← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 128

Sashe 13

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*****
Bayine ke ta zarya acikin babba Masarautar *MATAWALE* kowani bawa na sanye da kaya launi iri ɗaya mata nasu rawaya doguwar riga maza ɗinki mai sulke wanda aka sarrafa shi da yadin haɗa da hular wangale geta ɗin da akayine yasa bayin suka jera layi kowa ya sada kanshi ƙasa, tunda motocin suka fara kunno kai babu motar tai ƙasa da miliyan ashirin (20) a ƙalla motocin zasu kai biyar biyu gaba biyu baya daya a tsakiya wadda tafi kowace Motar dake ciki ƙayatuwa gami da kyan gani, murfin motocin huɗu aka buɗe a tare dogarai ne da security's majiya ƙarfin dantse waƴanda sun sha suit black da baƙin glass dogarai na sanye da riga malin-malin da sharɓeɓiyar bulala wasun su harda tsofaffin taɓaryu kai kace wanda zasu yaƙi, busar da aka fara ne da algaita shi zai tabbatar maka da dan sarki *SULTAN* ya dawo daga ƙasa mai tsarki wato Makka warda ke zaune a nahiyar Saudiya, ɗaya daga cikin security's ɗinne ya ƙaraso da Sauri ya buɗe murfin motar tsakiyar ya ja gefe ya tsaya, a hankali ya turo kafar shi wadda ke sanye cikin takalmin sarauta ruwan zaiba mai matuƙat kyau sai da jinjina sannan ya idda fitowa gabaki ɗaya bayin dake harabar wurin zubewa sukayi suna masu kwasar gaisuwa, wow masha Allah haɗuwar guy ɗin har kusan sumar dani tayi duk da a lokacin fuskar shi na cikin rawani, zabuni ne sanye a jikin shima mai ruwan sulki wanda yasha aiki da milki zare sai alkyabba milk Wanda tasha aiki ta gaji kanshi na sanye da rawani white idanuwan shi na sanye da dan siririn glass fari gabaki ɗaya gurin haskyan shi kawai ke baiyana yana ɗauke da ɗan siririn hanci da jajayen laɓɓansa wanda suka kasance ƙanana kamar ya shafa janbaki, taku uku zuwa biyu yake cikin isa da mulki fadawa da security's na bayan shi, Isar su bakin wata haɗaɗɗiyar ƙofa yaja ya tsaya badawan dake bakin ƙofar ne suka buɗe mai ƙofa, daga wa fadawan bayan shi hannu yayi alamar su tsaya bakin ƙofa shi kan shi hannu abin kallo ne fari yake tas yana ɗauke da agogo ruwan haɗalashi na azirfa mai tsadar gaske yatsun hannu shi na sanye da zoben azurfa,

Haɗaɗɗan parlour ne Wanda ya amsa sunan shi yasha Royal chair's ash and black bayine keta kaikawo, gimbiya ce zaune saman ɗaya daga cikin kujerun tana sanye da doguwar Riga lace mai tsaɗar gaske green ana mata massages, a hankali Sultan ya ƙaraso yayi hugging nata tabaya wani irin lallaunsan murmushi gimbiya ta saki bayin dake ɗakin ne suka shiga kwasar gaisuwa hannuwa kawai ya daga masu cikin calm voice din shi cike da shagwaɓa yace, "habibty I really missing you" ya idda zancan tare da zagayowa miƙa mashi hannuta tayi yayi kissing nashi sannan ya zauna da nuna alamar gajiya murmushi gimbaya ta saki dan tasan halin ɗan na ta yanzu yana iya cewa kayan sun isheshi tun kafin ta gama zancan zuci Sultan ya fara ƙorafi "habibty ni dai gaskiya kayan nan sun isheni bana iya 1hour da su ya faɗa yana furzar da iskar bakin shi, bari na wuce part ɗina nayi take shower na dawo" murmushi gimbiya ta saki, "amma kafin kaje part naka ya kamata kaje part din maimartaba da part ɗin second mom ɗin ka first" cike da isa yace, to.

Kai tsaye be zame ko ina ba sai fadar maimarta ba security da fadawa na biye da shi dai-dai bakin ƙofar ya daga masu hannu alamar su tsaya, shiga yayi yana faɗaɗa murmushin shi Wanda ke fito da laka kyan shi, cikin rawani face ɗin shi take amma ana ganin kyata inaga ya cire rawanin, sarki dake saman kujera shi ta mulki datijo mai natsuwa da adalci da Sanin ya kamata, Sultan na isa gaban shi ya zube yana kwasar gaishuwa , a hankali sarki ya mike ya dago shi ya rungume tsam shi kan shi sarki yasan yayi missing dan na shi sun dau lokaci suna rungume da juna sannan Sultan yayi break up din hugging din yana smile, maimartaba ne yace, "masha Allah Sultan ka ganka ko cikakyan babba mutum mai natsuwa da kamala" ya mutse fuska Sultan yayi yace, " Allah ya taimake ka nifa kayan nan duk sun isheni ya fada a shagwabe," murmushi maimarta ba yayi irin nasu na manya yace, "a hankali zaka saba," sun Dade suna hira da maimarta ba sannan ya wuce part din gimbiya jalila wato second mom din shi step mother din shi, shiga shi part din ta, bayi suka fara kwasar gaisuwa suna mai kirari, gimbiya jalila dake zaune saman Royal chair ta wani hada rai tayi zaman yan sarauta tana cin fruit ganin bayin ta na zube wane ya sheda mata dan gold din ya zo Wanda ake fifita shi akan ya'ya ta da sauran yaran gidan, tabe baki tayi tare da mikewa badan ta so ba tana sakin murmushin yaƙe, murmushi Sultan ya saki irin Wanda take ji kamar ta kashe shi dan haushi hannu ta miƙa mashi yayi kissing ɗin shi sannan yayi kissing goshin ta tare da yin hugging din ta cikin sweetest voice din shi yace, "ruhi I really miss u" break up din hug din yayi gimbiya jalila na murmushi mai cike da ma'anuni mai cike da dunbun munafurci na gidan sarauta.

```Taku har kullun Salma Mas'ud Nadabo ``` ✍🏻
[1/7, 2:25 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊

💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞

*Story*
*And*
*Writing*✍🏽
*By*
*Salma Mas'ud Nadabo*👑

*Edit by*:
*Aliyu Miko Muhammad*

🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
(```We are the best among the rest```)

https://mobile.Facebook.com/Real-hausa-fulani-writers-forum-RHFWF-173973194167/?refid=52&red=opera-speed-dial&-tn_-H-R

*Email*:[email protected]
*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com

*Page: 31_32*

Gimbiya Jalila ce ta koma saman kujerar ta, ta alfarma tare da yiwa Sultan nuni daya zauna, murmusawa Sultan yayi tare da cewa, "Ruhi na ba zama ya kawo ni ba zuwa nayi kawai dan ki san na dawo gida lami lafiya" yana faɗa yana sakin wani ƙayataccen murmushi har dimple ɗin sa yana lomawa ciki, "ai hakan na da kyau ɗan sarki jikan sarki mejiran gado" haɗe rai Sultan yayi tare da kissing din goshin Gimbiya Jalila ya fita da sauri fadawa na bin shi a baya da security's, dogwan tsaki Gimbiya Jalila ta ja tana tunanin irin taurin rai da wayau irin na Sultan, sauke ajiyar zuciya Gimbiya Jalila tayi.

Sultan na isa turakar sa ya nufa fadawa suna biye da shi a baya da security's buɗe mai kofa akayi cikin isa ya shige tangameman pralourn shi wanda yasha kayan alatu Royal chair's ne maroon masu kyau da tsada da lallausan carpet in banda ƙamshi da sanyi AC ba abinda ke tashi faɗar tsaruwar parlour ɓata lokaci ne komai na parlour ɗin ya hadu iya haɗuwa duk wani kayan mulki da saurata parlour ya haɗa, wani irin lallausan murmushi Sultan ya saki saboda ganin ƙannan shi Jere a parlour su biyar, suna jiran isowar shi mata uku maza biyu, gabaki ɗayan su sada kai sukayi a ƙasa suna mai sannu da zuwa kowanne a cikin su yasha kayan sarauta dan gabaki ɗayan su alkyabbace a jikin su, a hankali ya tako zuwa gare su kowanne ne su mika hannu yayi Basmal ce da ta farko hannu ta ya fara kissing ta mai sannu da zuwa tare da kissing din goshin shin shi sai Ashada dake ƴan harare-harare da zafin kai ke ɗibar shi, da badan Gimbiya jalila ta matsa mashi ba da ba abinda ze sa shi ya tarbar yayan nashi, mutum se shege iyayi ta tsirfa, hannu shi da Sultan ya kama ne ya sasa dawowa daga duniyar tunani murmushi Ashada ya saki suna kallan juna shi da Sultan ido cikin ido ganin ba ze iya ja da kwarjinin Sultan ba yasa ya janye idanuwa shi tare da zare hannuwan shi daga cikin na Sultan, ƴar dariya Sultan yayi irin na yaro man kaza, sannan yayi kissing hannun Nawwara dana Minal, Nasim ke washe baki wato ɗan autan su wanda jinin su ya hadu da Sultan, Sultan na ji da shi kamar kawai yana zuwa setin shi daga shi sama yayi yana kissing nashi ta ko ina yana cewa, "I miss u my boy" dariya Nasim yake yana San kai hannu kan hanci Sultan dan dariya Sultan yayi tare da kawar da kanshi janyo kan Nasim yake yana cewa cikin tsamin murya" Uncle kissing naka zanyi this time around ba jama hanci zanyi ba Allah" ya fada yana rauyasa kai shi me wayau "to naji sarkin wayau wata rana se naga hanci na a hannu ka na lura Darling, washe haƙori yayi Wanda ya fara fanfara, a hankali ya ɗaura lips ɗin shi saman goshi Sultan yayi masa kiss, sannan Sultan ya sauke Nasim Lumshe idanuwa yayi tare da daga masu hannu alamar su fita cikin natsuwa suka bi layi suka fice.
Chapter 13 · 0% Book details