← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 128

Sashe 35

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shigewa mota yayi cike da tunanin Nihal dan ko kasa k'arasawa yayi masaukin shi, k'ara kawai ya juya kano se yafi samun natsuwa yanzu shi ta ina ze fara neman Nihal Allah ya hada fuskokin su, ya Allah haka Ammar ya rink'a wannan tunanin da Sanbatu anya ze iya jurewa rashin Nihal kuwa a haka har ya iso kano, jiki ba kwari yana parking motar shi a parking lot lokacin yayi dai-dai da fitowar Basmal daga mota ta dawo daga makaranta sanye take da gown milk kanta na sanye ta veil black tayi kyau sosai duk da ba wata kwalliya tayi ba, mamaki ne ya rufe ta ganin Ammar har ya dawo yau, cikin siriri murya ta tace, "ya Ammar tsayawa yayi cak be juyo ba be kuma yi magana ba, A hankalin ta k'araso wajan shi tare da kallan fuskar shi wadda ke cike da damuwa tace, "my dear waya b'ata ma rai, har ka dawo daga shanono ne? be ce komai ba se ma rungume ta da yayi tsam a jikin shi, ya lumshe idanuwa yana tunanin wani hali yanzu Nihal take ciki sun dau lokaci a haka sannan ya sake ta za tayi magana ya daura finger d'in shi saman lips d'in ta yace, "bana san wata tanbaya please" sannan yayi gaba bin shi tayi da idanuwa tare da kad'a kai tayi cikin gida.

Zaune yake saman kujera yana sanye da jallabiya fara idanuwan shi na manne da glass yayi kyau har ya gaji kamar shi yayi kan shi dan kyau yana shan coffee yana danna system da alama abinda yake mai muhimmaci ne saboda gabaki d'aya hankalin shi na kanta, knocking d'in da akeyi ne ya sasa d'ago idanuwan shi tare da cewa, " come in" cikin honey voice d'in shi Sinbul ne ya shigo kan shi a k'asa yace, "Ranka yadad'e maimartaba na san ganin ka," gaban shine ya yanke ya fad'i take a nan yaji zuciyar shi na harbawa, a hankalin ya furta "ganin zuwa" toh sinbul yace, tare da ficewa ya maida k'ofar ya rufe a hankalin ya ture laptop d'in gaban shi tare da aje cup din hannu shi saman stool, a hankalin ya taso ya bud'e kofar ya fice,

Direct Fada maimartaba ya wuce dauke da sallama a bakin shi ya shiga lokacin ba kowa se maimartaba, murmushi maimartaba ya saki, a hankalin Sultan ya k'araso tare da gaishe shi har a lokacin bugun zuciyar shi na k'aruwa zama yayi kan shi a k'asa maimartaba yayi gyaran murya tare da cewa, " *SALIM* ! Gaban Sultan ne ya k'ara fad'uwa a karo na biyu, saboda maimartaba bai fiya kiran suna shi na ainashin ba, jin hakan ya tabatarwa Sultan dacewa muhimmiyar magana zasuyi, tattaro hankalin shi yayi gabaki d'aya kan maimartaba sannan maimartaba yace, "Ba komai bane yasa na kira ka ba, se dan nashe dama ka, ka fara shirye-shirye bikin ka idan kana da abinda kake buk'ata seka fad'a min, mun riga da mun gama magana da Ammi kuma hakan yamin dad'in sosai, kasancewar zab'in daga hannu Ammi ya fito, insha Allah nan da sati d'aya za'a daura auran, dago jajayan idanuwan shi Sultan yayi yana tunanin wacece wannan me k'aran kwana haka, cikin sanyin murya Sultan yace, " Abba ni fa ban gane wace magana ake ba hasali ma bamu tab'a irin wannan magana da Ammi ba" jum kad'an maimartaba yayi tare da cewa, "Ai ba wata bace ta nesa bale hankalin ka ya tashi Nihal wadda Ammi ke ruk'o," Ware idanuwa Sultan yayi yana tunanin wacece ma Nihal A hankalin yace, "ranka yadad'e ni dai ban shirya ma aure yanzu ba ya ida zancan yana satar kallan maimartaba, "Ai mun riga da mun gama magana kaje Ku sasanta kan Ku kai da yarinyar," ya ida zancan tare da had'e rai, wani irin miyau me d'aci Sultan ya had'iya, yana bin maimartaba da kallo ko ze janye maganar ganin ba wasa a fuskar shi yasa ya fice jiki a sabule.

Cikin zafin har ya nufi part d'in ammi fuskar shi murtike abinka da fara fata fuskar nan tayi jawur jijiyoyi duk sun fito, tun a bakin kofa yake kwallawa ammi kira, da sauri ammi da Nihal suka fito jin kiran yayi yawa Sultan tsaye idanuwa shi jawur yace cikin sanyi murya , "Ammi ina so ki je ki cewa maimartaba kin janye maganar had'i ni aure da Nihal, dan bana san ta bana san auran I don't like her ammi, idan kuma kina san bacin raina ayi k'ok'ari a daura min auran not ever in my dream auran nan ba zeyuyu ba Sultan ba ze auri bastard ba, se me asali wadda nasan daga ina ta fito ba tsintar ciyar mage ba," yana ida maganar ya fita fuuuu.. Kamar guguwa, ammi na kwala mashi kira ko saurarata beyi ba, Nihal ko da gudu ta shige d'aki tare da sakin kuka tana tunanin ta samu *SAUYIN RAYUWA* Ashe ba haka abin yake ba wata wahala ta tsoma kanta Ammi zata shigo dakin kuma se ta fasa tare da shiga dakin ta, tana sauke numfashi a hankalin dan har wani jiri take gani saboda kalaman da Sultan ya fad'a Ammi be taba ja in ja da ita ba se yau.

Yakumbo dake mak'ala ce ta saki lalausan murmushi dan yau se gimbiya jalila ta ji labari me dad'i ammi da Sultan a samu matsala duk da ba duka taji zancan ba.

Adda na zaune a parlour Ammar ya shigo jiki a sanyaye Adda ce ta mik'e tare da tanbayar shi lafiya jikin a sanyaye ya rungume Adda tare da sakin kuka lalashin shi Adda ta shigayi duk da bata san damuwar d'ana taba, se da yaci kuka ya gaji yana sauke ajiyar zuciya sannan Adda ta jashi tare da zaunar da shi saman kujera ruwan sanyi tasa ikilima ta kawo mashi, se da ya sha sannan ya daura kan shi saman k'afad'ar Adda, a hankalin ta ke shafa kan shi yana sauke a jiyar zuciya, A hankalin Adda tace, "Ammar ko zaka boyewa kowa damuwar ka ban dani ya kamata ka fad'a min abinda ke damun ka Ammar," cikin sanyin murya Ammar ya shiga bata labarin Nihal be boye mata komai daga rayuwar Nihal ba ya ida zancan tare da cewa, "Adda ina tausayawa Nihal ban san hannu suwa zata fad'a ba gata yarinya k'arama bazata wuce shekara 16 ba a irin wannan shekarun tana buk'arta me kula da ita musanman iyayan ta idan suna da rai" ita kanta Adda se da ta zubar da kwalla tare da yima Nihal Addu'a Allah yasa a hannu na gari take haka Adda ta rink'a lalashin Ammar har yayi shuru ya d'an warware har ya ci abinci tare da shigewa part nashi.

Direct gidan waziri Sultan ya wuce saboda gidan so annoying ya shiga gaida Adda yayi dake jera abinci dare a dining ita da ikilima, kallo Adda ta bishi da shi tare da ganin damuwa k'arara a idanuwan shi amsawa tayi, sannan ya wuce part d'in Ammar, zaune ya gashi saman kujera yana kallan news amma kwata-kwata hankalin shi baya wajan Sallama Sultan ce ta katse mashi tunani murmushi ya saki tare da cewa dude, zama Sultan yayi tare da lumshe idanuwa shi yace, "na lura so ake abi ta hannu ammi aga bayana" Sultan ya ida zancan yana goge hawayan shi da bayan hannu shi, k'ara rudewa Ammar yayi ga tashi damuwar ga ta Sultan kuma anan Sultan ya kwashe yadda su kayi da maimartaba da ammi, murmushi Ammar ya saki tare da cewa, "Nasan ammi baza ta ma zabi mara kyau ba Sultan jiki na, na bani hakan Alheri ni", harara Sultan ya watsawa Ammar rike hannu shi Ammar yayi yace, "please stop making this so difficult insha Allah auran Alheri ne," fisge hannu shi Sultan yayi tare da mik'ewa ze fice, shan gaban shi Ammar yayi yana, yace, "Haba Sultan ban sanka da haka ba, kayi hakuri mana idan ma dan wani mugun abun akayi idan Allah ya dubi zuciyar Ammi Allah ze kare ka Sultan ni dai nasan ammi bazata zab'a ma abinda ze cutar da kai ba ya kamata ka daina irin wannan tunanin, Eh yes nasan kana da mak'iya a zagaye da kai amma be kamata ka rik'a zargin kowa ba Sultan please ka rink'a yiwa mutane kyakyawan zato, balan tana na san zab'in Ammi me kyau ne, please kayi hakuri komai ya wuce, ka zo muje muyu dinner,"
"Ban ci na koshi"
"Ni kuma ina jin yunwa I can't allow you to go home with an empty stomach, na san can ma idan kaje ba ci zakayi ba, muje" harara Sultan ya k'ara sakar mashi yace, "gidan mu zan tafi tunda kai ma goyan bayan Ammi kake"
Ba haka bane goyan bayan ka nake"
Murmushi Sultan yayi har dimple d'in shi na lomawa, shiyasa a kullun yake san Ammar duk bakin cikin dake damun shi daya ga Ammar yake jin komai ya wuce, murmushi shima Ammar d'in yayi sannan suka wuce dining area Ammar ne yayi saving nasu tuwan shinkafa da miyar d'ayan kub'ewa tasha naman rago se kamshi take suna ci suna fira kamar basu bane matsala ke damu ba , can Sultan ya tsaya da cin abincin ya ja d'an siririn tsaki yace, "the most annoying thing yarinyar ko asali babu mtsww," murmushi Ammar yayi yace, "Ni dai ba ruwana nan gaba idan ka fad'a, ko aibinta baza rik'a gani ba," Ammar ya ida zancan yana dariyar shak'iyanci, harara Sultan ya watsa mashi tare da aje spoon d'in hunnu shi dariya Ammar yayi yace, "Sorry ! Sannan Sultan ya cigaba da cin abinci suna hira sama-sama bayan sun kamala dinner Sultan ya dad'e a gidan waziri sannan ya dowa gida.
Chapter 35 · 0% Book details