Sashe 75
Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
A wani dan madaidaicin gida Nazili ta faka motar ta BS da big boy suka dauki Tj suka shige da shi cikin gidan Nazili na biye da su, se da suka shinfidar da shi sannan BS ya kalli Nazili dake bin su da kallo tab'e baki Nazili tayi tare da cewa, "Nasan nan ze ishe ku, ku zauna har se kura ta lafa, duk abinda zaku bukata na ci da sha akwai" sannan Nazili ta ida zancan tana kokarin ficewa BS ya biyo ta yana cewa, "Ranki ya dade ya kamata ki bamu sauran kudin da kika ce zaki bamu..! kin ga se a ida yima Tj magani da su, tunda sauran kudin yan'sanda sun amsa" waigowa Nazili tayi tana kallan BS a sheke tare da nad'e hannuwan ta a kirji tace, "Amma dai kai baka da hankali ko..! Nazili ta ida zancan tana murmushi rainin hankali tace, "cewa nayi idan aikin ku yayi kyau zan ida biyan kudi ina kuka gama aikin naku da har zan baku wani kudi bayan yarinyar dana ce ku kashe tana asibiti kwance tana samun kulawa a hannun sultan, maimakwan ace tana kwance a kabari gida ya cika da yan zaman makoki, let me tell you something BS babu kwaban sisi na da ze kara ciwo..! taimako daya zan maku shine na samo doctor ya cigaba da duba Tj shine kawai abinda zan iya, shima saboda ina dan jin tausayin shi amma da badan haka ba ko kallo baku isheni ba, saboda na riga na gama contract da ku" Nazili ta ida zancan zata bud'e murfin mota rike murfin motar BS yayi yana cewa, "kin san Allah dole ki idasa biyan sauran kudin saboda duk yadda kika ce muyi munyi kawai lokacin ta ne bayi ba bazeyo ki ce baza ki idasa biya ba, idan ko kika ki toh wallahi se na tona asirri..! BS ya ida zancan yana ciro wayar shi aljihu ya cigaba da cewa, "duk plan din da kika tsara yana cikin wayar nan ki bini a hankali if not se na kaiwa sultan din ya ji da kunna shi" dariya Nazili ta saki BS yayi sakatarere yana kallan ta sannan ta gyara tsayuwa tare da matsowa tab da BS tace "kasan kuni wacece kuwa? mu zuba ni da kai shege ka fasa..! abinda nasa aka aikawa Nihal zan sa a aikatama mafi muninshi kafin ka kira sultan ka fada mashi ni zan kira shi na fadi mashi, sannan ko ka tona min asirri kasan bazan yi zaman gidan yari ba tunda bani na harbe ta ba, hasalima ina iya cewa ban san ku ba, karka manta cikin gida na kake zaune yanzu an fada ma ni shashashace ka ga wannan gidan..! murmushi Nazili tayi tare da furta "zagaye yake da wayanda suka dame ka suka shanye a daba da daukar kisa ba bakin komai ba, shiyasa nayi dana sanin daukar ku kumin aiki, ina da yaran da suka fiko tantiranci..! idan kaji wasa ka juya baya kasha kallo..! da kyar BS ya iya juyawa murda-murdan kati ya gani rike da bindigu zagaye da gidan wani irin miyau ya hadiye yana jinjina bala'i irin na Nazili da mugunta lallaikam ta damasu ta shanye a makirci, dafa kafadar BS Nazili tayi tare da kakabe mashi kafada shi tana cewa, "kayi kokarin tona min asirri na san gidan tsoho har can zani na kawar da su ina fatan ka gane wani tsoho nake nufi" Nazili ta ida zancan tana babaka dariya har da hawaye sannan ta tsaya tana cewa, "har ka ji tsoro ko? cool down my friend se ka tona min asirri sannan" Nazili ta ida zancan tare da daurewa ta cigaba da cewa, "bani wayar nan ko na dauke ka da harbi..! Nazili ta ida zancan tana tsare BS da bindiga ba alamar imani atatare da ita jiki na rawa BS ya mika mata wayar warcewa Nazili tayi tare da aje wayar a kasa ta take da takalmin kafar ta me tsini, tana dariya wayar na fafashewa sannan ta aje bindigar tare da shafa kumatu BS wanda ya gama tsorata da lamarin Nazili lallai wannan yarinyar annobace cikin mutane hura mashi iskar bakin ta Nazili tayi a ido kif-kif ta ido BS yayi tare da sauke idanuwan shi saman fuskar Nazili, dauke hannun ta Nazili tayi dake saman cheeks din BS tare da goge hannun ta da tissue sannan tace, "fool kawai..! ta ida zancan tare da shigewa mota ta bar wajan
Bayan yan mintoci da tafiyar BS doctor ya zo duba Tj security's basu kawo ma ran su komai ba, doctor ya shiga ganin shi wayam da doctor ya ganine yasa doctor ya shiga kwallawa security's kira a rude suka shigo daki, abinda idan su ya ganine ya sasu razana cike da tanbaya doctor yace, "ina patient din,? Bello dake gefe doctor yace, "shit kenan wannan ba doctor bane gaskiya an raina mana hankali" cike da tashin hankali suka kwashe abinda ya faru suka shedawa doctor, bello ya ida zancan yana cewa, "yanzu mi zamu cewa boss munyi sakaci da aikin mu shit..! a rude security suka kira DPO Bilal suka sheda mashi DPO Bilal be ga sakacin kowa ba se nasu fada dai sun sha shi har se da gwiwar su tayi sanyi, a daran suka bazama neman su Tj ko Allah ze sa zasu bar gari a kama su DPO Bilal ko ba karamin takaici yayi da irin sakacin da security's suka tafka ba.
*****
Bayan kwana biyu sosai Nihal ke samun kulawa wajan sultan duk da cewa bata sani ba tana como, sultan kuwa ya daura damara kyautatawa Nihal da inganta rayuwar ta har se ta samu SAUYIN RAYUWA da farin ciki me daurewa ko da ze rasa komai nashi a kanta, saboda labarin Nihal ya bashi tausayi sosai, bangaran makaranta ko tuni yasa an zana ma Nihal exam har sun gama result kawai ake jira, su minal ko sun dawo gida cike da murna da san ganin matar yayan nasu labarin da suka ji cewa Nihal na asibiti basu ji dadi ba, duk yadda suka so suje su ganta sultan ya hana yace tana Como su bari a fido da ita, dan haka sun dukufa da addu'a cike da zakuwar ganin ta.
Sultan ko kullun yana makale da Nihal a ganin shi hakan da yake tausayi ne ba soyayya ba, Ammar ko kullun cikin bashi gwarin gwiwa yake da kara jadada mashi labarin Nihal saboda yasan sultan mutum ne mai tausayi ta haka ze dasa mashi san Nihal din har ya wayi gari ya kamu, har Nihal ta fito daga Como sultan na bata kulawa har mamakin sauyawa sultan Nihal take ko tari me karfi baya bari tayi hakan yasa Nihal ta dan saki jiki da shi, minal da nawwara ko kullun suna kan hanyar zuwa asibiti, Nazili ko bakin ciki cin ta yake dan gani take abinda ta aikata yasa sultan ya kara san matar shi da bata tsaro na musanman hakan ba karamin hauka yasa Nazili ba.