Sashe 3
Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwalla mata kiran da Gwoggo keyi ne ya katse masu farin ciki, rausaya kai Nihal tayi cike da shagwaba da nuna gajiyawar ta da irin kewar mahaifiyar ta da zatayi, ɗaga labulan ɗakin da akayi ne ya sanya ta miƙewa da sauri, Gwoggo ce ta aika mata kallan banza tace, "yau ga ƴar jakar uba, ina ta ƙwalla maki kira kinyi zaman ki ko kin manta yau littinin Sara na da makaranta, maza fito kiyi aikin da ke gaban ki, da sauri Nihal ta fito Gwoggo ta bita da ranƙwashi tare da aika wa Umma kallon ƙyanƙyami.
Ko da Nihal ta fita itacuwan duk jike suke da kyar ta samu ta hura wuta ta daura ruwa, bayan ƴan daƙiƙu ruwan ya tafasa ta juye a bokitin wanka ta hadawa Sara ruwa ta kai mata har toilet, sannan ta dawo ta tsaya bakin ƙofar ɗakin Gwoggo tace, "Gwoggo na haɗa ruwan wankan," banza akayi da ita kamar basu ji ba gajiya tayi da tsayuwar ta koma bakin murhu ta daura ruwan koko, can sai ga sara ta fito tana miƙa ta yi shige warta cikin kewaye.
Bayan ta sheƙa kokon ta juye shi a bokitin, ta dauka, kusan a tare suka fita da sara ita ta wuce makarantar boko ita kuma ta wuce talla.
Tafiya take a hankali cikin nutsuwa, jin kamar ana binta a baya yasata ɗaga ƙafa, shima Wanda ke bintan ɗaga ƙafa ya sake yi a karo na biyu, shan gaban ta da akayi ne ya sata razana saura kadan bokitin kokon ta ya kife, wata uwar ajiyar zuciya Nihal ta saki tace, "yaya,"
"na'am matsoraciya" dan murmushi Nihal ta saki tace, "Allah na ji tsoro," murmushi ya ɗan saki daga bisani yace, "nayi laifi a min haƙuri," murmushi kawai Nihal tayi, kanwata, "ina jummala na ganki ke ka dai yau,? "Ai jummala na makarantar boko dama asabar da lahadi ne kawai take zuwa talla da safe,"
"ke kuma me yasa baki zuwa,? rausaya kai Nihal tayi idanuwan ta suka kawo ruwa ta kauda kai, "Eyya sis am sorry na bata maki rai ko,? girgiza kai Nihal tayi alamar a'a,
"yanzu kin san mi za'ayi bari na sauke maki bokitin nan sai ki fada min kudin bokitin na baki kiyi sadaka da kokon sai ki koma gida," zaro idanuwa waje Nihal tayi tace, "na koma gida yanzu ai Gwoggo ka sheni za tayi,"
"to matsoraciya, muje to sai ki ta yani hira "to" kawai tace mai.
A hankali suke takawa suna tafiya yaya na jan ta da hira sama sama, sai da su kayi tafiya mai ɗan tsayi sannan suka isa wata ƙatuwa gona wadda ta sha shuke shuke da ababan ban sha'awa shin kan shi gurin abin kallo ne, kukan tsun-tsaye ne ke tashi gashi komai na gurin green sai ratsin flowers pink and white sai ruwan dake gudana a gefe samu kyau da haske, gonar kuma na zagaye da ƙarafuna kana hango wani dan qararamin gida wanda yasha ginin sarauta gefe ga mota mai tsada fake a gurin, sakin baki Nihal tayi tana mamaki dama Ashe akwai irin wannan
gurin a kauyan shanono, ganin yaya, ya amshi bokitin hannun ta ne, ya sata dawowa daga duniyar mamaki, gaban wani babban mutum yaje Wanda, da alama shike gadin gurin ya miƙa mashi bokitin yana masa magana fararan haƙoran sha na baiyana, sai a lokaci Nihal ta ƙarewa yaya kallo sanye yake da jeans n t-shirt, riga mai gajeran hannu blue light sai Jean's dark blue ga sumar kanshi ta kwanta sosai tasha gyara, ganin yana tahowa ne ya sata sunkuyar da kai tana wasa da ƴan yatsun Hannun ta, "ƙanwata na barki tsaye ko? murmushi kawai Nihal tayi, dan taku biyu zuwa uku su kayi suka ƙarasa bakin ƙoramar dake gudana a wurin zama yayi sannan Nihal itama ta zauna.
Kallon shi Nihal tayi tace, "yaya na tanbaye ka,? "Eh mana" ya faɗi hakan yana smile kasancewa yaya mutum ne mai fara'a, "yaya wai dan Allah nan wurin wake da shi?. "ni da nake garin shanono ban taɓa zuwa wurin nan ba," yadda Nihal take maganar ne ya bashi dariya, ɗan darawa yayi, yace, "Nima nan gurin oga nane kuma aboki na shine nace mai zan zo kauye shine ya baki keys din gurin na sauka," langwabe kai Nihal tayi tace, "shima yana da kirki kamar kai,?
"sosai ma, yama fini kirki duk wasu hallaye masu kyau gurin shi nake koya," "kai yaya, ni dai nasan a duniya nan babu Wanda ya kai ka kirki" dariya yaya, yayi yace, "idan na fara faɗa maki kirki irin na aboki na sai mu kwana mu tashi Bamu gama ba," ko yaya?
"eh mana" "to ya sunan shi,? kallon ta Yaya, yayi yace, "suna shi bawan Allah" Dan bata fuska Nihal tayi tace, me yasa yaya baka son faɗa mana sunayan yan birni, da mun tanbaye ka, ni da jummala sai ka ce bawan Allah," lokaci nan zaki sani kin ji ƙanwata" rausaya kai kawai Nihal tayi sosai suke hira da yaya dan zaman da sukayi yaya ya gano Nihal na da son fira da raha, amma sai dai da akwai abinda ya lura yana damun ta, bangaran Nihal ko ji take ta samu wani ɗan uwa, dan har wani gurbi na ɗan uwa yaya, ya samu azuciyar Nihal, sallama baba mai gadi ne ya katse masu tunani miƙawa Nihal ɗin bokitin yayi tare da yi ma yaya godiya, amsar bokitin Nihal tayi, tare da miƙewa yaya ne yace,
"lokacin tafiya gidan har yayi? daga mashi kai kawai tayi kusan a tare suka taho suna tafe suna kara wata hira idan Nihal tayi wani ƙauyancin sai ya kece da dariya har sai da suka karyo kwanar gidan su, sannan ya ciro kudin ta ya bata har da ƙari akai, zare kudin ta Nihal tayi ta miƙa masa ƙarin da ya bata harara wasa ya mata yace, "ki aje shi ko ba yau ba wata rana zai maki anfani,"
"to" kawai tace ta shige gida da sauri.
Cike da sallama a bakin ta, ta shigo gidan, Baffa da Gwoggo na zaune saman tabarma ba Wanda ya amsa mata sallamar ta, duƙawa tayi tana gaishe su ba Wanda yace ƙala sai ma Gwoggo ce data miƙa mata hannu alamar ta bata kuɗin ta, ciro kuɗin tayi cas ta bata, sannan gwoggo tace, "ki hura wuta ki daura ruwan shinkafa da wake ga wake na jiran ki, ki tsince shi tsaf idan kin gama ki tsince shinkafa, ga kuma yaji na jiran ki, ki daka "to Gwoggo"
Madafi ta shige ta fara hura wuta ga wani irin hayaki da ke tashi, saboda ɗanyan icce ne gabaki daya madafar ta gauraye da hayaki, da sauri Nihal ta fito tana tari Gwoggo dake zaune ce ta hankada ta tace, "ko zaki mutu sai kin hura min wuta nama faɗa maki," malam dake gefe yace, "dolen ta ma ai"
Da ƙyar ta hura wutar ta tashi, ta daura tukunyar tare da zuba ruwan da ta ɗebo, ta fito da wake ta fara tsincewa bayan ta kammala ta fara tsintar shinkafa lokaci ɗaya ta gama tsince shinkafar yayi dai-dai da tafasar ruwan, wanke waken tayi ta zuba a tukunya ta fara dakar yaji cikin yan awani ta kamala abincin ko da ta gama lokacin su Gwoggo sun bar tsakar gida, zuzzuba abinci tayi a roba, roba daya ta ɗauko ta juye a leda tayi sauri ta kai dakin su tana fitowa tayi kicibis da Gwoggo gaban tane ya yanke ya fadi, ta kowa ta fara yi a hankali ta duƙa zata dau tray talla, saukar mari taji wanda ya hardasa mata zaman yan bori, cikin masifa Gwoggo tace, "idan har baza ki fasa shiga ɗakin Hansatu ba lokaci dana saki aiki ba, ni kuma bazan fasa cin uwar ki ba na rantse," sallamar da akayi ne ya katse mata zance wangale baki tayi tana sakin murmushi, "oyoyoyo yan bokoko an dawo," Sara dake wani zunbure zunbure tace, "Gwoggo wani kuma dabbanci tayi maki hala,"
"ke dai bari ai indai wannan ce kullun cikin yin halin tumakai take, ki shiga kiyi wanka ki shirya abincin ki na jiran ki, kin ji
"to Gwoggo" sannan Gwoggo ta bita a baya har ta kai bakin kofa ta juyo tace, "karkiyi ƙoƙari ki tashi ki tafi idan na zo na same ki nan na lahira sai ya fiki jin dadi Allah sannan ta shige ciki.
Wani irin kuka ne ya kubuce wa Nihal kuka take sosai kamar ranta zai fita haka ta dau tray ɗin talla tana tafiya tana kuka, ga zafin rana da haska fuskar ta, ta kunbura saboda marin da tasha, a haka take tafiya ga wata uwar yunwa dake dawainiya da ita haka ta ƙarasa tasha.
Kasancewar rana ce yasa duk samarin tashar nan dan haka anata siyan shinkafar da wakyan, kafin ka ce mi har ta gama ciniki, sai duk babu dadi zaman ba jummala ba yaya.
Ɗauke da sallama a bakin ta, ta shigo gida Mudi ne zaune saman kujera tayani gulma yana zuƙar wiwi ko inda yake Nihal bata kalla ba sai ɗakin Gwoggo ta nufa cikin sanyin murya tace, "Gwoggo na dawo," shuru tayi kamar bata ji ba, can sai gata ta fito ɗauke da tray gyara tace, "idan rana tayi sanyi ki kai wannan wajan danbe"
"To Gwoggo" sannan ta miƙa mata cinikin rana.
Aje tray ɗin tayi tsakar gida ta ɗauko buta, ta fara dibar ruwa a rijiya ta juye abuta sannan ta shige kewaye dan kama ruwa, har ta shige Mudi na binta da kallo da jajayan idanuwan shi.