← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 128

Sashe 100

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gimbiya jalila ce ke zagaye daki ban da tsuma ba abinda take tace, "yakumbo kin ga fuskar yaran nan kuwa wani kallo daya watsamin sai da hantar ciki na ta katsa," Ashad yace, "dama tunda naji shuru na fada maki akwai matsala, hankali na be kwanta ba hakan na nufi ya gane da sahannu mu, ban san da wani ido zan kalle shi ba gobe zan hada kaya na, na barka kasar nan da ba zan zauna ba har Abba ya ji labarin abubuwan dana aikata tare da sa hannu ki momi" Ashad ya ida zancan tare da ficewa part na shi ya shiga ya bud'e drewar ya fara loda kaya cikin trolley maganar data doki dodan kunna shi ce ta sashi dagowa a razane yana kallan sultan "ina zaka je a tsohan daran nan? bakin shi na rawa yace, "uhm, uhm, yaya da yaushe ka dawo?
"yau na dawo,"
"am....!
"Zuwa nayi mu sha coffee mun dade bamu gana ba" sultan ya ida zancan yana jan hannu Ashad daya sankare suka fito parlour se zare ido Ashad yake yana hadiye-hadiye sultan ya zauna da shi ya shiga hada masu coffee Ashad na bin shi da ido zuciyar shi na lugude dan bakin shi ya mutu mudus, sugar sultan yasa yana juya coffee ya juyawa Ashad baya idanuwan shi cike da kwalla ya mikawa Ashad cup ba tare da ya bari sun hada ido ba, jikin Ashad na rawa ya amsa yana rike da cup din ya kasa shan coffee din yace, "yaya..!
"sha mana ko kana jin tsoro kar na kashe ka ne kanina..! amsar cup din sultan yayi ya shaye coffee din hawaye na bin kuncin shi yace, "Ashad me na tsare maka a duniya? Me kake nema a duniya wanda sai ka kashe ni zaka samu, ko duniya zata taru tana bani labari wani yayi ma dan uwan shi abinda kamin ba zan yarda ba, amma sai gashi dan uwana yamin, ban taba tunanin kiyayar da kake nuna min a idanuwan ka ba takai haka ba Ashad, kayi kokarin kashe ni yafi a kirga me kake nema a duniya wanda har se ka kashe ni" sultan ya ida zancan yana jijiga Ashad hawaye ne suka zabowa Ashad ganin yadda sultan ke kuka yana jijiga shi ya cigaba da cewa, "ina san ka kanina bani da dan uwar sama da kai Ashad, amma kai baka da babban makiyi sama dani, ka riga ka zamar min da uwar rigar kaya na cire ka nayi yawo tsirara na saka ka cutar dani, ka cutar dani yafi a kirgi duk wani farin ciki na kai ke bi kana rusa shi ban taba tunanin haka kake ba, Ashe kai ke bibiyar rayuwata ba kowa ba yanzu kuma ka dawo kan matata wanda nake matukar so zan iya yafe maka komai amma ban da cutar da Nihal, idan har mutuwa tace farin cikin rayuwar ka" bindigar dake ciki aljihun shi sultan ya ciro ya kama hannu Ashad ya daura mashi yace, "ka harbe ni ka huta Ashad ka kashe ni da kanka amma ka fara fadi min laifin dana aikata maka kake aikata min haka sai na nemi yafiyar ka..! jikin Ashad ban da rawa ba abinda yake sai hawaye dake zubo mashi yana kallan bindigar da sultan ya daura mashi a hannu sultan ya cigaba da cewa, "idan baza ka iya kashe ni da bindigar ba ga poising ka samin cikin tea din nan ka duramin shi har se na shanye, tsawan kwana uku zan dauka kafin poising din ya fara aiki kaga ba wanda ze gane kai ka kashe ni, idan har hakan shi ze samama farin cikin har karshan rayuwar ka, na taba cutar da kai ne Ashad? ka fadin min idan na taba, ka jefe rayuwar mutane dawo cikin hadari saboda kana san ganin bayan yayan ka sultan..! kasan mutane nawa ka kashe saboda ni,? I can't still believe cewa my on blood brother do such a thing like that not even in my dream" kuka Ashad ya saki yana cewa, "ya ishe ni haka dan ka gane ina san kashe ka sai me? naji nike yunkuri kashe ka wace rana ko wani yini, kan san dalili..! saboda mi za'a fifita ka a kai na, kan wani dalili komai za ace kai ne, ba a taba cewa ni..! duk wani abu mai kyau na kane ni kuma fa? ba me taba jin sunana na tashi sai na ka, me yasa ba zanyi yunkurin kashe ka ba saboda nima a rinka kiran suna na kamar yarda ake kira ka, hata kanena ka kwace sun zama naka kai kad'ai kakar ta mu ma ta zama taka kai kad'ai sai kace kai kad'ai ne jika sannan ta zaba maka mata mai kyau, ni ban isa auran bane ko ban dace a samamin matar bane? gurin aiki karkashin ka nake aiki bayan karatu daya mukayi kwallin da kake takama da shi nima shi gare ni, kana tunanin duk haka na min dadi se na zuba ido ina kallan ka? ba tare da na nemar wa kai na mafita ba, ko ban kashe ka ba bakin cikin ka ze iya kashe ni to kafin haka ta faru kara na kashe ka..! Ashad ya ida zancan yana kuka sultan ma kuka yake yana cewa, "idan ba'a kira babba a gida ba karamin za'a kira Ashad? wanna dalilin yasa kake so ka kashe dan uwan ka Ashad" Sultan ya ida zancan yana kama hannun Ashad ya daura bindigar a kirjin shi yace, "harbe ni ka huta kashe ni Ashad," kuka Ashad ya saki tare da ture sultan ya fada saman kujera jikin shi na rawa ya koma gefe guda yana kuka rike da bindiga gabaki dayan su kuka suke bame lallashin wani a cikin su Sultan yace, "idan har kashe ni shi ne ze samama duk abubuwan daka fadi Ashad ka kashe ni, amma ka yafe min Ashad bani na kwance maka kanne ba, kai ne baka jan su a jiki gurin aiki bani na hana ka jajircewa ka kai matsayi na ba, bani na hana ka zuwa wajan Ammi ba, kan me yasa zaka zauna kana ganin laifi na Ashad har kana yunkuri kashe ni" sultan ya ida zancan tare da mikewa kafar shi Ashad ya rike yana sakin kuka bakin shi na rawa yace, yaya..! Tsayawa sultan yayi cak yana jin san kanin nashi tunda hannu ka baya rubewa ka yanke, cikin dakewa sultan yace, "Ashad tunda ka rantse sai ka kashe ni zaka samu kwanciyar hankali ka kashe ni, koda wani lokaci ina zaman jiran ka" sultan ya ida zancan tare da ficewa Ashad na kallan shi har ya fice ya bar part din kuka Ashad ya kuma saki.

Bangaran sultan part na su ya nufa yana tunanin kalaman da Ashad ya fadi wani abun har da laifin su dama idan har a family za'a nunawa wani launi fata ana iya dasa mashi bakin ciki wani me karamin kwakwalwar har ya aika abinda ba shi bane, Allah ya tsare mana imani mu da wannan tunanin sultan ya janyo Nihal jikin shi ya lumshe ido ba wai dan yana jin baccin ba.

Kiran sallah Asuba ne ya tashe su bayan sun idar da sallah Nihal ta koma bacci, ta bar sultan yana lazumi saman prayer mat.

Misalin karfe 9:00am Nihal ta tashi a hankali ta sauke idanuwan ta kan sultan dake hada kaya cikin trolley murmushi ya sakar mata, cikin sanyi murya Nihal tace, "love ina zaka je naga kana hada kaya cikin jaka? Nihal ta ida zancan a shagwabe aje rigar Hannun shi sultan yayi ya tako gaban ta yace, "hayaty tafiya zamuyi"
"ina zamu? Nihal ta fada tana turo dan karamin baki ta figer din shi sultan yasa yana zagaye lips din ta yace, "yawo ko baki so? da sauri Nihal ta duro daga saman gado tana cewa, "zani mana, dama bana fita kullun ina cikin gida, to amma haka zan bika fuska ta a kone" rungume ta sultan yayi ta baya ya daura kanshi a kafadar ta suna kallan juna ta cikin mirror ba laifi kunar ta dan ragu saboda zumar da sultan ya shafa mata a hankali sultan ya sakar mata pack a kumatu yace, "Ni ke nake so ba cute face din ki ba hayaty, kuma nima baki ga na zama gurguba ki je kiyi wanka saura 30 minutes flight din mu ya tashi" makale kafa Nihal tayi tana cewa, "love ka daina cewa mijina gurgu..! Cikin wata murya mai cike da shagwaba data kara mata kyau cikin rada sultan yace, "ko na maki wankan ne? sultan ya fada yana kashe mata ido zaro ido Nihal tayi tace, "laaa..! ta ture shi ta shige toilet da gudu dariya sultan ya saki yana cewa, "kin manta baki dauki towel ba" ya ida zan yana daukar towel ya karasa bakin toilet din ya mika mata har sai da yayi kokarin fisgo ta Nihal ta sakar mashi kara dariya yayi ya barbaza sumar kan shi ya ida shirya kayan cikin trolley ya fita dan mikawa sinbul.

Koda Nihal ta fito daga wanka bata sami sultan a dakin ba sai wata orange gown da ta gani saman bed murmushi Nihal ta saki ta dauki rigar, shafe jikin ta tayi da lotion ta fashe jikin ta turare Masu kamshi sanyi dadi sannan ta saka rigar tana kokarin zuge zip sultan ya shigo lokacin har ya shirya cikin black suit yayi kyau har ya gaji takowa yayi ya zuge mata zip din rigar Nihal na kallan shi ta cikin mirror san shi da kaunar shi na karuwa a zuciyar ta, sannan suka fito.
Chapter 100 · 0% Book details