← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 128

Sashe 62

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Misalin karfe 12:00pm lesson teacher Nihal ta tafi, part din Ammi Nihal ta wuce a gajiye, lokacin Ammi na zaune saman three star tana kallo, murmushi Ammi ta saki tare da cewa, "har an gama lesson din? aje books din hannu ta Nihal tayi saman kujera tana cewa "eh Ammi,"
"toh madalla, Allah ya taimaka"
"Amin" zama Nihal tayi saman kujera Ammi dake kallan ta tace, "kin gaji ko?ai haka karatu yake se hakuri, ki shige bedroom ki samu hutu, zan turo maki Yasmin ta maki massage, yau ba se kin wani daura wani abuba dazu mom ta aiko da cewa kuje part nata ke da Sultan kuyi lunch" murmushi Nihal ta saki tana cewa, "amma fa na ji dadi dama tunanin abinda zan dafa nake gashi yau na gaji sosai" Nihal ta ida zancan a shagwabe dariya Ammi tayi tana cewa, "to ai gashi yanzu kin samu hutu" cike da farin ciki Nihal ta hada books nata dama ta gaji dayi ma k'atan kawai abinci ya zauna yana ci ba godi bare na gode sannan Nihal ta shige bedroom, toilet ta shige ta sheka wanka ta fito daure da towel da karamin tana goge jikin ta Sultan ya fadu mata a rai murmushi Nihal tayi tana goge jikin ta, dressing mirror ta nufa ta shafe jikin ta da lotion sannan ta shirya cikin jean da pink shirt me dogwan hannu ta kama jikin ta sosai sannan tasa black boot Nihal tayi kyau kamar ita tayi kanta, jan baki ta shafa ma lips din ta gashin kanta ya zubo har gadan bayan ta yana ta shining sannan ta fito parlour, lokaci Ammi ta shige bedroom din ta, part din mom Nihal ta wuce, dauke da sallama a bakin ta ta shiga parlour, mom dake zaune ana mata massage gefe ga fruit tana sha murmushi mom ta saki cikin ladabi Nihal ta gaishe da mom tare da samun guru ta zauna, bayin mom taba umarni su zubawa Nihal abinci tuwan shinkafa miyar egusi taji vegetable se kamshi take zama Nihal tayi ta shara abincin ta bi da fresh juice me sanyi se da ta cinye abincin sannan ta dago ido kunya ce ta kamata ganin mom na kallan ta dariya mom tayi tace, "ki saki jikin ki daughter nima kamar mom naki nake babu wata kunya tsakanin mu" daga kai Nihal tayi suna taba hira da mom sama-sama kiran sallah la'asar ya tashi su mom, a dakin mom Nihal tayi sallah bayan sun idar mom ta bud'e karamin frigde ta ciro fresh milk ta zuba a glass cup ta mikawa Nihal, washe baki Nihal tayi tare da amsa ta shanye shi duka har da lashe baki saboda dadi sosai Nihal ta saki jikin ta, haka mom tasa akayima Nihal massage, Nihal taji dadi jikin ta sosai, bayan sun fito parlour tana zaune Nasim ya shigo da gudu parlour ya fada jikin Nihal yana cewa, "Aunty Nihal please ki zo ki tayani wasa bani da friends" ya ida zancan a shagwabe murmushi Nihal tayi tana kallan shi mom dake gefe zaune tace, "Nasim ina Momi? daga ido zama yayi yana cewa, "dazu ta fita ita da yaya Ashad takin fita dani" Nasim ya ida zancan kamar zeyi kuka yana cewa, "Gashi bani da friends aunty Nihal please ki tayani" kama hannuwan shi Nihal tayi tana cewa, "to shikenan zan taya ka" mom ce ta mike tana cewa, "bari na karasa part din maimartaba idan Sultan ya dawo abincin shi na dining area" to Nihal tace tana kallan mom har ta fita sannan ta juyo tana kallan Nasim tace, "wani wasa zamuyi? Nihal ta ida zancan tana daura shi bisa cinyar ta, washe bakin Nasim yayi yana cewa, "wasan b'uya zamuyi zan daure maki eye's naki da veil se ki nemo ni, idan kika kamani se ki boye na nemo ki" to Nihal tace cike zakuwa veil din ta tasa ta daurewa Nasim ido sannan ta boye bayan kujera zagaye parlour Nasim yake yana cewa, "Aunty Nihal zan kama kine fa," ganin Nasim ya zo bakin kujera yasa Nihal tashi a hankali ta boye bayan labile, jin kamar motsin mutum yasa Nihal fisgo hannun me shigowa dan karya tona ta,ba kowa bane se Sultan da shigowar shi kenan kwata-kwata Nihal bata lura da shi bane tunanin ta Basmal ce toshe mashi baki Nihal tayi tana cewa, "kiyi shuru karya jini" kamshin turaran Sultan ne daya doki hancin ta ne yasa Nihal juyowa kamar mara gaskiya zuciyar ta na tsanata bugawa idanuwan ta a rintse ta juyo a hankali ta sauke su saman fuskar Sultan, kallan juna suka Shiga yi har a lokaci hannun Nihal na saman lips din sultan, a hankali ta zame hannun ta tana cewa, " am..!! toshe mata baki sultan yayi yana cewa kamar me rada, "kiyi shuru Nasim nan wajan" tsare shi da ido Nihal tayi tana kallo daga labilan da kayi ne yasa Nihal karayin lamo tana kallan Sultan, cike da shagwaba Nasim yace, "aunty Nihal ina kika Shiga har yanzu ban gano ki ba" ya ida zancan kamar yayi kuka, fitowa Nihal tayi daga labalan ta bar Sultan a cikin daga Nasim tayi tana dariya tana cire mashi veil din dake idan shi, dariya shima yake yana cewa, "aunty Nihal kin boye waje menisa" a hankali sultan ya fito daga jikin labilan Hannun shi na zube cikin aljihu zamewa Nasim yayi daga jikin Nihal yana cewa, "uncle! da gudu ya karasa gaban Sultan daga shi sama sultan yayi yana mashi wasa yana cewa, "my boy! Murmushi Nihal tayi tana kallan sultan, moment din su na dazu na dawo mata lumshe ido tayi tana sakin lalausan murmushi.

```Taku har kullun salma mas'ud nadabo```
[1/7, 2:29 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*Story*
*And*
*Writing*✍🏾
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITERS FORUM*🐄
(```We are the best among the rest```)

*_Assalamu alaikum bayan gaisuwa mai yawa tare da fatan kuna lafiya, nasan da yawa masoya littafi na sun ji ba dadi sakwamakwan jina shuru da kukayi, ba komai ya janyo haka ba se losing phone dina danayi shiyasa but yanzu am back insha Allah zaku rinka ganin posting dina na gode sosai da soyayyar ku masu Kira kafin nayi waya da wayanda suka min message ta WhatsApp thanks for the caring fan's Ana mugun tare irin sosai din nan na sadaukar da wannan page din gare ku fan's_*

*Page: 85_86*
Chapter 62 · 0% Book details