← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 128

Sashe 30

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sultan ne zaune a office idanuwan shi manne da glass yana duba files d'in marasa lafiya da sister Naja ta kawo mashi, knocking d'in da akeyi ne yasa Sultan cewa, "come in" ammar ne ya shigo sanye da suit Ash yana smile hannu shi rik'e da wasu files , b'ata fuska Sultan yayi yana bin files d'in hannu Ammar da kallo har ya zauna, Sultan yace rai a had'e, "Karma ka ce ni ka kawowa wannan abun na duba, dan wallahi yanzu ma zan bar office d'in gida zani fita zamuyi da Ammi aha" dariya Ammar yayi yace, "maida wuk'ar Sarkin hawa, ni zan Cuba ba kai ba na patients d'in nane"
"Hmm thank god Baka San gajiyar da nayi bane tunda na zo nake duba patients, theater biyu nayi fa Allah na gaji naso ace kai kayi theater amma se ka zo late" Sultan ya ida zancan yana aikawa Ammar Harara, "bari na fita tunda harara ta kake yi,"
Mik'ewa Sultan yayi yana cewa, "Nima yanzu zan wuce se mu wuce tare" briefcase d'in shi ya daukar a tare suka bar office d'in.

Yana isa gida part nashi ya wuce, wanka yayi a gurguje saboda yasan ammi da k'orafi shiryawa yayi cikin wata fara shada tasha aiki na sarauta da brown zare sannan yasa brown hula, yayi kyau sosai abin ka da fara fata se haskyan shi ya k'ara fitowa, direct part d'in ammi ya wuce ko da yaje dama ta shirya cikin wata gown d'in lace me tsada maroon shi take jira, Alkyabba ta Sultan ya amsa yasa mata, silver an mata aiki da bak'in zare sannan suka fita security na biye da su suka shige mota.

suna isa gidan hakimi a parking lot sukayi parking Sultan da ammi suka fito bayi da fadawa nata kwasar gaisuwa dayima Sultan kirari,

dauke da sallama a bakin su suka shige main parlour hajiya dake kallo ce ta d'ago tace, "A'a sannu da zuwa ammi" larai ta Shiga kwalawa kira ta kawowa su ammi abin motsa baki, kallan Sultan tayi tace, " yau za'ayi ruwa da k'ankara, shiyasa naga hadiri ya had'u" Sosa keya Sultan yayi yana murmushi, hajiya tace, "ammi yaushe me suna Abba ya fara zuminci? Dariya ammi tayi tace, " wato sharin da akewa mai gida kenan"
"Toh shi d'in ne baya zuminci bari hakimi ya shigo kiji mi ze ce" bata ida rufe Baki ta ba hakimi ya shigo shi ma tsokar Sultan ya Shiga yi sun dad'e suna hira Kiran Sallah magrib ne yasa hakimi da Sultan suka wuce masalaci, se bayan sallah isha suka dawo se da sukayi dinner sannan su Sultan suka fito tafiya gida har bakin mota hajiya da hakimi suka rako su.

Saman tebir Nihal ta samu ta kwanta tana tunanin yadda RAYUWA ta sauya mata ba uwa ba uba , ba wajan kwana kuka take sosai, ga wata yunwa dake azalzalata, gashi gurin shuru ba motsin kowa se kukan karnika dake tashi wani mugun tsoro ne ya lulub'e ta, tare da nadamar gudowa daga gida dama ta tsaya gwoggo ta kasheta, surutan da take ji k'asa-k'asa ne yasa zuciyar Nihal k'ara tsinkewa da wata fargaba, wasu mazane su uku suka nufo wajan da Alama yan shaye-shaye ne ganin mutane tayi tsaye a kanta mik'ewa tayi zaune jikin narawa tana bin su da idanuwa taf da kwalla, kuka Nihal tasa tare da duk'ewa ta had'a hannuwa tana cewa, "dan Allah kuyi min rai karku kashe ni"
Dariya babba cikin su yayi yana magana cikin maye yace, "ba maganar kisa a nan bamu lokaci zakiyi mu huta," share hawayan ta Nihal tayi saboda bata gane hausar ta su ba tace, Indai guru ne gashi nan na Baku" tana maganar tana k'ok'arin rab'awa ta gefe d'aya daga cikin su fisgo ta yayi ya maido ta k'ara Nihal ta saki hawaye na bin fuskarta manna ta yayi da bango se matsawa Nihal take kamar zata shige bango jin shi daf da ita har suna jin numfashin juna yasa Nihal ware idanuwan ta wani irin k'ara ta saki tare da gantsara mashi cizo ta bankad'e shi ta runtuma da gudu suma da gudu suka bita godi Nihal take har da fad'uwa tana tashi tana cigaba da gudu har ta iso bakin titi ko gani batayi samarin nan na biye da ita ji kake kiiiiiii!!! Mota ta tashi da Nihal take a nan ta zube, birkin da aka ci ne yasa Sultan cewa,"what's wrong? Ammi ma shuru tayi tunanin ta yan bashine suka tare su lokaci d'aya security's d'in Sultan da shi kanshi suka bud'e murfin motocin su, gabaki d'ayan su da mindiga a hannu su Alex ne yace, " Audu what's wrong? Cikin ina... ina.. yace, "Accident" da sauri Sultan da Alex suka k'araso tare da had'a baki wajan cewa, "mutum ko mi?
mutum yace jikin shi na rawa, dafe goshin shi Sultan yayi yana cewa, " Ya Allah yau kuma ta nan aka b'ulo min" k'arasawa yayi gaban Nihal Wanda ke kwance shame-shame jini na zuba kota ko ina, Wuyan ta Sultan ya tab'a tare da cewa, "Masha Allah tana numfashi" daukar ta Sultan yayi cak aka sata a back seat d'in mota ammi ko duk ta rikice musanman da taji wata aka kad'e komi ya fido mace da wannan daran ganin gilmawa samari yasa Sultan bin wajan da kallo

*_typing akwai wahala walla da kyar na ida wannan_*😫🤕🤧

```Taku har kullun Salma mas'ud nadabo ```🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*Story*
*And*
*Writing*✍🏾
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
(```We are the best among the rest```)

*_Ina ba masoya hakuri a kan jina jiya shuru na gode sosai da kulawar a kai naji dad'in sosai da kuka tanbaya ta lafiya akan jin shuru Allah ya bar kauna wannan shafin naku masoya SAUYIN RAYUWA_*

*Page: 55_56*

Cikin takunshi na isa da mulki ya k'araso gaban ammi ya zauna, murmushi ammi ta saki tana cewa, "yanzu nake maganar ka naga tunda ka tafi baka dawo ba," d'an tabe baki Sultan yayi se hakan ya k'ara fito da dimple d'in shi yace, "um bani da doti da rana yau se dare hope dai Dr amir ya zo ya duba ta,?
" Eh ya zo ya cire mata k'arin jinin sannan yace, "da dare za'a mata allura,"
"Good tana cin abinci? Ammi tace, "Eh amma se dai bata jin dad'in bakin ta da kyar take tura shi,"
Mikewa Sultan yayi ya nufi gadan Nihal dake zaune, cikin honey voice d'in shi kamar me rad'a yace, "mi ke maki ciwo? Ya zuba mata idanuwan shi masu rikita yan'mata, gabaki d'aya Nihal ji tayi jikin ta ya hau rawa saboda wani k'war jini da Sultan yake mata ga kyan shi dake rikitata cikin sarkewar harashe tace, " ba komai se dai jiki nane ba k'arfi ji nake kamar ba nawa ba" lalausan murmushi Sultan ya saki yana cewa, "insha Allah a hankali jikin naki ze dawo kamar nakin, ki rink'a taimakawa kanki kina cin abinci komai ze zama Normal" ya fad'a yana tsare ta da idanuwan shi, k'asa da kai Nihal tayi tana wasa da yatsun hannu ta, Basmal ce ta katse shurun da cewa, "Ammi ya kamata mu wuce gida yama yayi yanzu a fara kiran sallah magrib, tunda yayana ya zo nasan ze bata kulawa sosai" ta ida zancan tare da rik'e hannun Nihal tana kallan Sultan tana Smile, wani kallo Sultan ya watsa ma Basmal na rashin fahimata Dan shi duk a tunanin shi Basmal ce zata kwana da Nihal, bud'e baki yayi da niyar magana ammi ta katse mashi zance da cewa, " Na San ze ba maki kulawa Nihal duk abinda kike buk'ata ki fad'a ma Sultan kin ji" ta ida zancan ta shafa cheeks d'in Nihal, d'aga mata kai Nihal tayi tana satar kallan Sultan Wanda yayi kicin-kicin da rai, basket din abinci Basmal ta d'auka ammi na gaba Sultan ya bisu a baya a hankali suke tafiya ammi na bashi labarin Nihal da yadda ta tausaya mata, se da ta kai aya Sultan yace, "Than se mu maida ta inda muka d'auke ta fine," ya fad'a rai bace, ammi tace, "Ai na riga dana yanke shawara tabi mu gida kawai saboda yarinyar ta bani tausayi"
Sultan yace "Ammi ! Tare da Jan fasali yace, "babu idan zamu da ita, ni kwata-kwata ban yadda da ita ba, kuma wannan labari banga abin tausayi a cikin shi ba, ai ba kanta aka fara almajiran ci ba, kuma bata da families ne,? wannan maganar ba tayi kama da hankali ba,"
Ammi tace cike ta tsiwa, "na Riga Dana yanke shawara hakan, kuma ai ba gidan ka zan aje ta ba, gidan d'ana zan aje ta,"
Dafe goshin shi Sultan yayi idanuwan shi sun rine sunyi jawur ya juyo da ammi suna facing juna cikin sanyi murya yace, "ammi you have to no mutane ba abin yadda bane how comes za'a ce bata da families ammi you have to think about this matter," zame hannu Sultan ammi tayi daga jikin ta tace. "me anfanin matsayin naka ? Dana mahaifin ka ?ai Dan Ku taimakawa marayu da marasa k'arfi ne Allah ya baku matsayin Sultan, ina tananin zaka zama shugaba mai adalci Ashe ba haka abin yake ba, da ina tunanin zaka fi mahaifin ka tausayi da adalci Ashe ba haka abin yake ba, Sultan na riga Dana gama magana Nihal tare damu zata zauna ko kana so ko baka, ko shi mahaifin naka bai isa ya hanani aje Wanda nake so a Inda nake so a cikin gidan ba, bale kai Sultan" sannan Ammi ta bar wajan da sauri, Sultan ya bita yana cewa, "Ammi you have to understand" ko saurara shi ba tayi ba aka bud'e mata murfin mota ta shege.

Rike k'ugun shi Sultan yayi tare da furzar da iska me zafi ya wuce cikin asibiti.
Chapter 30 · 0% Book details