jalili ce zaune yakumbo na zuba mata kirari wato baiwar ta, kuma yar gaban goshin ta wadda suke hada makirci tare, tabe baki Gimbiya jalila tayi tare da gutsura Apple din da ke hannu ta yakumbo na mata massage tace, "Allah ya k'ara nisan kwana Gimbiya ba Wanda ya isa ya ja dake, ke ce a gaba ke ce a baya kinyi babakere kin hana yan' uba," wani irin murmushi Gimbiya jalali ta saki tace, "Na baki kujera makka yakumbo," godiya yakumba ta shiga jera mata daga mata hannu tayi Alamar ya isa tana murmushi tace, "kin San Matsala ta yakumbo? girgiza kai yakumbo tayi gimbiya ta lumshe idanuwa tana shakar iska tace, " Sultan shine matsala ta yaran nan Allah ya zuba mashi taurin rai kamar fir'auna, na rasa yadda zanyi naga bayan shi, kwata-kwata Gimbiya Nadiya bata dace ta zama mahaifiyar sarki ba, ni na dace na zama ki duba ki gani yakumbo ya'ya na maza biyu mace daya,"
"Haka ne ranki yadade"
"Ita fa nadiya namijin ta daya mata biyu, wacece a cikin ta dace ta zama uwar maza" Gimbiya Jalila ta ida zancan tana lumshe idanuwa, murmushi yakumbo ta saki tace, "ranki yadade ba wadda ta dace da ta zama mahaifiyar sarki kamar ki Gimbiye" tabe baki Gimbiya jalila tayi tace, "Ni fa kashe sarki a waje na Abu me sauki ne, amma kashe Sultan shine babba tashin hankali na tun yana ciki yake zuba min taurin kai gashi kuma har ya zo duniya, dana kashe shi zan kawar da sarki Ashad ya hau kujera Mulki Nadiya da ya'ya ta mata suyi waje" ta ida zancan tana sakin dariya tare da saka faru a bakin ta murmushi yakumbo tayi tare da tasowa dai-dai saitin Kunnan Gimbiya jalili tana mata rad'a sannan taja kefe kai sunkuye murmushi Gimbiya jalila ta saki tace, "Na baki kit d'ina daya na gold" zubewa k'asa yakumbo tayi tana godiya Gimbiya jalila ta d'aga mata hannu.

A hankali Nihal take takawa har ta karaso wajan da suke haduwa da yaya tun daga nesa ta hango yaya zaune saman resting chair, ba k'aramin kyau ya zuba mata ba sanye yake da jeans n tshirt Jeans din black riga white me dan k'aramin hannu gashin kan nan nashi luf-luf yasha gyara ga wani irin ni'imatacan kamshi da yake zubawa tun kafin ka k'araso wajan sa, tun da ya hango Nihal yake ta washe fararan hakoran shi k'arosawa Nihal ce ta sashi mik'ewa har lokacin Nihal kanta na k'asa, a hankali ya karaso daf da ita tare da sakin smile yana k'ok'arin sauke ma Nihal bokitin koko har a lokaci Nihal bata dago idanuwa taba, a hankali yaya yasa hannu ya dago da habar Nihal yana kallan kyakyawar fuskata, wasu siraran hawaye ne ke sulalo mata, cikin calm tune yaya yace, "k'anwata mi aka maki waya taba min ke hala gwoggo ce, mi ya sami kayan ki suka jik'a duk wannan tanbayoyin yaya yake jerawa Nihal wani irin kuka Nihal ta saki tare da fad'awa jikin yaya ta kankame shi tana sakin kuka, gabaki d'aya jiki yaya sanyi yayi, ji yake kamar an sare mashi laka tsayuwar ma neman gagare shi take, daurewa yayi ya janyo kuzarin shi cikin kasalaliyar murya yana shafa bayan Nihal tayi shuru yace, "k'anwata kiyi hakuri kinji wata rana se labari insha Allah everthing will be ok my dear kin ji" d'aga kai kawai Nihal tayi tana sauke ajiyar zuciya, sannan ta zame jikin ta daga na yaya hannuwa ta ya rik'e har suka k'araso resting chair suka zauna yaya na kallan ta cike da tausayi.

Zaune yake yana dana system idanuwan shi manne da glass knocking din da ake ne yasa Sultan yace, "come in" cikin honey voice din shi sister Naja ce hannu ta dauke da files tana smile tace, "yallabai ina kwana dago idanuwa Sultan yayi tare da amsawa ya zuba wa files din hannu Naja sexy eye's ball din shi yace, " Naja ya kamata Ku fara sa tausayi alamarin nan ban gama da wasu ba se a k'aro wasu, please Ku aje sauran Idan ammar ya dawo ya amsa,"
"to shikenan Doctor yadda ka ce haka za ayi"
"Ga files din nan na saman file din na Alhaji barau ne Wanda za'ayima operation da misalin karfe 10:00am" hannu Sultan yasa ya amsa tare da gyara zaman glass din shi ya bude file din yana dubawa sannan ya aje a gefe, tare da mik'awa Naja wasu file's din yace, ga wad'an nan na gama da su a ki kai su store ki je"
"Ok"
"Sannan ki fada masu doctor bashir su shirya kafin 10:00am"
"OK Doctor" har tayi gaba Sultan yace, "and kema ki shirya tare zamu shiga theater room"
"Toh shikenan" sannan Sister Naja ta ja mashi k'ofa ta fice.

Agogo dake mak'ale a bangwan office din ya kalla kusan karfe goma saura minti 15 suit din shi ya cire tare sasauta nicktie din shi ya nanad'e hannu rigar shi toilet ya shiga ya dauro Alwala, sallah ya gabatar raka'a biyu ya dad'e yana addu'a Allah ya basu nasara kan operation din da zamuyi sannan ya sallame sallah.

A hankali ya murda handle din kofar office din shi ya fice wani daki ya Shiga dake kallan office din shi, gabaki d'aya d'akin zagaye yake da mirror kowani zing d'aya yana da mirror tare da yar k'aramar loka a gefe, murmushi Sultan ya saki ganin sauran doctor's din suna shiryawa yace, "Har kun shigo kenan" bashir yace, "Eh" a takaice, makule Sultan ya Ciro ya bude loka shi sannan ya Ciro kayan da suke sawa Idan zasu shiga operation, se da ya fara cire zube hannun shi da agogo ya tura a loka sannan ya fara shiryawa, masha Allah haka suka shirya tsaf kallo d'aya zaka masu kasan sunsan abinda suke, Sultan ne ya fara fice wa sannan su bashir suka biyo bayan shi abin sha'awa, dakin da aka kwantar da Alhaji barau ya shiga Hajiya ikilima na gefe Alhaji ta zabga uban tagumi sallamar sultan ce ta katse mata tunani amsawa tayi, sannan Sultan ya tanbaye ta me jiki, da sauki tace a taikece bakin gadan Sultan ya k'arasa yana sakarwa Alhaji barau murmushi yace, "Insha Allah yau zaka samu sauki" yana maganar yana zuk'o alura dake Hannun shi, murmushi Alhaji barau ya saki yana cewa, A hankali "dana ji dadi," alura Sultan ya mashi yana murmushi sannan yazo setin fuskar shi yana nuna mashi finger's din shi daga d'aya zuwa biyar ganin bacci yayi gaba da shi yayi mu bashir magana su dauke shi, gado suka canza mashi tare da Jan wancan suka shiga theater room suna shiga red danja ta kama, hajiya ikilima se zarya take a waje Allah ya ganin tsoran aikin yan Nigeria take Dan dai ba yadda zatayi Alhaji yace se nan Wai likitin k'wararene wacece wata tsiyace, to wallahi ta dau alwashi duk abinda ya sami mijin ta kotu ce zata rabasu da asibitin.
Chapter 20 · 0% Book details