← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 128

Sashe 50

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

amsar ledar Nihal tayi ta shige toilet wanka ta farayi sannan tayi duk yadda Sultan ya fad'a mata canza kaya Nihal tayi cikin doguwar riga pink ta kama jikin ta Sosai kamar Sultan ya aunata kafin ya siyi rigar ita kanta tayi mamaki yadda riga ta zauna mata d'as, a hankali ta bud'e handle d'in kofar toilet ta leko zaune ta hango Sultan yana latsa waya, a hankali Nihal ta tako kanta a kasa ta zauna baki gado tana satar kallan Sultan dake zaune yana latsa waya jin kamar ana kallan shi yasa ya dago karfa suka had'a ido kauda kai Nihal tayi a zuciyar ta tana cewa wayo Allah na yanzu wannan mugun ze rai nani, mika mata cup d'in da Sultan yayi ne da bread rolls ne yasa Nihal dagowa amsa tayi har a lokacin Sultan ya tsare ta da idanuwan shi masu rikitata kasa tayi da kanta tana shan tea tana gyara gashin kanta da yake zubuwa yana rufe mata fuska tea din kawai Nihal ta iya sha dan bakin ta ko dad'i babu tana gama shan tea d'in ta aje cup din da ragowar bread rolls magani Sultan ya balo ya mike mata da glass cup na ruwa ran nan a had'e kwabe fuska Nihal tayi kamar za tayi kuka ganin ba wasa a face d'in Sultan ya ta amsa ta shanye bayan ta Shane ta ta aje glass cup d'in hannu ta, can kasan makoshi Sultan yace, "ki na iya tasowa mu wuce gida" to Nihal tace tare da daukar fost din ta, ta yafa veil d'in ta suka fito har a lokacin kan Nihal na kasa, parking lot suka wuce Alex ya bud'e masu murfi mota suka shige direct hotel suka wuce sakin baki Nihal tayi tana mamaki mutumin da yace zasu je gida miya kawo su nan zaune tayi ciki mota, dan ita a ganin ta babu inda zata da ya wuce gida, can kasan makosh sultan yace, "ki fito! tsare shi da ido Nihal tayi tana cewa, "ina ne nan mi ka kawo ni nan nayi dare fa yayi"
"saboda daran yayi shiyasa na ce ki fito" shuru Nihal tayi har se da Sultan ya riko hannun ta suka fito a tare har suka k'arasa reception hannun Sultan na makale dana Nihal da kallo Nihal ke bin hotel d'in ATM card Sultan ya bada aka curo kudi sannan aka bashi key d'in dakin da zasu sauka, har a lokacin Nihal na raba idanuwa har suka iso bakin lift sultan ya dana ya bud'e makalewa Nihal tayi tana bin lift d'in da kallo tana kallan Sultan dai-dai setin kunan ta Sultan yace, "yar kauye kawai ba cinye ki za'ayi ba" had'e rai Nihal tayi tare da watsawa Sultan kallan da yafi kama da harara ta fisge hannun ta, ta shege lift d'in hard'e hannuwan tayi a kirji ta, ta ja gefe ta tsaya, shigowa Sultan yayi yana kallan ta ta kasan ido tare da danna lift din ya rufe har suka isa Nihal na gefe duk cikin dari-dari take lift na budewa Nihal ta fice da sauri tun kafin Sultan yace mata fita zasuyi murmushi Sultan yayi tare da biyo bayan Nihal tafiya kadan sukayi suka k'arasa dakin su, key sultan yasa ya bud'e se da ya kuna light a dakin sannan Nihal ta shiga tana bin dakin da kallo ciki da parlour ne tsaye Nihal tayi tana bin ko ina da kallo har Sultan ya cire suit d'in shi ya aje saman kujera ya rage daga shi se shirt harkokin shin ya shigayi har a lokacin Nihal na tsaye juyowar da zeyi suka kara hada ido da Nihal hannu shi daya na zube a cikin aljihu daya kuma cup d'in coffee kauda kai Sultan yayi tare da cewa, "tsayuwa zaki cigaba dayi ne" ya ida zancan yana kuna TV shuru Nihal tayi tare da zama saman kujera ta takure waje daya, kallan kasan ido Sultan yake mata sannan yace, "idan kina bukatar wani Abu ki shiga daki ki shirya kanki ki kwata" kamar jira Nihal take ta shige daki da saurin ta Sultan yabi bayan ta da kallo.

Nihal na shiga bedroom Lafiyar bed kawai ta bi ta kwanta dan wani irin bacci take ji, bangaran Sultan ko a parlour ya kwanta saman kujera.

*Washe gari*

A hankali Nihal ta zame blanket din jikin ta tare kallan agogon dake manne a daki waro ido tayi ganin karfe goma, da sauri ta duro daga kan gado ganin Leda a gefen bedside drawer yasa Nihal budewa kayane da duk wani Abu da zata bukata toilet ta shige tayi wanka a gurguje dan burin ta be wuce ta ganta a gida ba daure da towel ta fito goge jiki tayi ta shafa lotion, gwon ce peach colour d'inkin girgar kamar bubu shape din ta ya fito sosai tayi kyau sosai duk da fuskar ta ba make up, kayan da ta cire ta tura cikin Leda a hankali ta bud'e handle d'in kofar hango sultan tayi tsaye gaban dining yana aje abinci sanye yake da suit Ash yayi kyau sosai sajan shi ya kwata luf-luf gashin kanshi se shining yake jin kamar ana kallan shine yasa ya dago da sexy eye ball din shi karfa suka hada ido da Nihal kauda kai Nihal tayi kamar me neman wani Abu ciki siriryar murya ta tace, "ina kwana," kamar me koyan magana sultan yace, "lafiya lau" sannan Sultan yace, "ki zo kiyi break" sultan ya fada a takaice
"na koshi ni gida nake so na tafi" Nihal ta fad'a tana tsare Sultan da ido shima d'in kallan ta yake sun dau lokacin me tsawo suna kallan juna sannan Nihal tayi kasa da idanuwan ta saboda karjinin da Sultan ya mata kauda kai Sultan yayi tare Jan kujera ya fara breakfast din shi tare da yin dana sanin yi mata magana, jin yunwa na nukurku sata yana sa Nihal satar kallan plate din abinci gwiwa a sage ta karaso tare da Jan kujera ta zauna ran nan a had'e serving d'in kanta tayi chips with paper soup d'in yan'ciki hannu Nihal tasa ta fara tura abinci dan ba karamar yunwa take ji ba, ta kasan ido Sultan ke kallan ta yana mamaki taurin kai iri na Nihal na nuna isa kamar d'iyar wani, goge baki shi yayi da tissue sannan yace, "muna iya tafiya yanzu" ya ida zancan yana kallan Nihal dake k'ok'arin kai lomar abinci kunya ce ta rufe ta rasa yadda zatayi tayi gashi ita bata iya ce mashi ya jira ta idasa cin abinci dan karya raina ta Sultan ne ya tsare ta da ido alamar ta tashi ko ta koshi ko bata koshi ba wannan ba damuwar shi ba ce, fasa kai lomar abinci Nihal tayi tare da Ciro tissue ta goge hannun ta da bakin ta sannan suka fice.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya yau farin ciki gobe a kasin Nihal ta kara wayewa tayi kyau se dai kullun tunanin ta ina zata taga jakar da su Ammi suka tsince ta da ita ko Allah ze sa ta samu number aunty Aisha ta shiga, lokaci yayi da ya kamata taga dangin mahaifiyar ta ko ta samu natsuwa.

kamar yadda Sultan yace wa Ammi ze nemama Nihal lesson teacher haka ya nema mata but Arabic da boko sosai Nihal ke mai da hankali tana mai kara jin itama zata san wani Abu game da addinin ta da boko dan ba wani samun ilimi tayi a hannu su gwoggo ba, in ban da ilimin talla.

*******************************

Bangaran baffa duniya ta fara yi mashi zafi kullun cikin fargaba yake da mugayan mafarke-mafarke kullun a razane yake tashi cikin dare, gwoggo ko abinda yake ya fara isatar dan ko zaman lafiya yanzu yayi karanci a gidan, mudi ko tunda ya aika ta abun kunya, suna dawowa daga asibiti tunanin Nihal ya isheshi da takaicin abinda yayi mata had'a kayan shi yayi, yayima baffa karyar cewa ze je birni neman aiki ya gudu, sara ko ta lalace bin maza ba kama hannun yaro musanman yanzu da take SS 1 dama can da bokwan take anfani tana yawo banza malamai su matsa yan tasha su matsa indai za'a bata kudi musanman yanzu da gwoggo ta daure mata kungun iskanci dan yanzu wata ran ba a gida take kwana ba, abubuwa sun had'ewa baffa sun mashi yawa gashi asirri da yayi ma'aikatan gareji ya fara sakin su dan har sun fara cewa ya biya su albashin su yadda ya kamata ko su aje aiki ko su buga shi a kotu.
Chapter 50 · 0% Book details